Posts

Showing posts from August, 2017

MATATA GIMBIYATA 69-70

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          6⃣9⃣➖7⃣0⃣ *END*   *FOUR YEARS LATER*       "Emaan ki tsaya mana zakiyi latti fa tun d'azu kink'i bari na sa miki button" Deenah kenan yayinda take ta faman shirya Emaan gashi ta kusa latti to school amma k'iriniya ya hana ta tsaya wa waje d'aya    Tsaye yake jikin mota yana kallon agogon hannun shi. Sighting yayi ya d'aga kai yana kallon entrance na gidan , komawa ya yi domin duba dalilin dad'ewar Emaan d'in yana bud'e k'ofa sai ta fice da gudu tana dariya. Da gudu Deenah tazo not considering akwai mutum a k'ofa taci karo dashi sai da suka Kusan zubewa k'asa Sadeeq ya tokare k'ofa da hannun shi ya gyara tsayuwar shi. Juyawa yayi yana kallon Emaan dake ta sheqa dariya yace "Princess!!" Buya  tayi a bayan motar shi kuma ya sake Deenah zai tafi. Hannun shi t

MATATA GIMBIYATA 67-68

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          6⃣7⃣➖6⃣8⃣   "You are indeed a blessing to me my princess, I feel like hunting all the happiness in this world just for a gift to you."    D'ago idanuwanta tayi ta aza kan fuskar shi dayake rigingine take kanta bisa cinyarsa tayi Murmushi, zauna wa tayi kan gwiwar ta tana facing nashi hannuwan ta sak'ale cikin nashi tace "Awe that's so sweet of you " janyota yayi jikin shi yana maimaita maganar ta yana kwaikwayon muryar ta hakan yasa ta rufe fuskar ta a k'irjin shi tana dariya, mutsu mutsu  ya fara yana dariya hakan yasa ta tsaya kallon shi   "Chakulkuli fa kika yi min" ya fad'a yana k'ark'are dariyar mutumiyar kuwa abun nema ya samu ta dinga tickling nashi da kyar yasa ta daina dalilin kwantarta da yayi gami da danne duk hannayen ta.   Like Arnav and khushi haka suka k

MATATA GIMBIYATA 65-66

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          6⃣5⃣➖6⃣6⃣    "Domin farin cikinki na hana kaina farin ciki na d'auki d'an da na mallaka duk duniya na bakishi, kin zo da kuka mijinki ya gaji da zama ba haihuwa, labarai dai iri daban daban masu narkadda zuciya, Abban Sadeeq yasa na bakishi kika nesantani dashi, all those years I stay silent under pain of loosing him, ni da bana tare dashi ban yi kyashi akan abunda ya Tara ba saike wanda babu hidimar ki da bai d'auke ba? Kin cuceni, Ashe haka d'an uwa yake ba alk'awari? Murmushi Sadeeq yayi yace "Wasu y'an uwan".. Ya nisa sannan yaci gaba da cewa "Zan bar gidan nan Mom, domin ganina a cikin shi ma yana sa memories su dinga dawo min ,I want a new life!"    Daidai shigowar Ramlah kenan tana kuka, da gudu Hajiyar ta rik'e ta tana tambayarta abunda ya faru cikin kuka Ramlah ke b

MATATA GIMBIYATA 63-64

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          6⃣3⃣➖6⃣4⃣   Hannunta yaja suka haura wani spiral staircase har wani had'add'en flat wanda da kallo d'aya ya sace zuciyar Deenah. "Cry no more GIMBIYA ta!  I promise never to hurt your feeling even for a second" D'agowa tayi tana kallon cikin idanun shi tace "Nan ina ne?"   "Gidanki ne" yabata amsa yana murmushin sannan ya sake ta yace "barin deb'o kaya a mota, ki shiga kiyi freshening up nasan kin gaji take some rest ni zanje in taho miki da Sadeeya" Ita dai bata fahimtaba, meye laifin wancan gidan? Amma fa wannan ya d'auke mata hankali sai dai yana fita tsoro ya kama ta da gudu ta bi bayan shi har ya kunna mota ta bud'e tayi zamanta a gaba, Murmushi yayi kawai ya fara tuk'a motar, bai d'aukeshi lokaciba ya isa gida, tare suka shigo su Hajiya anyi

MATATA GIMBIYATA 61-62

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          6⃣1⃣➖6⃣2⃣    Babu abunda ta d'auka sai binshi takeyi, koshi kanshi yasan ba abunda zata d'auka domin dama ba da niyya ta shigo ba ma ahaka har yayi gaba ya barta tana tafe kai a k'asa, bata ankara ba taci karo da mutum harta jefar masa da waya ta durk'usa k'asa ta d'auko wayar ta mik'a gami da d'ago wa dan bashi hak'uri.    Gaba d'aya in zaka bincika Deenah a Wannan lokacin ta riga tasha jinin jikinta, idanuwanta da bakin ta wangalele ta kasa ko da motsi mutuwar tsaye kam tayi yafi so Arba'in a lokacin nan dan danan jikin ta ya d'au b'ari ko had'iye miyau ta kasa yi balle magana. Ai kuwa ba shiri ta ranci na kare tun k'arfinta tasa a gudun daidai lokacin Sadeeq ya juyo sai ji yayi ta fad'o jikinshi gami da rungumeshi iya k'arfinta kuwa ta chakume rigar shi kai ka

MATATA GIMBIYATA 59-60

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          5⃣9⃣➖6⃣0⃣    Dakyar Deenah ta daddafa tayi sallar isha kanta har sarawa yake a fusace ta mik'e ta nufi wardrobe ta sauya kayan ta zuwa doguwar Aseel jallabiya bak'a sannan ta yi Rolling kanta da mayafin shi ta zari takalman ta k'irar Vinci ta saka, ko waigo d'akin batayi ba ta fice tana rik'e da wayarta, yadda ta fito a fusace tayi waje yasa Sadeeya ta haura don sanar da Sadeeq amma sai ta iske yana waya, tayi tsammanin zai kammala da wuri amma taga akasin hakan don haka tace "Madame fa ta bar gida"   Sadeeq Bai san lokacin daya zame daga kan gadonshi ba yace "What?!!! " Sadeeya ta maimaita masa abunda ta fad'a , kamar mahaukaci haka ya zura aguje ya d'au car keys yasa maigadi ya bud'e gate amma kafin ya fita Saida ya fara firing gateman wai bai iya aikin sa ba.   Haka yabi

MATATA GIMBIYATA 57-58

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS PAGE DINNAN NAKUNE BESTY ZARAH BUKAR MY LOVELY DOTA MISS XOXO ND SWEETHEART HAFSAT RANO #1love♥ #Ana tare #if you know you know kawai👍🏻          5⃣7⃣➖5⃣8⃣    Haka ta jira Deenah ta fito da bunches na dubu d'aya guda biyu a hannunta gami da mik'a mata.   Juya kud'ad'en Ramlah tayi kafin ta d'ago ta dubi Deenah tace "two hundred thousand? Me Wannan zai mana?"   "Haka naga daman bayarwa, kin mayi sa'a da d'ari Daya zan baki fa" Cewar Deenah dake k'ok'arin rufe k'ofar, tana rufe wa kuwa tayi tafiyar ta.   Ramlah kam gaba d'aya ranta a dak'ile yake bata gane me yake faruwa ba.     Babban tashin hankalinma sai da Hajiya taga kud'in, ita cewa ma tayi Ramlah ta maida kud'in daga baya kuma ta fasa ta amshe su gami da sa wa a jaka ta fice tana huci suka bar gidan.

MATATA GIMBIYATA 55-56

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          5⃣5⃣➖5⃣6⃣ *On phone*   Hajiya "Haba Abubakar! Yanzu kana nufin har ka fice ka tafi ba tare da ka min sallama ba? Baka saba haka ba Lallai akwai wani abu" Sadeeq "am sorry na yi latti ne kuma zan yi missing flight shi yasa, ban tsayaba, yanzu ma I'll hang up saboda...."   Bai k'arasa ba ta dakatar da shi ta hanyar cewa "Ina buk'atar wasu kud'ad'e kuma gashi baka nan ya zan yi?"   Wani shu'umin murmushi yayi yana tuna abunda yaji suna fad'a kafin yace "Hajiya kud'i akwai su, ki tambayi Deenah zata baki komai na hannun ta"   Wani irin juyawa kayan cikin Hajiya suka yi ,kanta ya Sara a hankali tace "Wace Deenah?" "Hajiya Deenah d'aya nake da shi fa, ita zaki tambaya komai a hannunta yake se anjima, take care"   Kashe wayar yay

MATATA GIMBIYATA 53-54

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS         5⃣3⃣➖5⃣4⃣     Koda Sadeeq ya dawo d'aki ya wuce bai fito ba sai da ya tabbatar ya shirya tsaf in black suit komai normal sannan ya ja trolley d'in shi zuwa k'ofa kafin ya ajiye, kai tsaye d'akin Deenah ya nufa inda ya iske ta kan sallaya, ko da suka yi ido hud'u mik'e wa tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta nad'e sallayar sannan ta ajiye tana k'ok'arin zare hijab.   Hannun ta ya fisgo har saida k'irjin su ya bugu dana juna, ba tare da ta d'ago ba ta fara k'ok'arin wafce hannun nata tana ja da baya yana matsowa har ta had'e da bango.    Ganin babu mafita yasa ta tsaya idanuwan ta kan hannun shi da yayi mata zobe a bango da shi. Zan tafi Egypt" ya fad'a cike da shu'umanci, sannan ya cigaba da cewa "Its more like a business trip sati d'aya zan yi but

MATATA GIMBIYATA 51-52

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          5⃣1⃣➖5⃣2⃣ I miss our conversation, i miss how we used to talk every minute of every day nd how i was able to tell you everything dat was on my mind. I miss you so much Maama💔 may Allah grant you jannatul firdausi Amin👏🏻    Alama yayi wa Sadeeya kan ta tafi, sannan ya k'arasa inda take zaune yayi facing d'in ta. Hannunta ya rik'e sannan da kyar ,murya ciki ciki yace "Ko ba komai  yau naga me k'auna ta tsakani da Allah ba dan ganin ido ba. Deenah na rik'e Hajiya tamkar mahaifiya domin tun ina k'arami take tare da ni, lokacin da mahaifiyata bata da lafiya, ganin yadda muka shak'u da Ummah Nah ta bar mata ni, duk wata kulawa ta takoma hannunta har na girma na zama mutum. Deenah Hajiyar da na sani da ba ita ce yanzu ba, wancan bata iya cin abinci har sai naci, bata barci in bani da lafiya sannan ko

MATATA GIMBIYATA 49-50

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          4⃣9⃣➖5⃣0⃣     Da Murmushi ta fito tana y'ar wak'arta daga ita sai dogon wando na jeans da vest ash mai kyau bata ma lura da cewa akwai mutum a gaban ta ba sai da ta iso dab da shi ta hangame baki ganin irin halin da yake ciki hankali a tashe ga uban gumi kuma kuka kawai yake tayi.    Iya rayuwar Deenah bata tab'a ganin cikakken namiji iri Mr Imam yana kuka kamar ran shi zai fita ba.    Jiki a sanyaye ta durk'ushe gaban shi tace "Miysa kake kuka? Miya faru da kai"   asalin damuwa Deenah ta kai k'ololuwa taga kukan nashi ba na k'arewa bane dan haka ta tura shi zuwa falon ta sannan ta rufe k'ofa suka k'arasa ciki itama taja kujera ta zauna tana aikin bashi hak'uri amma kamar ingiza shi take yi ganin haka yasa ta mik'e gami da rungume shi tana hawaye kan shi a cikinta tace "

MATATA GIMBIYATA 47-48

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          4⃣7⃣➖4⃣8⃣      Tun da ta shiga kitchen take sak'e sak'en yadda zata yi maganin Hajiya, cije leb'e tayi sannan ta fara haramar yin girki tsabar tsiya ruwa Deenah ta d'aura bayan ta soya mai da albasa sannan ta jajjaga attaruhu mai Uban yawa ta d'irka a ciki sannan ta gabza kayan k'amshi da seasonings hakan yasa duk yadda k'amshi ya kai Wannan girki ya kai. Cikin y'an mintina ta kammala komai. D'an kad'an ta saka a bakin ta don jin yadda yajin yayi ita kan ta saida ta kurb'i ruwa. Sannan tayi wata dank'areriyar Murmushi gami da zuba wa a plate ta fito d'auke da roban ruwa mai uban sanyi ta ajiye gaban Hajiya  sannan ta koma setin ta tazauna tana jiran wasan ya fara.     Cike da isa ta bud'e plate ,zo kaji yadda k'amshi ya rufe ko ina su Hajiya har yawu ya tsinke, bata tsaya

MATATA GIMBIYATA 45-46

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          4⃣5⃣➖4⃣6⃣     Haka plan d'in ya tafi smoothly Sadeeq har ya fara condemning Dr Bilal kawai rana tsaka Zeenat ta d'auke k'afarta cak daga zuwa asibiti, abu kamar wasa duk kulawar Sadeeq na hannun Mahmoud wanda shima ya san plan ne Amma bai san dalili ba, sai kuma Sadeeya y'ar aikin gidan, ko ranar da aka sallami Sadeeq daga asibiti Zeenat bata gida, da ta dawo ta iske shi cikin falo yana tambayar ta inda taje ko kallo bai isheta ba, haka Zeenat ta zama duk inda taga dama zuwa take Kuma a lokacin da taga dama, sannan kuma in ya tambaya sai tace aiki take yi. A kwana a tashi halin Zeenat gaba yake yi yanzu kam Sadeeq ya gama yarda da maganar Dr Bilal d'ari bisa d'ari ganin yadda take treating nashi kamar ba itace zee d'in da take fad'in ta fi kowacce mace sa'a ba, kamar ba ita ke fad'in bata jin

MATATA GIMBIYATA 43-44

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          4⃣3⃣➖4⃣4⃣      "Bilal ina ganin lokaci yayi da k'irk'irarren labarin cewa Abubakar Imam gurgu ne ya zama tarihi, ina ganin yanzu kam na samu abun da nake nema."   Dr Bilal ya yi Murmushi yace "da alama hak'ar ka ta cimma ruwa kenan?" Kai Sadeeq ya jinjina yana mai k'urban lemo.    Mahmoud da Ke gefe a tsaye yace "ni daman na dad'e ina cikin duhu ban san dalilin da yasa Sadeeq yayi k'aryar cewa ya samu hatsari ya zama haka ba. So tunda yanzu wasan rainin hankalin naku ya k'are ai sai a fad'a min dalili"      Mr imam bai ko tanka ba Dr Bilal ne ya fara bawa Mahmoud labari. *Flashback*      "Zaune yake kan kujera yana duba newspaper k'afa d'aya kan d'aya, duk da yana duba jaridar amma kunnuwan sa suna sauraron kalaman Bilal"      "Abokina

MATATA GIMBIYATA 41-42

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          4⃣1⃣➖4⃣2⃣   "Jar Uban can! Amma tunda aka haifen ban tab'a ganin makira irin wancan lankwashashiyar Deenah n ba! Ko munafurci ma tsoron ta yake. Amma tunda tace ita y'ar wasa ne ni kuma captain ce! Bazan tab'a barin ta ba wlh se na cimma buri na "   Ramlah dake tsaye jikin k'ofa ta saki doguwar tsaki tace "Ummah abun takaicin ma kin ga yadda take masa tausa yadda kika san wasu turawa Umma wallahi bak'in cikin da naji baki ji shi ba dan wallahi ni na so in shak'e Deenah d'azun, wai daman akwai wata kuchaka irin Deenah da zata iya tanka miki? "    Hajiya tayi dariyar manya tace "Yaro yaro ne! Ai kuskuren mu d'aya ne kawai, da tun farko ya kamata mu fara shafe Deenah daga rayuwar Abubakar amma tunda bamuyi hakan ba salon da ta d'auko shi zamu d'auka sannan mu shafe t

MATATA GIMBIYATA 39-40

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          3⃣9⃣➖4⃣0⃣     Zaune yake as usual kan wheelchair yana k'ok'arin had'a tea yayinda saman table d'in Ke cike da food, flasks iri iri Sadeeya zata fara aikin serving nasu.   Salamar Deenah ta sa duk suka mai da duban su ga inda suka ji Salamar amma me? Kowa sakar baki yayi dalala musamman Sadeeq da ya kasa k'arisa amsa Salamar ya d'auko kallo tun daga k'afafun ta har k'ugun ta sannan ya cigaba zuwa k'irjin ta kafin idanuwan su suka yi arba da juna.   "Assalamu Alaikum"   Ta sake maimaita wa nan ma da kyar ya iya amsa wa Hajiya da Ramlah ganin hankalin shi ya dugunzuma duk haushi ya kama su sai ji suke kamar su shak'e Deenah.   Ita kuwa cikin salon shak'iyanci ta durk'ushe har k'asa ta kwashi gaisuwa tana musu wani shu'umin kallo.   Hankalin Sadeeq bai gama tashi ba

MATATA GIMBIYATA 37-38

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          3⃣7⃣➖3⃣8⃣      Ya dad'e yana zaune yayin da take baccin ta a jikin shi, yasan magariba ta kusa dan haka ya mik'e da ita a hannun shi kamar y'ar tsana ,ya kwantar kan gado ya yi saurin koma wa kan wheelchair nashi ya zauna dan yasan zata iya farka wa any moment from now saboda baccin da tayi na wahala ne daman.     Juyawa yayi ya bar d'akin ya nufi nashi flat d'in don yayi wanka. Deenah kuwa bai dad'e da fita ba ta farka cikin magagin bacci ta mik'e don a lokacin an k'ira sallah ne ai kuwa k'afa ta rik'e ga wani ubansun ciwo ba shiri ta saki k'ara ta rik'e k'afar.    Yana shirin fitowa dan zuwa masallaci ya jiyo ihun wanda hakan yasa ya nufi d'akin Deenah, tana zaune yadda take bata sake yin motsi ba har ya k'arisa gaban ta suka fuskanci juna. D'ago k'afar yayi y

MATATA GIMBIYATA 35-36

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          3⃣5⃣➖3⃣6⃣      Ita kuwa Deenah na chan lungun gado tana kwance, tabbas taji shigowar Sadeeya kawai bata yi niyyar amsa mata bane.    Mr Imam da kan shi ya sa Sadeeya ta shigo da shi flat d'in Deenah. Tsaya wa yayi yana k'arema d'akin kallo kafin ya umarce Sadeeya da Cewar zata iya tafiya , babu musu ta fice direct gami da tura k'ofar ta rife kirif.   Shu'umin Murmushi Sadeeq ya sakar yana shafa  k'asumbar sa sannan ya kawar da kai yana kallon wayar ta dake jefe a k'asa kusa da gado.    "Ni iya rayuwa ta ban tab'a ganin mace mai irin wannan zak'ewa haka ba, kiyi laifi Kuma Ki b'ata rai har Ki takura kan Ki a k'asan gado.? Abunda zai fi kawai Ki tashi kije kiyi apologising ma Hajiya, Ki bata hak'uri kawai."   Deenah dake kwance a ranta tace "ba dai hak'uri ba?

MATATA GIMBIYATA 33-34

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸 💘MY WIFE MY PRINCESS💘 STORY BY JEEDDAH JA'O WRITTEN BY FEEDOH DEEDOH          (NWA) EDITED BY ROOKIEY KAXS          3⃣3⃣➖3⃣4⃣ Assalamu Alaikum my beautiful people, inaso inyi amfani da wannan damar na k'ara mik'a maku godia ta akan karamcin da kukaman text, kira na amsa ba adadi har da wanda ma sukazo tun daga wani gari dan ku tayani rashin Maama danayi nagode sosai Allah ya saka da alkairi yabar zumunci, wanda basu samu damar kira ba ko text kuma na gode maku saboda adua duk inda akayita tana zuwa banda bakin da zan gode maku sai dai kusani wallahi yar_ficika na k'aunarku kuma tana alfahari daku a duk inda kuke nagode! nagode!! nagode!!! #1love♥       Tun da Deenah ta shige d'aki bata ko lek'a k'ofa ba tana kan gado ta had'e kai da gwiwa ko kayan ma bata sa ba.   Shi kuwa Ramlah na kai shi, tun daga bakin k'ofa ya dakatar da ita nan ta juya ta koma k'asa wajen Hajiya. Yana shiga d'aki ya mik'e ya f