RASHIN GATA 171-175
🌼🌼RASHIN GATA🌼🌼
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```
*NAH*
```FOUR STAR'S```✨✨✨✨
*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*
```SADIYA ABDULLAHI SHEHU
(STYLISH BCH)```
*ZAINAB Y HASSAN*
*(AUTAR HAJIYA)*
```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```
171-175
Kallonta yayi tun daga sama har kasa yaga tasha wani uban hijjab kamar wadda zata gidan mutuwa tuntsurewa yayi da dariya yana kallonta hannunta ya kamo yana janta tana tirjewa akan cewa ya saketa amma yaki har sai da ya dangana da parlour sannan ya saketa da sauri jin wani d'an karan tsunkuli datayi mai ba tare da yayi zato ba.
Sameer! please me kakeyi a cikin gidan nan?
Zama yayi a d'aya daga cikin kujerun parlour, kafa d'aya kan d'aya ya dora ba tare da yayi magana ba ya tsaya yana kallonta, cikin ranshi wani tsananin dad'i yakeji. Wai bakaji bane? yaji ta fada cikin takaici dan bata son mijinta ya shigo yagan shi bata san mezata ce ba...
Cikin wani irin husky voice taji yace "gurinki mana" ido ta zaro tare da cewa "gurina kuma Sameer?" cikin d'aga kai yayi mata alamar ehh tare da mikewa tsaye yana gyara wuyan rigar shi.
Daf da ita ya karaso ita kuma tana ja da baya, jin ta tokare da bango yasa tayi saurin juyawa zata ruga ya cafkota ya matseta jikin kofar sitting room dake a kulle saurin rintsa ido tayi kirjinta sai d'agawa yake numfashinta na fita da sauri da sauri ya kai bakinshi saitin hancinta ya dan lasa tare da hura mata iska cikin idan ta dake a rufe.
yarrrr! taji cikin duk ilahirin jikinta har zuwa cikin kwakwalwar ta tayi saurin juya mai baya jita ke tamkar kofar ta tsage ta shiga, murmushi yayi dan yanzu hakan datayi ya tabbatar mai da cewa itace matar shi.
Ware hannuwa yayi ta baya taji ya rungumeta tsam tare da kokarin juyo da ita amma furr taki yadda hakan ta kasan ce.
Fuskarshi ya sakala kanshi cikin wuyanta, cikin wata irin murya yace mata," please Nana juyo ki kalleni karkija zuciyata ta fashe sabida tsananin kaunar ki da nakeyi, ya karasa fad'a murya can kasa tamkar mai ciwon hakori...
Wai shin Sameer zuwa kayi ka kashemin aure? yanzu so kake azo aganka dani cikin wannan halin ko kuma wani sabon wulakanci ne kazo har gidan aure na zaka dasa minshi!
"So what? Dan na kashe maki aure aydama ke tawace danna kashe maki aure kinga saina aureki" ya fad'a cikin rashin damuwa, duk kuwa da yaga irin halin datake ciki na tsoro. Da kyar ya iya cika ta tayi gefe tana sauke wani wahalallan numfashi tamkar kirjinta zai fito.
Cikin takaici ta kalleshi tace, " ina son tunatar dakai cewar hakan dakake ba shida kyau, kuma Allah bazai taba barinka da nufinka na b'atanci a kaina ba" tana kaiwa nan tayi hanyar bedroom d'inta idonta fal hawaye ga wani irin masifaffan so da kaunar Sameer d'in tana dawo mata sabuwa fil.
Kan gado ta fad'a tare da saka sabon kuka, afili kuwa cewa take.
"Allah kai kasan halin da nake ciki, Allah ka yaye min wannan mumunan halin dana shiga, Allah ji nake tamkar na sadaukar da kaina ga Sameer sai dai ina jin tsoran ka ina kuma hango irin azabar dakatanadarwa masu irin wannan halin.
Na shiga Uku ta furta hakan da karfi, shi kuma Sameer time d'in ya karaso da spare key ya bude ya shiga cikin d'akin, maida kofar yayi sannan yasa mata key ya zare shi tare da sawa cikin aljihun shi..
"Cikin sauri ta mike tana zare idanuwa hankalin ta a tashe ganin shi har cikin d'akinta, karasawa tayi da gudu wajan data ajiye phone d'inta, yana kallonta baice komai ba haka kuma bai hanata aiwatar da abinda take kokarin yiba.
Kara wayan tayi a kunne tare da cewa hello Mama cikin tashin hankali, a rude Mama tace "lafiyarki kuwa Nana!?" tace "a'a Mama kinga sameer ko ya shigo min d'aki kuma ni wallahi Allah ban kirashi ba" ta fad'i hakan cike da tashin hankali da rud'ani.
Jitayi Mama na dariya kafin tace "amma Nana shine dan Mijinki ya shigo d'akinki kamar bakida wayo zaki bugo ki sanar min tab to Allah ya kyauta miki nikam banda ta cewa wallahi..."
Kunya ce matsanaciya ta ziyarci zuciyar Nana, ai ko sallama bata yiwa Mama ba ta cilla wayar baya ta juya tana mamakin wannan katon al'amar wanda sam bata taba zato ba...
Cikin ranta kuwa cewa take yanzu murna zanyi ko kuwa fushi zanyi na rashin ko inkula da yayi man? bata yanke shawara ba taji ya rungumota ta baya yana murmushin sa mai matukar kyau da burgewa.
Cikin kunnan ta yace "to ya? Kin amince na zama abokin rayuwarki Ko kuwa?" cikin jin kunya tayi kasa da kanta amma batayi magana ba domin kuwa batada abin cewa.
Janta yayi suka karasa bakin gado suna karasawa ya kwanta rigingine sannan ita kuma ya janyota ta fad'o kan cikin shi nan da nan ta fara boye fuskarta cikin jikin shi dan bata kaunar su hada ido sabida haka nan taji tana matukar jin kunyar shi for the first time..
Yana shafa bayanta yana bata hakurin irin wulakancin da yayi mata tun farkon haduwar su har zuwa auren su daya gudu ya barta.
"Please My Doctor wallahi a dalillin son da nake miki ne yasa na gudu sanda akace an min aure batare da nasan cewar da kece ba sai yau.
Ina san ki mance komi ki kuma yafeman wallahi Yanzu kece komi tawa you are my everything and I always stay with you and I could spend the whole my life with you, kuma kisani ina sanki san da ban tab'a yima wata mace ba sai ke zan zauna dake cikin kowane irin hali na sameki...
Haka Sameer ya dinga tona asirin zuciyarshi..
Samun kanta tayi da rungume shi tsam cikin jikinta, yayin da wasu zafafan hawaye da suke zubo mata wanda ta rasa kona meye.
Sameer kam jin da yayi ta matse shi hakan ya tabbatar masa da cewa ta hakura kuma itama tanajin irin feelings din daya keji......
Tsam ta tashi daga jikinshi, da hanzari ya rik'ota fizgewa tayi ta nufi hanyar fita tashi yayi da sauri ya rik'eta "Ina zaki?" Kallonshi tayi tace "gidanmu mana" dasauri ya kalleta yace "what?" Kaji minace baka buk'atar na sake maimaitawa, naji Amma miyasa kika zab'i kitafi kibarni? Saboda bakasan darajana ba taya zanyi zaman aure da wanda ya furtaman kallaman tsana ba sau d'aya ba..
Duk'awa yayi ya rik'o hannunta Nana nasan ni mai tarin laifi ne wajenki dan Allah kiyi hak'uri kiyafeman kiman duk hukuncin daya dace dani Amma banda na rabuwa dake dan rabuwa dake daidai yake da rabuwa da numfashina, kiban dama zan nuna maki ba Sameer d'in da kika sani bane ba wannan sabon Sameer ne sai yanda kikayi dashi, hawayen data gani yana zubowa daga idonshi kad'ai ya isa ya tabbatar mata Sameer yayi nadamar abinda ya mata.....
❤XOXO👍
Four stars🌟🌟🌟🌟
Comments
Post a Comment