RASHIN GATA 131-135

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TANBARI*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

Assalamu Alaikum
Muna mai ba masoyanmu hakuri akan rashin post dinmu da baku gani akai akai muna busy ne amma in shaa Allah komi ya kusa komawa daidai in shaa Allah da komi ya zama daidai zaku dinga jinmu kullum Four stars na godiya yanda kuke nuna kulawarku akan wannan labarin namu mungode sosai #1love

THIS PAGE IS FOUR YOU RAMLAH YUSUF AYAGI♥
 

131-135

   Haka Mama ta dinga yi mata nasiha tana lallashinta, jitayi maganganun Mama zasu saka zuciyarta ta fashe saboda zafinsu, tashi tayi ta kalli Mama murmushi tayi tace "ni zan shiga d'aki" binta Mama tayi da kallo, juyawa tayi ta nufi d'akinta, kallonta Mama keyi tausayin d'iyarta duk ya cika mata zuciya ita dai kam baccin wani abu da bata aura ma Nana Sameer ba....
   Tana shiga d'aki ta fad'a kan gado wani sabon kukan ta saki sai da tayi mai isarta kana ta tashi ta nufi toilet alwalla tayi tazo ta tada sallah adu'a tayi sosai tana kai kukan ta ga Allah akan ya zab'a mata abinda yafi zama alheri ta dad'e tana adua daga nan ta tashi ta nufi kan gado tana tunin mijin da zata aura wanda take ganin tallarta aka mashi wasu hawaye masu zafi taji sun gangaro mata....

*****
   Yamma lik'is ta shigo gida kallo d'aya zaka mata kagane tana cikin damuwa saboda yanda ta rame. Da sallama ta shiga parlour'n amsa mata tayi cikin sakin fuska "sannu da gida Mama" abinda tace kenan tana daidai zama, "yauwa Nana" Mama ta amsa mata, zama tayi kusa da Mama kallonta Mama tayi tace "iyayen mijinki sunje neman aurenki jiya  yau suka dawo kuma ambasu dan an tsai da aurenki nan da sati uku masu zuwa" gabanta ne ya yanke ya fad'i, tashi tayi ta d'auki handbag d'inta tabar parlour'n...
   "Nana" Mama ra kirata , amsawa tayi da Naam jiki sanyaye ta juyo, "ya namaki magana amma banji kince komai ba?" Mama ta tambayeta..
   Murmushi ta k'ak'aro ta d"ora akan fuskanta "bakomai Mama Allah yasa haka shi yafi zama alheri" tana kaiwa nan ta juya ta tafi..
   Tabbas jikin Mama yayi sanyi dan tana ganin kamar batama tilon d'iyarta adalci ba amma ba yanda zatayi tana san Nana tayi ingantacciyar rayuwa, ko bayan ranta tasan su Umma zasu tallafi maraicinta...

*****
   Zaune take gaban Umma tana mata kuka, kasa lallashinta tayi sai da tayi mai isarta kana tayi shiru "Khadeeja" Umma ta kirata d'agowa tayi da rinannun idanunta ta kalleta..
   Ina cewa munkai k'arshen maganan nan? Dan Allah kima mamanki biyayya karki bata kunya kinga har an tsaida magana dan Allah karki sa mamanki taji kunya duka fa bikinki yau saura sati biyu kuma yau ake shirin kai lefe dan Allah kiyi hak'uri ki dan gana ki d'auka k'addaranki ce haka..
  Hawayenta ne ta share tace "shikenan Umma in shaa Allah bazan k'ara damuwa ba" rungumeta Umma tayi tace "yauwa yar albarka koke fa" haka dai ta dinga mata nasiha har ta samu ta amince da auren..
   Bankwana ta ma Umma ta d'auki jikarta, jitayi ta ci karo da mutum dasauri ta d'ago ganinshi yasa hankalinta yatashi rab'ashi tayi ta wuce "Nana" ji tayi gabanta ya fad'i dan tunda take da Sameer bai tab'a kiranta ba da sunanta sai yau, miya sameki haka kika rame? Kallonshi tayi da mamaki, murmushi tayi tace "kai ma ai ka rame" murmushi yayi yace "banjin dad'i ne" Allah ya baka lafiya abinda tace kenan ta rab'ashi ta wuce, mamakin yanda ya kulata yau basuyi hayaniya ba takeyi harta isa gida.....
   Koda ta shiga gida abinda tagani ne yasa tasan tabbas auren nan dagaske akeyi yinshi za'ayi..
   Sallama tayi, amsa mata Mama tayi da fara'a itama fara'an tamata wadda fara'an bata kai ciki ba..
   "Sannu da gida Mama" abinda tace ma Mama kenan, yauwa sannu Nana ya wurin aikin da kuma jikin Mummy, lafiya lau Mama...
   Hanyar d'akinta ta nufa "Nana" Mama ta kirata naam ta amsa..
   Zo nan, ba musu ta juya ta koma inda Mama take....
   Baki ga kayan lefenki ba? Murmushi tayi tace "Mama nagani" toh ki bud'a kiga idan akwai abinda bai maki ba sunce saiki fad'i..
   Komi yayi Mama, akwati sha biyu ai baza'a saka kayan banza ba so ba sai na duba ba tana kaiwa nan ta juya ta nufi d'akinta.....

FOUR STARS🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245