Posts

Showing posts from February, 2017

JARABAWA TACE 176~180

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                           (NWA)                      1⃣7⃣6⃣➖1⃣8⃣0⃣    Gudu sukeyi Allah kad'aine ya karesu saboda irin gudun da sukeyi ya shahara bakin gate d'in Alheri clinic suka tsaya, sungumarta Aflan yayi ya nufi ciki yana kwalama Nurse kira dasauri nurses suka taso suka amsheta suka sakata cikin gadon marassa lafiya, emergency aka nufa da ita, biye suke ana zuwa k'ofar emergency aka tsaidasu..    Wani irin kuka Fu'ad ya fashe dashi babu wanda bai ba tausayi ba kowa kuka yakeyi in ka cire Uncle dake ta faman lallashinsu...    Zama Fu'ad yayi ya dafe kanshi yana hawaye, dafashi Aflan yayi d'agowa yayi ya sakar mashi wata muguwar harara, murmushin k'arfin hali Aflan yayi yace "kayi hak'uri nasan laifi nane dana san haka abun zai faru wlh da ban bada shawarar haka ba" d'aga mashi hannu Fuad yayi yace "malam ya isheni haka dama nasan baka san Lady shiyasa ka b'ullo da hak

JARABAWA TACE 171~175

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                           (NWA)                   1⃣7⃣1⃣➖1⃣7⃣5⃣                  *BAYAN SATI BIYU*    Kwance take tana waya in banda shagwab'a ba abinda takeyi, tsoki Lady tayi tace "Intee kinsan k'arfe nawa yanzu zaki dameni da waya?" dariya tayi ta kashe mata ido ta juya ta cigaba da wayarta, cikin shagwab'a tace"nidai dan Allah kazo ina san ganinka wlh nayi missing d'inka" .    Dariya yayi yace "karki damu My love ina nan zuwa wajenki" dariya tayi wadda sai da ta fito mata da fararen hak'oranta tace      "Yaushe?"    Murmushi yayi kamar yana kallonta yace "kedai ki saurareni nace zanzo" shikenan sai kazo, haka suka cigaba da firarsu ta soyayya, iya shak'a Lady ta shak'a dan gani tayi da gangan Inteesar ta mata haka...    Nikaina na rasa dawa Intee ke waya haka..      Sai k'arfe biyu na dare Intee ta gama waya, bargo taja zata kwanta, yaye

JARABAWA TACE 166~170

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                           (NWA)               1⃣6⃣6⃣➖1⃣7⃣0⃣     Sanye take cikin red super kallon Lady tayi tace "Anty Lady nayi kyau?" D'aga mata kai tayi, zumb'ure baki tayi tana buga k'afa tace "pls Anty say someting mana" kinyi kyau shikenan? Ihu tayi wanda sai da yasa Lady ta razana, tsoki tayi tace "waike yaushe zaki daina ihu? Bakisan kin girma ba?" Dariya tayi kafin ta bata amsa taji sallamar su Yaya da gudu tabar d'akin tana oyoyo Mummy, tab'e baki Lady tayi ta tashi ta fita...    Da gudu ta isa gaban Yaya mak'alk'aleta tayi tana dariya, murmushi Uncle yayi yace "Intee karki karyaman mata" dariya tayi tace "Daddy nayi missing d'inta da yawa fa" toh ai gatanan yanzu kinganta, dariya Yaya tayi tace "ka kyaleman Baby yaushe rabon mu had'u" yehhh datz my Mummy..    Hannunta Mummy taja suka zauna, "yasu Maamma?" Suna n

JARABAWA TACE 161~165

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                           (NWA)                  1⃣6⃣1⃣➖1⃣6⃣5⃣    Ganin kukan bazai mata magani ba ta tashi ta nufi d'akin Yaya a hankali ta tura k'ofar ji tayi k'ofar ta bud'e shiga tayi zaune suke ita da Aflan babu mai ma wani magana, da sauri ta k'arasa wajen Yaya fad'awa tayi jikinta tana mai rera sabon kuka itamaYayar kuka takeyi sosai..    "Yaya dan Allah kiyafeman wlh bazan gafartama kaina ba idan kina fushi dani tabbas nasan ko iyayena nada rai iyakar rik'on da zasu yiman kenan dan Allah kiyi hak'uri bazan yafema kaina ba idan har ma auratan dasu ka gina aurensu kan amana da yardar juna sun sami matsala ta dalilina" duk Lady ce ke wannan maganan..    D'agota Yaya tayi ta share mata hawaye murmushi ta mata tace "ba laifinki bane ba Lady laifi nane dana kasa rik'e amanarki har na d'aga hannu na mareki" da sauri ta d'ago tace "wlh baki kasa rik'e

JARABAWA TACE 156~160

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                          (NWA)                     1⃣5⃣6⃣➖1⃣6⃣0⃣    Aflan ne ya shigo d'akin Yaya da sallama waje ya samu ya zauna kusa da ita yace "Mummy kiyi hak'uri dan Allah" d'agowa tayi ta kalleshi tace "karka damu Aflan nayi danasanin marin dana ma Lady gashi Daddynku yayi fushi wai dagaske na kasa rik'e amanar da akaban ta Lady?" Girgiza kai Aflan yayi yace "Mummy baki kasa ba kina iya bakin k'ok'arinki komi yafaru nine sila" sai kuma ya fashe da kuka lallashinshi ta dingayi itama tana nata kukan...    Tunda Uncle ya shiga d'aki ya kulle kanshi ya rasa dalilin dayasa Yaya take matsama Lady yanzu, kota manta amanace wajenta? Dole ya d'auki mataki akan abinda suke mata, dan abinda suke mata shi zai sa ta k'ara tsanar Fu'ad wanda shi kanshi yanasan aurenta da Fu'ad, yana tunani a haka har bacci ya d'aukeshi..    Yunwa taji zata lahanta ta  dan

JARABAWA TACE 151~155

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                           (NWA)                 1⃣5⃣1⃣➖1⃣5⃣5⃣    Horn sukayi maigadi ya bud'e masu gate cinna kan motar yayi cikin harabar gidan, saida yayi parking kana suka fito su duka sukayi cikin gida..     Zaune take tayi ta gumi  sallama sukayi amsawa tayi tare da d'ago kanta, "sannunku da dawowa" abinda tace masu kenan, Uncle kad'aine ya amsa mata Aflan da Yaya kuwa ko kallonta basuyi ba...    Da sallama tashiga d'akin kwance yake bai amsa ba haka kuma bai d'ago ya kalle ta ba, zama tayi tace "Aflan magana nakeso muyi dakai",  d'agowa yayi ya kalle ta "inajinki" abinda yace kenan...    Mina maka? Miyasa ka canja miyasa ka sauya daga Aflan d'in dana sanka? Idan har wani abu na maka yakamata ka fad'aman bawai kadinga man haka ba, kasani kaine komai nawa ban cancanci irin haka daga gareka ba ban cancanci rashin ko in kula da kake man ba..    Kallonta yayi yac

JARABAWA TACE 146~150

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                          (NWA)                      1⃣4⃣6⃣➖1⃣5⃣0⃣      Yana isa gida, parlour ya tardasu Uncle da sallama ya shiga amsa mashi sukayi zama yayi kusa da Uncle, shafa kanshi Uncle yayi yace "my Boy ya jikin Fu'ad?" Dasauk'i sosai Yaya tace "Allah ya k'ara sauk'i" Amin Mummy mungode...    Tashi yayi yace "bari naje d'aki nayi wanka" sai ka fito suka bashi amsa...     Corridor suka had'u da Lady rab'ata yayi ya wuce ko inda take bai kalla ba, Aflan ta kira sunanshi juyowa yayi yace "yadai?" Amm...dama... Sai kuma tayi shiru, baki da abun fad'a ryt? Girgiza kai tayi tace "mina maka haka?" Murmushi yayi dan yasan ba abinda zata tambaya ba kenan, "babu komai kinsan rayuwa komi canjawa yakeyi" yana kaiwa nan ya fad'a d'akinshi yana dariya..    Girgiza kanta tayi ta wuce parlour tana share kwalla, "Lady"     Ju

JARABAWA TACE 141~145

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                           (NWA)                    1⃣4⃣1⃣➖1⃣4⃣5⃣    Zaune ya tarda ta parlour tayi tagumi rab'ata yayi ya wuce sai da yakai bakin k'ofa ya juyo yace "zazzab'i ke damun Fu'ad kuma kisani duk abinda ya sameshi kece sila kuma dake iyayenshi zasuyi kuka" yana kaiwa nan ya juya ya tafiyarshi yana dariya...    Tashi tayi ta nufi d'akinta fad'awa tayi kan gado tana kuka mai tsuma rai saida tayi mai isarta kana ta share hawayenta..    Wayarta ta jawo ta kira besty ringing biyu Zainab ta d'auka, hello besty kina ina? Banji mi akace ba shikenan dama ina san ganin kine, kuma gashi baki gari saikin dawo kenan, kashe wayar tayi ta wurgata kan gado ta sake fashewa da sabon kuka..    Ita dai tasan basan Fu'ad take ba kuma haka bata k'inshi amma rashin lafiyarshi yana d'aga mata hankali...    Tafe yake cikin motarshi yana sauraron wak'ar Karode bello Godwin a hankali yake

JARABAWA TACE 136~140

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                          (NWA)              1⃣3⃣6⃣➖1⃣4⃣0⃣     D'akin Lady ya nufa suna biye dashi da sallama ya shiga d'akin kwance take ta kasa amsa sallama sai faman kuka da takeyi "Lady" ya kira sunanta tashi tayi zaune ganinsu tsaye yasa ta mik'e ta fad'a jikin Yaya tana kuka...    Bubbuga kafad'arta Yaya tayi tace "ya isa haka nan kukan" d'agata tayi ta share mata hawaye...    Hannunta taja suka zauna, zama Uncle yayi yakira sunanta d'agowa tayi ta kalleshi, miyasaki kuka? Kallon Aflan tayi, kauda kanshi yayi gefe. Sadda kanta tayi tana hawaye, yace "ba kuka na tambayeki ba"...    Hawayen ta goge tace "Fu'ad ne yace yana sona" nan ta kwashe komai ta gaya masu tana kuka...     Numfasawa Uncle yayi yace "toh miye laifin Fu'ad? Inaga yau nafara ganin yaron nan amma na yaba dana tsuwarshi  Nafeesa ya kamata kisan abin da kikeyi kinsan dole kiyi

JARABAWA TACE 131~135

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                          (NWA)                       1⃣3⃣1⃣➖1⃣3⃣5⃣    A falo suka had'u da Ammi ta fito daga kitchen rik'e da plate da sauri ta aje plate d'in hannunta, tazo ta kamashi ganin halin da yake ciki yasa hankalinta yatashi "Fu'ad miya faru dakai? Wani abu aka maka? Baka da lafiya?" Duk a tare ta jero mashi wannan tambayoyin..    Hawayen da suka gangaro mashi ya share, wuri ya samu ya zauna ya dafe kanshi zama tayi kusa dashi tace "Fu'ad wai miye? Kaman magana dan Allah ko naji sanyi mana"...    D'agowa yayi yana hawaye yace "Ammi bata sona tace bata sona ta tsaneni ba zata tab'a sona ba wlh Ammi inasanta santa yaman illa ki taimakeni karki rasani" kuka ya fashe dashi mai tsuma jiki..    Shiru Ammi tayi tana mai tausayin halin da d'an ta ya shiga tabbas tasan yana san Nafeesah amma bata d'auka san yakai haka ba in shaa Allah zata san ya zatayi  taga y

JARABAWA TACE 126~130

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                           (NWA) THIS PAGE IS FOR YOU RAMLAH YUSUF AYAGI THANKS FOR D LOVE AND SUPPORT  #1love❤                    1⃣2⃣6⃣➖1⃣3⃣0⃣    Kallonshi tayi tace "yau ni kake kira da Nafeesa?" Murmushin takaici yayi yace "ai tunda bakisan ki girmama nagaba dake ba banga amfani baki girman ba kema" girgiza kanta tayi tana hawaye, juyawa yayi zai fita "Aflan" takira sunanshi tsayawa yayi amma bai juyo ba, tashi tayi tazo gab dashi tace "tun muna yara muke tare bamu tab'a samun matsala ba dan haka yanzu ma bazan bari musamu ba zanje naji kiran da Fu'ad yakeman indai hakan zai saka ka farin ciki.."    Juyowa yayi yana murmushi ya kalleta yace "nagode sosai Anty lady" murmushi tayi tace "zan maka komai in har zai saka farin ciki" hawayenta ya goge mata yace "toh jeki d'an shirya kar yaga kinyi kuka" ba musu ta nufi toilet. Girgiza kai yayi yabar

JARABAWA TACE 121~125

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                          (NWA)                         1⃣2⃣1⃣➖1⃣2⃣5⃣     Dariya yayi yace "Amminah kalli duk yanda kikayi" murmushi tayi tace "nidai inajinka". Zama ya gyara yace Amminah yau nayi magana da Lady" da sauri Ammi ta kalleshi tace "are crious?" Dariya yayi sosai yace "am serious" bani labari abinda tace mashi..    Zama ya gyara ya kwashe komai ya gayama Ammi, yana gamawa ta kalleshi tafara dariya turo baki yayi ya mik'e, da sauri ta kamo hannunshi ta zaunar dashi b'ata fuska yayi yace "Ammi miye na dariya?" Dariya ta k'arayi tace "Allah Fu'ad baka gajiya da shirme yanzu ashe ba gaya mata kayi kana santa ba daga kaje gidansu kun gaisa shine kake ihu haka?" Turo baki yayi yace "Ammi ai da haka zamu saba" gaskiya ne abinda tace...    Fu'ad Ammi ta kirashi, amsawa yayi da naam kaban hankalinka magana zanyi dakai, zama ya gyar

JARABAWA TACE 116~120

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                           (NWA)                  1⃣1⃣6⃣➖1⃣2⃣0⃣    Tunda ya shiga gida Ammi tasan ba lafiya, kusa da ita yasamu ya zauna kanshi ya dafe, d'agoshi tayi ta sakar mashi murmushi tace "ba'asan namiji da tsoro ba lallai wannan yarinyar mai tsada ce tunda take saman my one nd only tunani" d'agowa yayi ya kalli Ammi fuskarshi da kaganta kasan yana cikin damuwa yace "Ammi na ganta, amma ganinta baiman dad'i ba Ammi, tak'i saurarena"...... Nan yakwashe komai ya gayama Ammi dayake itace abokiyar shawararshi...    Zama Ammi ta gyara tace "Auta kayi wauta miyasa zakace zaka kawo mata wata wayan? Konice abinda zan maka kenan" Ammi nafayi hakane saboda nasamu contact d'inta, Allah Ammi inasanta idan ban sameta ba saidai na fasa aure. kallonshi Ammi tayi tace "karkadamu in shaa Allah yarinyar rabonka ce" turo baki yayi yace "Ammi sunanta Nafeesa ko kice Lady&q

JARABAWA TACE 111~115

JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION                           (NWA)                 1⃣1⃣1⃣➖1⃣1⃣5⃣ WAYE FU'AD?         Alh Sani d'an k'auyen katsina ne jibiya, yana da mata guda mai suna Zulaihat auren zumunci akama Alh sani da Zulaihat saboda ta kasance d'iyar yayan babanshi, Alh Sani d'an kasuwa ne kuma katsina yake zaune da matarshi, Allah yabashi dukia mai tarin yawa, Alh Sani da Hajiya Zulaihat suna da yara shida Aisha itace farko sai Asma'au sai Ramlah sai maryam sai Amina, tun daga kan Amina Hajia Zulaihat bata sake haihuwa ba sai da ta shekara biyar kana Allah yabata ciki murna Alh Sani yayishi, cikin na shiga wata tara ta haifo d'anta mai kama da ita, murna wurin Alh Sani ba'a magana, ranan suna yaro yaci suna Fu'ad..    Haka Fu'ad ya taso cikin so da k'aunar iyayenshi da yayyenshi komi suka samo Fu'ad, amma duk da irin sanda ake mashi bai hana aka bashi ingattancen tarbiya da ilimi ba...    Yana girma ky