HUDAH 01~25
[4/8, 15:32] Feedoh: ⭐⭐HUDAH⭐⭐
NA
Feedoh & meesha lurv
0⃣1⃣~0⃣5⃣
K'wance take fuskanta rufe kamar tana bacci, while ba bacci bane, da alamu kuka takey, wata yar dattijuwa ce ta shigo dakin tana kiran huda huda huda,aww Ashe kina nan k'wance kinaji ina k'walamaki Kira kinyi shiru, kina nan kina sana'ar taki kenan kuka, Allah yakawo maki randa zaki daina wanan kukan naki, huda tace Maaah ban tunanin ak'wai wannan ranan, toh nidai idan kingama kukan tashi ki gyara jikinki zan aykeki, tace toh, huda tagama shirinta tsaf ta fito tace Maaah nagama, maaah tace ga sak'o can kikaima hajia sadiya, huda tace toh Maaah natafi, toh saikin dawo karki jima huda tace toh maaah.
Bayan huda takai sak'on da maaah ta ayketa takai, tana tahowa wani ya dinga binta yana Kira ko kallon inda yake batayiba dan gani take duk maza halinsu guda, harta shiga gida yana binta saida yaga tashiga gida ya juya, huda tayi sallama tana maaah nadawo ma tafito daga bandaki da buta tace sannu da dawowa auta , huda tace yawwa maaah hajiya tace tagode tana kuma gaidaki, maaah tace Ina amsawa.
Maaah da huda na zaune bayan sallar isha'i wani yaro yayi sallama, wai ana sallama da huda, huda tace jekace batanan, maaah dake gefenta ta k'walama yaron Kira tace jekace tana zuwa, maaah ta juyo kan huda tace haba Auta har yaushe zaki daina korar samari, KO kuma sokike muzauna nidake,aure fa zaki watarana, huda tadago idanuwanta da suka canja Kala tace, maaah har yaushe zansa ran aure, bayan rayuwata tagurbata, maaah ta dafa kafad'arta tace huda kidaina fidda rai daga rahamar ubangiji, komi da kika gani mukaddari ne daga Allah, haka dai maaah taitama huda nasiha harta yarda zata fita.
Shiko yanda akayi yasan sunanta, bayan tashiga gida saiyama wani yaro yama magana yace yasunan yarinyar nan data shiga gida yanzu, yace sunanta huda...
Koda huda ta fito waje fuskar nan tata, murtuke kamar bata tab'a fara'a ba, tamai sallama, ya amsa yace nasan zaki mamakin zuwana gidanku tunkan hanya nake maki magana kikaki sauraro na shine na biyo ki, na farko dai sunana naufal, kuma gaskia bazan boye makiba tunda naganki naji kin kwanta man, kuma so nake in aure ki, huda ta d'ago idanuwanta da suka rune tace kayi hakuri bazan iya sanka , saboda na kulle shafin soyayya a rayuwata naufal ya dubeta yacen kozan san dalili, tace basai kajiba wannan sirri na ne nikadai amma da kindaure kin... Bata bari ya ida ba tace malam kayi hakuri nagama magana ta kuma saida safe......
Written by
Fiddausi Abdul'azeez (Feedoh)&
Ayeesha Musa (meesha lurv).
®NWA®
[4/8, 15:32] Feedoh: ⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & meesha lurv
0⃣6⃣ ~🔟
Da sauri tayi hanyar shiga kofar gida, tana mai zubar hawaye, "magana yake mata amma ina tanajinshi ta shige gida da gudu, tana mai kara sautin kukanta" tana shiga cikin gidan maah na zaune inda ta barta taga ta wuce d'akin da gudu tana kuka, batayi yunkurin binta Dan tasan yadda takeji a zuciyarata, cuta ce ariga da an cucesu.
Shiko Naufal yana tsaye inda yake, yana bin kofar shiga gidansy HUDAH da kallo kamar mai kallon TV tunani yake mai yasaka HUDAH tashin hankali daga anbatar soyayya, da alama akwai Abu mai girma da yasameta ta sanadin soyayya, alamu sunnuna a kwayar idota baiga kinsa ba atare da ita saidai tsoron abinda so yayi mata, toh komai miye sai na binciko da yardar Allah, komai naji duk muninsa inasonta ahaka kuma sai na aureta, insha Allah.
Wani murmushi yayi mai ciwo ya juya yabar wajen can daga gefe nahago mota ijiye a wajen, wajen naga ya nufa ya bud'e motar ya shga yaja yabar anguwar.
Saida maah tabar HUDAH tayi kukanta mai isarta, sannan tashiga d'akin bayan ta ta dafa da sauri HUDAH ta d'ago kai, tana ganin maah ta fad'a kanta tana kuka nan maah taciga da shafa bayanta har tayi shiru, " maah tace haba Auta na har yaushe zaki ji abinda nake gayamiki," ko dayaushe inaso kisa tawakali aranki, ki yarda da kad'dara kad'dara CE(feenah Jafar) tasaki cikin wani hlin idan kikayi imani da ita kika mik'awa Allah lamarinki kikayi hak'uri sai kinga ribar Abu arayuwa kowa da irin tashi jarabawar, kin anshi jarabawar da Allah yayi maki hannu biyu, kuma ki gode masa wlh karshe zaki sha mamaki yadda Allah zai dawo maki da fari cikinki Wanda yafi Nada kinji auta da murmushi HUDAH ta d'ago tace Ngd maah dagayau zanyi amfani da abinda kikace insha Allah nadaina kuka, maah tayi dariya yauwa auta kokefa tashi muje waje kinji.
Written by
Fiddausi Abdul'azeez (Feedoh)
Ayeesha Musa (meesha lurv).
®NWA®
[4/8, 15:32] Feedoh: ⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha lurv
1⃣1⃣~1⃣5⃣
Bayan sun fito waje nan suka xauna bayan sun zauna nan maah, ke tambayarta waye yazo wajenta, nan take fad'amata kowaye, da yadda sukayi da shi nan maah ke mata fad'a miyasa take haka yakamata kitsaya ki saurari duk Wanda yazo wajenki, " duk abinda ya faru kad'dara ce bawai yin kankine ba, kifad'awa duk Wanda zai aureki gsky," in yaga dama ya tsaya inko yaga bazai iya ba ya tafi, " SBD bada sanki haka ta faru ba Allah ne ya kad'dara maki, kiyi hak'uri idan yadawo ki tsaya ki saurareshi," nan HUDAH tace insha Allahu maah zanyi duk yadda kika ce nan maah tace ko kefa.
Nan suka d'au wata hirar sun dad'e suna hira HUDAH sai kyalkyala dariya take, maah sai dad'i takeji yadda HUDAH tasaki jikinta har take dariya, yaushe rabu da taga HUDAH na dariya har ta manta kullum saidai kuka yakam ranar farin ciki ce awajenta, basu suka tashi awaje ba sai wajen 11 nan sukaje suka kwanta.
Washegari tun da asuba suka tashi sukayi, sallah Huda ta fito ta fara gyaran gida ta share tayi wanke wanke dama al'adar tace datayi sallah abinda zatayi kenan, dagari ya danyi haske ta daura masu abin Kari, taje ta duka har k'asa tace Maaah Ina kwana, Maaah ta amsa fuskarta sake, tace Auta kintashi lapia Huda tace lapia lau,maaah tace Allah yamaki Albarka HUDA, Allah yakawo randa zanga aure,n ki huda ta sadda kai kasa tana dariya,
Huda tagama had'a masu kalaci, bayan sungama kalaci,maah tace Auta aje ayi wanka, huda tace toh, ta tashi, Maaah tabita da kallo tana girgiza kai,bayan huda tashirya suna zaune Maaah nak'ara kwatanta mata rayuwa, Maaah tace idan bak'on ki yadawo kisaurare shi kuma kibashi labarin ki, idan yaji zai aure ki ah, haka Alhamdulillah, HUDA tace in shaa Allah Maaah, suna nan zaune suna fira, yaro yashigo da sallama Maaah ta amsa, yace Ana sallama da huda, Maaah ta kalli huda tamata murmushi, huda tace jekace inji wa, yaron yaadawo wai ance inji naufal, huda ta tashi jiki sanyaye tasaka hijab ta fita, inda ta tardashi jiya nan yatsaya, tamai sallama ya amsa fuska sake, tagaishe shi ya amsa, yace HUDA bazan gaji DA naci ba dan tunda naganki naji kinman kuma irin matar da nakeso na aura ce ke, kuma in shaa Allah ke rabona ce, na (Hauwa jabo) Huda ta dago idanuwanta da suka canja Kala, tace naufal na amince dakai, amma zan baka labarin wacece HUDA sannan saika gani idan zaka iya aure na, tace idan kashirya muje daga bisa wancan dakalin nabaka labari na..Na kalli Meesha naga tana gyangyadi nace oh no feedoh ita kuma wannan daga daukar rahoto saita Fara bacci, Meesha dallah tashi mubisu gatacan zata Fara bashi labarinta,saiga Meesha tayi wuk'i wuk'i da idanuwa tana feedoh mubisu karta fara labarin...
Written by
Fiddausi Abdul'azeez (Feedoh) &
Ayeesha Musa (meesha lurv)
®NWA®
[4/8, 15:32] Feedoh: ⭐⭐HUDA⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha lurv
1⃣6⃣~2⃣0⃣
Asalin labarin
Malam Abdallah shine mahaifna, Asalinsa d'an kauyen katsina ne, jibiya kasuwanci ke kawoshi cikin garin katsina, sana'arsa saida robobi ne, anan Allah yahad'ashi da mahaifiyata hadiza, tazo siyayya wajenshi, tunda yaganta yaji tamai saboda ya yaba da natsuwarta da tarbiyarta, baiyi k'asa a gwiwa ba ya tambayeta wace unguwa take ta fadamai, tamai kwatance, da daddare ya shirya tsaf yaje gidansu kamar yadda yamata Alk'awari, ya aika yaro yamashi sallama da ita, ta fito suka gaisa lapia lau, daganan mahaifina yagaya mata buk'atarshi, tasan ya sure ta, saboda tunda yaganta yaji yana Sonya
Mahaifiyata, ta amince mai tace yazo ya nemi izini wajen mahaifinta, mahaifina ya nemi izin wajen mahaifin mamata yakuma bashi saboda dattakon daya ga yana da shi, yace mai duk sanda ka shirya katuro magabatanka, mahaifina yaje garinsu yasami wan babansu ya gayamai yasamu mata acan katsina yanaso aje anema mashi auren ta, yayan baban mahaifina yaji dadi sosai kuma yamai alk'awari idan sati yazagayo zasuje neman aure,n mahaifiyata, satina zagayowa yayan baban mahaifina da kannenshi guda ukku sukaje Neman aure, kuma Alhamdulillah anbasu saboda mahaifina da mahaifiyata suna san juna, aka saka biki wata bakwai..
Watanni sunja inda mahaifina da mamata suke kara kaunar juna saboda burin kowa ya farantama Dan uwansa rai, lokacin biki yayi akayi biki, aka kai mahaifiyata gidan mijinta, mahaifana suna zaune lapia lau, saidai mahaifiyata ta na neman cika shekara ko batan wata bata tabayi ba, abin yafara da munta shiko mahaifina ba ruwanshi baidamu ba saboda yasan haihuwa ta Allah ce, kuma yana kwatanta ma mahaifiyata tadaina damuwa, idan Allah yace zasu haihu, in shaa Allah zasu haihu, ana haka ranan nan mahaifiyata tatashi da ciwon ciki sosai harya kaisu gata fiya asibiti, anan aka shaida masu tana da ciki, mahaifina yayi murna sosai, mahaifiyata kuma ba'a magana, wata rana mahaifiyata tatashi da wani irin ciwon ciki gashi bakowa gidan ahaka tanaji tanagani tayi b'ari,mahaifiyata tayi kuka kamarmi, haka dai mahaifina yadinga kwatanta mata, dayi hakuri Allah zaibata wani..
Ana haka mahaifiyata saida tayi b'ari har say ukku abin duk yadameta, daga nan mahaifiyata bata k'ara samun ciki ba saida tayi shekara ukku, dan harta fidda ran haihuwa, Allah maji rokon bawa, Allah ya amsa adu'ar iyayena, domin mahaifiyata tasamu ciki zokaga murna wajenta kullum adu'arta Allah yasa cikin ya tsaya. Akwana a tashi cikin mahaifiyata yashiga wata tara, ranan wata talata mahaifiyata ta tashi da ciwon mara tun yana mata ya lafa har yakai batako iya daga hanunta gashi bakowa gidan, tana cikin wanan hali saiga mahaifina yadawo, yasami mahaifiyata cikin wannan halin, hankalinshi yatashi, ya shiga makwabtanmu yakira Inna lubabatu dayake suna mutunci da mamata, tace malam mota zaka samo mutafi asibiti yaje yasamo mota suka tafi asibiti, cikin ikon Allah suna isa asibiti, ana shigar da mahaifiyata dakin haihuwa ta haifo diyarta mace maikama da mahaifinta, murna wajen banana ba'a magana, mahaifiyata tasamu sauk'i aka sallamesu suka dawo gida, duk wanda yazo barka saiya yaba da babyn da aka haifa, ranan suna naci sunan HUDA, domin dama banana yama Mamana alk'awari idan mace tahaifa sunan ta huda domin mamata nasan sunan, kuma yacika mata burinta....
Lurv u Meesha
Written by
Fiddausi Abdul'zeez (Feedoh) &
Ayeesha Musa (Meesha lurv)
[4/8, 15:32] Feedoh: ⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha lurv
2⃣1⃣~2⃣5⃣
Nataso cikin so da kaunar iyayena domin subani kulawa iya kulawa akwai makwabtanmu, kusa da gidan mu gidan Alhaji Umar Dan chanji, mai kudine sosai yana da kirki sosai shi da mahaifina aminaine duk da kudinsa komai zaiyi sai ya shawarci mahaifina, amma matarsa bata da kirki ko kad'an ga rowar tsiya, yana da 'ya'ya uku biyu maza d'aya mace, babban sunansa Umar suna kirasa da faruq k'aramin kuwa sunansa Haidar macen ce karama kuma sa'ata tsakaninmu kwana biyu tare akayi sunanmu nida ita sunanta fareedah komai tare ake mana da ita wasa tare muke yi komai dakasani tare nakeyi da fareeda bata iya cin abinci sai dani koni ma haka, duk da hajiyansu batason taremu da ita amma bayadda ta iya dole ta barmu, har muka isa zuwa makaranta tare aka samu nida ita idan Abbu yakawoman abu tare zai Kawo mana nida fady koda nayi bacci Safiya nayi maaah zata d'akon tabani Niko da gudu zanyi gidan sun fady.
Ranar wata larava da yamma lokacin ina da shekara goma aduniya Abbu yadawo daga kasuwa yakawoman tsaraba, da sallamsr sa ya shigo gidan ina tsakar gida ina wasa naji sallamar sa da gudu nayi gunsa, na d'anesa ina murna tanace abbu sannu da zuwa da murmushin shi yace yauwa yar abbu wasa akeyi ne? Nace masa eh abbu yace toh ina yar uwar taki kike wasa ke kad'ai? Nace masa tund'azu muka rabu kai nakejira kadawo kabu tsarabarmu naje nakai mata dariya yayi yace to ae gani nadawo ina maaah dintaki? Nace tashiga bayi yanzu, muna cikin haka sai gashi ta fito
Bayan Abbu ya huta yaci abinci naji ya kwalan kira HUDAH da da Sauri na ansa na'am Abbu dagudu nak'arasa wajensa ina zuwa yace man to yar abbu ga tsrabar taku wasu dogayen rigunane masu kyau iri d'aya da takalmi mai tsini da igiya sai sarka da yan kunne fashion masu kyau komai iri daya yace man gashi nida yar uwata, rugumeshi nayi nayi Mashi godiya, sannan nad'au nawa na'ajiye sannan nad'au na fady na fita da gudu nayi gidansu dan na kai mata gudu nake yi sosai ban Ankara ba naji nayi karo da mutum nad'ago dannaga waye gabanane yayi masifar fad'uwa gani Wanda nayi karo dashi.
Lurv u Feedoh
Written by
Fiddausi Abdul'azeez (Feedoh)&
Ayeeesha Musa (meesha lurv).
®NWA®
Comments
Post a Comment