Posts

Showing posts from January, 2017

JARABAWA TACE 106~110

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                         (NWA)                      1⃣0⃣6⃣➖1⃣🔟    Takwas da rabi yatsaya gaban wani black gate, waige waige nakamayi dan nagano ma masu karatu wace unguwa ce, ba shakka Goruba road ne, horn d'in daya keyi shi ya mai doni cikin hankalina, da sauri get man ya taso ya wangale mashi gate, kan motarshi ya cinna cikin haraban gida, parking space ya samu ya faka motarshi bai tsaya kulle ta ba ya fito ya nufi cikin gida...    Cikin falo ya kutsa kanshi bako sallama, tsayawa nayi na saki baki ganin yanda cikin falon ya had'u, nabarma masu karatu su auna da kansu..    "Auta Lafiyarka ka shigo cikin gida ba sallama? Wannan ba d'abi'arka bace ba" wata dattijuwar matace wacce bazata wuce shekara sittin da biyar ba ba tayi magana..    Wuri ya samu ya zauna kusa da ita yace Ammi kiyi hak'uri" murmushi tayi tace "to naji amma ina kashige haka da sai yanzu zaka dawo gida? Duk yau ban gan

JARABAWA TACE 101~105

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                           (NWA)                        1⃣0⃣1⃣➖1⃣0⃣5⃣      K'arfe tara na safe ta fito cikin shirinta na bak'ar abaya tayi rolling da bak'in veil, falo tasamu Deeyerh tana aiki, zaro ido tayi tace "Deeyerh baki shirya ba? Kinsan fa kano zamu kuma flight d'inshi 12:00pm ne" dariya Deeyerh tayi tace "Anty nafayi wanka kawai kaya zan saka idan munci abinci"..    Dariya tayi ta zauna bisa kujera nan Deeyerh ta kawo mata dankali soyayye da tea murmushi tayi tace "Thanks amma tare zamu ci dan haka jeki had'a tea d'inki, ba musu Deeyerh ta tashi taje ta had'a tea d'inta...    Nan suka fara break suna fira, kallonta Deeyerh tayi tace "Anty Lady waye zai kaimu?" Murmushi tayi daidai tana aje cup d'in tea tace "nimana" ke! tazaro ido dama zaki iya long journey?  Dariya tayi sosai tace "idan mun tafi zaki gani idan kuma kina tsoro na bark

JARABAWA TACE 96~100

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                         (NWA) She isn't my mother, She isn't my sister, she's one of d family, who's more like a friend. she has fun with me, laughts with me, listens to me, encourages me, she spends time with me, believes me. Share with me, cheers for me. She understands me like a mother, she's there for me like a sister. And perhaps best of all she loves me like a daughter... She's ANTY MAIJIDDAH *This page is for you Anty Maijidda Musa*                9⃣6⃣➖1⃣0⃣0⃣    Cikin shirinta na Abaya tafito Abayan brown and purple sai tayi rolling da purple scarfs, d'akin Deeyerh ta wuce Deeyerh na ganinta ta saki baki, hararanta tayi cikin tsokana tace "miye kika saki baki kina kallo na?" Dariya Deeyerh tayi tace "Anty Lady kinga kyanki kuwa? Wlh kamar wata tauraruwa" harara ta sakar mata tace "karki ida shiryawa ki tsaya surutu" dariya Deeyerh tayi tace "ai nama gama muj

JARABAWA TACE 91~95

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                         (NWA)                        9⃣1⃣➖9⃣5⃣      Tun da na rufe babun soyayya na maida hankalina ga karatu na har Allah yasa muka gama bansamu wata matsala ba tunda na fara karatu har Allah yasa nagama ban tab'a samun matsalaba..      Kusan tare muka gama da Aflan koda yazo yaga halin danake ciki bak'aramin tausayaman yayi ba shi keban shawara akan na d'auka *JARABAWA TACE* haka nakuma amince da hakan..    Ranan da kika dawo kikazo gida koda kika ganni saida hankalinki yatashi ganin yanda na rame, kinyi kinyi na gaya maki damuwata amma na kasa saboda bansan nasa kaki cikin damuwa, kuma bansan na dinga tuna abinda yawuce..    Duk da nakasa mance abinda yafaru dani dan wani lokacin idan ina ni kad'ai na kan fad'a cikin tunani har kuka nakeyi..    Su Uncle suna k'ok'arin suga sun kyautataman saboda basu rageni da komai ba duk abinda nakeso shi sukeman, ko ban fad'a ba indai sun

JARABAWA TACE 86~90

JARABAWA TACE Yar _ficika NAGARTA WRITER'S ASSOCIATIONS                     (NWA)    THIS PAGE IS FOR YOU MY MENTOR HAUWA JABO THANX FOR D LOVE, KIA, COURAGE AND SUPPORT. YOU MEAN A LOT TO ME❤ #1love💕💕                  8⃣6⃣➖9⃣0⃣ Ina shiga d'aki na turo kofar d'akin, ji kake "Bammmf." Na fad'a kan gado na fara rera Nannauyan kuka, kuka ne mai hade da tsananin bakin ciki, haka har wahallen bacci yayi awon gaba dani. Na share awanni Ina bacci, mai cike da mafarkai kala-kala, Ina farkawa naga d'akin ya k'ara min duhu, tsaki naja, na wuce don sauke farali, na kare sallah Ina zaune ina karanta wasikar Jaki, kallon wayar nake yi sabida kusan kullum dai-dai wannan lokacin Sameer yana min SMS, a hankali na janyo wayar ina duba message d'inda yake min ada. Hankali ya kai gun wani SMS da ya min yake cewa..... "You're like a target that I always try to aim at. How I wish I could aim you at the heart. But every time I fail, I feel so sad. Y

JARABAWA TACE 81~85

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                            (NWA)                        8⃣1⃣➖8⃣5⃣       Dasauri na mik'e tsaye tafiya nafarayi sai kuma na tsaya, takowa yayi yazo kusa dani, "Lady" abinda ya fad'a kenan kasa d'agowa nayi saima hawayen da na cigaba dayi. Hankicif ya zaro daga cikin aljihunshi ya shareman hawaye, k'amshin da hankicif d'in keyi yasa na k'ara lumshe ido.      Kallon shi nayi nace "Sameer miyasa zaka tafi kabarni? Miyasa zakayi haka hukuncin da ka yanke yaman tsauri" murmushi yayi yace "ba da san raina nabarki ba komi yafaru duk ke kika jawo kinsan ban iya nisa dake.."        Uncle ne yace "toh kuzo ku zauna ni zan maki bayani" ba musu muka isa wajensu muka zauna...      Bayan mun zauna Uncle yace "duk abinda yafaru agaban idon mu"............nan ya kwashe komai ya fad'aman ya k'ara da cewa "kuma mu mukace yayi hak'uri ya daina zuwa wajenki

JARABAWA TACE 76~80

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                          (NWA)                         7⃣6⃣➖8⃣0⃣       Duk abinda yafaru gaban idon su Uncle akayi shi, falon suka k'araso dafashi Uncle yayi d'agowa yayi da idon shi da suka rine suka zama ja, murmushi Uncle ya mashi tashi yayi ya rik'e Uncle yace "Uncle wai bata sona mina mata haka mike gareni da zata k'ini" ba Uncle ba ko yaya ya bata tausai. Bubbuga kafad'arshi Uncle yayi yace "kayi hak'uri Sameer kabi komi a hankali ni nasan tana sanka kawai tana tunanin wani abu ne".       Miyeshi? Wane abune da zai sa ta k'ini haka wlh ina santa sai kuma ya fashe da kuka kamar yaro, rarrashin shi Uncle yayi yace "kayi shiru zan maka bayanin komai.."      Zama yayi ya dafe kanshi, suma zama sukayi nan Uncle ya mashi bayanin komai bai rage mashi ba, kallon Uncle yayi yace "dan Saleem ya yaudare ta shine zata k'ini?" Murmushi Yaya tayi tace "rad

JARABAWA TACE 71~75

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                          (NWA)                        7⃣1⃣➖7⃣5⃣       Tun daga sannan shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanina da Sameer, shike kaini makaranta ya d'au koni kullum yana gidanmu, kowa yasan k'awance na da Sameer.      Aflan har gori yakeman tunda na samu Sameer na daina kulashi saidai kawai nayi dariya, dan gaskia Sameer namiji ne mai saurin shiga rai duk abinda nakeso shi zaiyi idan banaso to ko yanaso ya barshi..      A haka kullum shak'uwa na k'ara shiga tsakaninmu, ranan wata litinin ya d'auko ni daga school muna tafe muna fira. Har muka iso gida, bud'e k'ofa nayi zan fita hannu na yakamo juyowa nayi na kalleshi nace "yadai?" Murmushi yayi yace "babu" to muje mana, ah ah zan wuce gida ne amma ki saurareni aftr isha akwai maganan da zamuyi dake, gyada kai nayi nace "shikenan Allah ya kaimu" ina kaiwa nan na fita ina d'aga mashi hannu har yaba

JARABAWA TACE 66~70

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                         (NWA) Wannan shafin nakune masoya na, nagode sosai da k'aunarku akaina Allah yabar zumuci. Naji sauk'i kuma in sha Allah zan dinga typing kamar kullum, da wanda suka kirani da wanda sukaman SMS da wanda Allah bai basu ikon kira ba duka nagode...love u more sweetos❤ #1love💕💕                       6⃣6⃣➖7⃣0⃣       Yana fad'ar haka ya juya ya nufi hanyar fita, sanyi jiki na yayi nasan ban kyauta ba maganar da na fad'a mashi. Sameer abinda nace kenan tsayawa yayi cak bai matsaba kuma bai juyo ba. Tashi nayi na isa kusa dashi  nace "Sameer kayi hak'uri akan maganan dana gaya maka ni kaina nasan ban kyauta ba" juyowa yayi da murmushi d'auke a fuskarshi yace "karki damu" yana kaiwa nan ya fita...       Komawa nayi na zauna nikaina nayi danasanin maganan dana fad'a mashi, amma ba yanda zanyi ne, haka su Yaya suka dawo suka iskeni, kallo na Yaya tayi tace "La

JARABAWA TACE 61~65

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                      (NWA) THIS PAGE IS FOR YOU MY AUNTIES ANTY MAIJIDDA MUSA ANTY AMINA KAURA ANTY SADEEYA JEGAL                     6⃣1⃣➖6⃣5⃣       Tunda Aflan yadawo na rage damuwa, kullum sai ya tsareni naci abinci haka zanci ko inaso ko banso, haka da mungama abinda muke zamu fita yawo. Zan iya ce maki kashi tamanin da tara na damuwa ta ya rage, saboda iya gwargwado Aflan na kula dani.       Saida Aflan yaga na warware babu wata matsala tare dani kana ya koma makaranta, randa zai tafi da kyar aka rabamu dan abinda ya faru dani ya dawoman sabo. Ni kuka Aflan kuka, bazan manta ba bayan mun kaishi airport har ya juya ya tafi, ya sake dawowa kallon su Uncle yayi yace "Daddy Mammy ga amanar Lady nan yanzu taimakon ku take nema dan Allah kudinga tsareta taci abinci" murmishi Uncle yayi ya dafa kanshi yace "karkaji komai My Boy in shaa Allah zamuyi iya bakin k'ok'arinmu" Kallon shi Yaya tayi tace &

JARABAWA TACE 56~60

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                       (NWA) THIS PAGE IS FOR YOU MY FOUR STARS⭐ ZARAH BUKAR~Besty AUTAR HAJIA~Kawa NAFEE ANKA~Sweetest STYLISH BICH~Hajia nah                     5⃣6⃣➖6⃣0⃣       Zanci abinda nace kenan, zama Aflan yayi ya dinga bani abinci a baki har sai da nace mashi na k'oshi kuma ya tabbatar da naci da yawa kana ya kyaleni. Babu wanda baiyi murna ba ganin naci abinci ranan, kallo na Aflan yayi yace "kinsan wani abu?" Girgiza kai nayi, yace " tashi kije ki wanka ki shirya fita zamuyi yanzu" nikaina inasan fitan dan nagaji da gidan. Ba musu na tashi nayi hanyar d'akina, ina shiga na fad'a toilet danyin wanka....       Ban d'auki wani lokaci ba na fito daga toilet, tsintar kaina nayi da sha'awar yin kwalliya gabam mirror naje mai na murza, simple makeup nayi nabi jikina da turaren rasasi, ina gamawa na kalli kaina ga mirror nikaina nasan nayi kyau murmushi nayi na nufa gaban wardrobe

JARABAWA TACE 51~55

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                      (NWA)                        5⃣1⃣➖5⃣5⃣         Shigowa sukayi suka samu wuri suka zauna, d'agoni Yaya tayi ta share man hawaye. Uncle yace "Nafeesah ki saurareni magana zanyi dake" shiru nayi ina kallonshi, nayi magana da Saleem yace man iyayenshi ne suka had'a shi aure da yarinyar ba yanda zaiyi ya bijirema maganansu, kuma baida k'arfin da zai aure ku duka biyu, dan haka kiyi hak'uri bayaci amanarki bane ba ba yanda zaiyi ne. Kallon shi nayi nace "yace yaci amanata mana miyasa ya shigo rayuwata miyasa zai maidaman farin ciki bak'in ciki" sai na sake fashewa da kuka...       Uncle yace "Kiyi hak'uri hakan baya na nufin zaki dawwama cikin bak'in ciki ba i know akwai ciwo kuma bai maki adalci ba amma kiyi hak'uri in shaa Allah sai kinyi dariya" yaushe ai banga ranan da zanyi dariya ba, jawoni Yaya tayi jikinta tace "kidaina fad'in haka Lad

JARABAWA TACE 46~50

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                      (NWA) THIS PAGE IS FOR YOU DEEJERH Banda bakin da zan maki godia irin kaunar da kike nunaman saidai ince Allah yasaka maki da alkairi yabiya maki buk'atunki na Alkairi....thankyou so much priya❤                  4⃣6⃣➖5⃣0⃣      Kyarma hannuna yakamayi bansan sanda na fara kwalla ba, da sauri na nufi d'akin su Yaya ina shiga banyi sallama ba na afka ciki saboda yanda na rud'e. Gaba d'aya suka mik'e ita da Uncle suna tambayana lafiya, kasa magana nayi sai kuka da nake faman yi, tsawa Yaya ta dakaman wanda yasa na fashe da kuka, d'aure fuska Uncle yayi yace "akanmi zaki mata wannan tsawar? Baki binta a hankali" hannuna yakamo ya zauna dani kallo na yayi yace "Lady mike faruwa?"      Mik'a mashi wayan nayi, yana amsa yakai dubanshi kan screen d'in zumbur ya mik'e shima yana salati, matsowa Yaya tayi kusa dashi tace "wai miye?" Wayan yabata tana

JARABAWA TACE 41~45

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                       (NWA)                    4⃣1⃣➖4⃣5⃣         Tana shiga kitchen ta tarda Deeyerh ta gama komi, rungume Deeyerh tayi tace "yar k'anwata sannu da aiki na barki ke kad'ai" dariya Deeyerh tayi tace "bakomai Anty nah ai kina da bak'uwa shiyasa, dama yanzu nake shirin kai maku abincinku." Gyad'a kai tayi ta d'auki tray d'in, da sauri Deeyerh ta karb'a dariya tayi tace "Deeyerh bakisan ina aiki ko" dariya Deeyerh tayi tace "Anty nah ban san ki wahala ne" tana kaiwa nan ta nufi d'akin Lady. Da sallama ta shiga d'akin tana aje tray d'in ta gaida Zainab, amsawa tayi cikin sakin fuska tace "mun barki ke kad'ai ko Deeyerh?" Dariya Deeyerh tayi tace "bakomai Anty.."       Juyawa tayi ta fita, bin bayanta Lady tayi da ido, tace "wlh besty inasan Deeyerh jinake kamar ciki d'aya muka fito da ita" murmushi Za

JARABAWA TACE 36~40

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                      (NWA)    THIS PAGE IS FOR YOU MIEMIE BEE                     BIEHEART❤ On your birthday, I may not be there. But that doe'snt mean that I don't care. I regret that I won't be by your side to celebrate, but I wish nothing but happiness in your fate. HAPPY BIRTHDAY IN ADVANCE MIEMIE BEE🎁🎊🎉                  3⃣6⃣➖4⃣0⃣         Ina shiga d'aki nafad'a kan gado ina dariya, waya na jawo na kira Aflan bugu biyu ya d'auka yace "Lady ban labari". Dariya nayi nace "wane labari zan baka?" Tsoki yayi yace "bansani ba Malama idan zaki gayaman ki gayaman yanda kukayi dashi" tab'e baki nayi kamar yana ganina nace "labari fa babu dad'in ji" da sauri yace "WHY?" Ceman yayi yana san k'awata Zainab kuma yaga nikad'aice Frnd d'inta shiyasa ya biyo ta hanya ta yasan zata amince dashi. Dariya Aflan ya bushe da ita yace "u mean

JARABAWA TACE 31~35

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                       (NWA) This page is for you Meerah Saad❤                3⃣1⃣➖3⃣5⃣        Ina fita muka had'u dasu Uncle, Yaya na ganina tafara dariya baya nayi da gudu zan koma d'aki cafko ni tayi tana dariya, sunne kai na nayi k'asa ina murmushi. D'agoni tayi tace "lallai wannan saurayin anaji dashi har gayu aka d'auka haka?" Kumbure fuska nayi na kalli Uncle dake ta faman dariya nace "Uncle kanajin Yaya ko?" Dariya yayi yace "Yaya adaina" nidaina,  "amma surukin nawa mai hankali dashi" cewar Uncle kenan dariya nayi na fizge jikina na ruga...      D'akin Deeyerh mai aiki na wuce nace mata! ta kwashi kayan abinci ta kaiman guess room ina da bak'o, ba musu ta tashi ta nufi hanyar fita....       Saida Deeyerh ta dawo kana na tafi, ina isa bakin k'ofan gabana ya dinga fad'uwa haka na daure na shiga da sallama, zaune yake yana latsa waya d'agowa

JARABAWA TACE 26~30

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                       (NWA)                    2⃣6⃣➖3⃣0⃣      Ban farka ba sai (10:00am) da yake ranan ina fashin sallah kuma ranan week end ce, ina tashi na shiga wanka ina fitowa nayi simple makeup wadrobe na nufa doguwan riga na saka ina gamawa na nufi hanyar parlour, a daining table na iske su Yaya da murmushi na k'arasa wajen, ina zama na gaidasu amsawa sukayi cikin sakin fuska, abinci na zuzzuba ma kowa kana na zuba nawa, nidai tunda na zuba na kasaci sai juya spoon nake, kallo na Uncle yayi cikin kulawa yace "Lady yadai? Naga bakicin abincin ko wani abu ke damunki?" Kafin na bashi amsa Yaya tace "tambayarta dai k'ila kai ta gayama maka saboda kwanakinnan na rasa gane kanta" kallona yayi yace "haka ne?" Murmushi nayi na sadda kaina k'asa...         Aje spoon d'in hannunshi yayi yace "Lady miye damuwarki? Gayaman abinda kikeso ni kuma zan maki shi idan baifi k'arfi na

JARABAWA TACE 21~25

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                         (NWA)             2⃣1⃣➖2⃣5⃣        Koda na tashi da safe na kasa mance abinda yafaru dani jiya, haka dai na shirya na nufi makaranta da aduar Allah ya had'ani da saurayin jiya, ina shiga lecture hall dake na fara had'uwa tasowa kikayi muka rungume juna, muna cikin gaisawa lecturer ya shigo gaba d'aya muka maida hankalinmu wajenshi...        Muna fitowa kika kalleni kika ce waini Nafisa lafiya na ganki cikin farin ciki haka? Murmushi nayi nace maki bakomai, girgiza kai kikayi can kikace Nafisa zanyi transfer na koma KD da karatu, cikin sanyin murya na d'ago na kalleki nace miyasa? Murmushi kikayi kikace hakanan kawai amma karki damu in shaa Allah kamar muna tare ne dan kinzama yar uwata, haka na hak'ura badan naso rabuwa dake ba amma ba yanda zanyi...      Haka muka gama lectures muka fito zamu tafi gida amma hankalina duk bai tare dani, ina tunanin yanda zanyi zaman makaranta ba tare

JARABAWA TACE 16~20

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                         (NWA)               1⃣6⃣➖2⃣0⃣        Nafara karatu cikin sa'a ban samu wata matsala ba kullum driver ke kaini makaranta yana mai doni, kamar yanda kika sanni bani da tarkacen k'awaye, saike da Allah ya had'amu dake da farko naso nak'i amincewa dake da kikazo man kina sona da k'awance saboda bantaba k'awa ba amma dana ga yanayinki da hankalinki saina amince dake, zan iya cewa kece k'awata ta farko dana farayi tunda na tashi a rayuwa...       Randa na fad'ama Arif nayi k'awa yayi mamaki har cewa yayi yaso ya ganki, dariya nayi nace "watarana zaku had'u" haka kowa na gidanmu yasan da k'awancen mu..      Watarana na fito daga lectures ina sauri zan tafi gida saboda Uncle zaiyi tafiya kuma inasan naganshi, sauri nakeyi na isa gaban mota saboda driver yazo d'aukata, jinayi nayi karo da wani abu, waya samsung k'irar edge ce ta fad'i tana fad'