RASHIN GATA 161-165

🌼🌼RASHIN GATA🌼🌼

```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

*NAH*
```FOUR STAR'S```✨✨✨✨

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI SHEHU
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HASSAN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

Team#
     RGT

161-165

       Niqab ɗinta ta cire tare da wurga shi kan table ɗin office ɗin kafinta faɗa kan kujera ta ɗora kanta cikin cinyoyinta tana ci gaba da kuka tare da takaicin abinda yake yi mata yawo a ranta.....
    bata daɗe ba aka fara neman ta cos akwai patient da yawa suna jiranta, wannan ne ma yaja ya rage mata tunani da damuwar da suka cika mata zuciya tayi aikin cikin kwanciyar hankali.
   Patient d'in data dubane k'arshe ya d'aga mata hankali, tana gama dubashi tayi rubuce rubuce kan file d'inshi tare da rubuta magunguna, wanda suka kawoshi ta nema dan su amso magani da alluran da zata mashi...
   Abin mamaki ba'a ga wanda suka kawoshi ba hakan ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba, da kanta taje ta siyo magani da allura ta mashi Amma haryanzu bai farfado ba, sai dai da taimakon Allah numfashinshi ya fara komawa normal..
   Kujera taja ta zauna ta k'ura ma mutumin nan ido ita kanta bata iya cewa ga dalilin daya sa take kallonshi ba, sai yamma lik'is tabar asibitin ta nufi gida cike da tausayin marar lafiyan nan...

   Direct ɗakinta ta shiga, wanka tayi tare da sa kaya marasa nauyi dan tasan bayanan zata iya duk irin shigar da taga dama, kitchen ta shiga dan samawa kanta abinda zataci, indomie ta dafa guda ɗaya da kwai biyu sai drinks data yi na watermelon with pineapple tasa ice cool kaɗan ta dawo parlour, zama tayi taci abincin ta sannan taɗan kwanta akan kujera dan ta huta kafin a kira magriba...
   Dasauri take shirinta sakamakon mafarkin datayi na mutuminnan yana buk'atar taimakonta, bata ko tsaya karyawa ba tayi sallama da mai aikinta ta wuce asibiti...
   Gudu takeyi kamar zata tashi sama Allah ne ya kaita lafiya, bata ko ida parking ba ta fito ta mik'ama security key ya gyara parking, tana bashi ta nufi d'akin da yake.. 
  Daga bakin k'ofa taji nishinshi yana ruwan, da gudu ta fad'a d'akin ruwa ta d'auko daga fridge gora ta bud'e kamashi tayi ta tadashi zaune, tunawa tayi da baici komi ba da sauri ta had'a mashi tea a hankali take bashi har ya shanye, yana shanyewa ta b'allo magani ta bashi yasha...
   Jinginar dashi tayi ta mashi murmushi tace "sannu Baba da jiki" d'aga  mata kai yayi alamar yauwa..
   Kallonshi tayi tace "Baba suwaye suka kawoka na duba tun Jiya bangansu ba" hawayen da taga yanayi ne ya d'aga mata hankali dasauri ta matsa kusa dashi tace "kayi hak'uri idan magana ta tab'ata maka rai" girgiza kai yayi ya cigaba da hawaye...
   Ganin bai daina kukan ba yasa ta mashi alluran bacci, cikin minti biyar bacci yayi gaba dashi, tagumi tayi tana tunanin mike damun mutumin nan haka? Tabbas yana cikin damuwa kuma yana buk'atar taimakon, Allah kaban ikon taimaka mashi mudai FOUR STARS mukace amin....            

   Gudu take cikin daji tana kwala mashi kira Sameer! Sameer!! Sameer!!! Dasauri ya rik'eta yace "Nana minene?" Kasa magana tayi sai nuni da take mashi da hannu, kafin ya ankara wani k'aton mutum ya fizgeta da hannunshi yayi cikin daji da ita da gudu, gudu suke yana binsu saida suka kai bakin wani k'aton rami, mutumin ya in gizata ciki da k'arfi juyawa yayi ya kalli Sameer ya bushe da dariya yana gama dariya ya b'ace duk'awa yayi yana kuka yana kiran Nana....
   Firgigit ya farka daga mafarkin da yayi, tagumi yayi yace "tabbas Nana na cikin wani hali kuma tana buk'atar taimakona.."
   Jin kiran sallar asuba ne, yasa ya mik'e ya fara shirin dawowa 9ja, yana gama had'a kaya yayi alwalla yana idar da sallah ya ja trolley d'inshi ya aje masu key d'in room d'inshi a reception ya fita...
   Yana fita ya d'auki drop bai tsaya ko ina ba sai airport....

     Nana yanzu kam ta riga tasan wane irin aure akayi mata, wanda take kiran shi da zaman gida NA (YAR_FICIKA) tun tana kuka harta hakura ta fawwalawa Allah ta kuma samai ido taga iya gudun ruwan shi dan indai ya kuma wuce wannan month ɗin wallahi saita gudu, da wannan kudirin take kwana take tashi.

     yau kam a gajiye ta dawo ga wata masifaffiyar yinwa datake ji, hakan yasa tana ajiye niqab da handbag da wasu files² ta faɗa toilet," wanka tayi sannan tasa wasu mini wears wando iya cinyarta ko gwaiwarta ɓe karasa ba sai riga iya cibinta pink colour haka ta karasa kitchen tana kokarin samun abinda zataci.
     Duk irin yinwar da take ji fruit salad ta haɗa tasa madara peak milk ta ɗakko ɗan bowl ɗin tafito parlour, zama tayi ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya ta fara sha tana yi tana kallon MBC bollywood time ɗin suna film ɗin muhje dostie karoghe love story ɗin yayi matukar burgeta tana kallo tana murmushi jitake tamkar itace Rani mukarju ɗin.
  
   "fitowa yayi daga shi sai wando boxer da farar vest yana danna phone ɗinshi, cak ya t'saya yana zazzaro ido tamkar yaga mutuwar shi, bata san da tsayiwar shiba sai jin faɗuwar abu tayi a gefen ta....
    "ai da gudu ta mike ganin wanda take gani a tsaye ya kura mata ido yana kallonta baki na rawa yace "Na....Nan....Nana!!....."
   Kasa cewa komi tayi ta nufi d'aki da gudu, tana shiga ta saka key fad'awa tayi kan gado tana kuka "miya kawo Sameer gidana? Miyasa zai zo gidana cikin wannan shigar? Dama Sameer d'an iska ne bansani ba?"
  Tsaye yake kamar wanda aka dasa "mi Nana keyi gidan nan? Kar dai ace itace matata, indai itace tabbas na tabka babban kuskure" kanshi ya dafe ya saki wani irin kuka, tabbas yasan yanasan Nana daya san ita aka aura mashi da tuni yaje gareta Dan kullum da tunaninta yake kwana....

Four stars🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180