RASHIN GATA 136-140

🌼🌼RASHIN GATA🌼🌼

```NAGARTA WRIYER'S ASSOCIATION (NWA)```

*NAH*
```FOUR STAR'S```✨✨✨✨

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI SHEHU
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HASSAN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

136-140

Gado tafad'a tana hawaye sosai, tare da afkawa tunani. Yanzu ita batasan irrin rayuwar da zatayi ba, bayan *RASHIN GATA* data samu tsawan shekaru, ga kuma wata fitinar na shirin riskarta, auren da batasan waye mijin ba, kuka takara fashewa dashi.

A haka mama tashigo ta riske tana hawaye, cikin sanyin murya take kiran sunanta,
"Nana d'ago ki kalleni".
Sai da tajima kafin ta d'ago kanta tana kallon mahaifiyarta.
"Aure ne bakyaso? ko kuma mijin da Zan Aura miki?
Kai tahau girgiza Mata, "Mama duk abinda kikeso shine farin cikina nima shi nakeso".
"To wanan hawayen na miye ne?
Yak'e wanda yayi kuka ciwo Nana tayi, tace
"Mama ba komai, kawai ina tunani rayuwane".
Dogan ajiyar zuciyar Mama ta sauke, tace "Nana kiyimin alk'awari bazaki sake zubar da hawayanki ba, ki yarda cewa mahaifiyarki ba zatayi miki zabin wanda bana gari ba, ki yarda cewa duk duniya babu wanda yakaini kaunarki, promise me?
Sunne kai Nana tayi ta amsata da cewa " yes mamana I promise you bazan sake ba" duk cikin kuka take maganar. Rungumeta Maman tayi tana mai lallashinta da sakamata albarka a cikin rayuwarta da Wanda zatayi nan gaba.

Kin sanar da abokan aikinki daurin Aureki ranar Friday Kowa? Mama ta tambayeta.
"A'a ban gayawa Kowa ba" "yakamata ki fada don, iyayen yaron sunci basai sun kawo katin daure auran nan ba, jama'ar Chan ma ta Isa, aman kamar aboka nan aikinki KO ta whatspp zaki iya sanar musu".
Toh kawai Nana ta iya cemata tajuya ta kwanta.

Yau takasance sauran kwana uku Bikin SAMEER DA NANA, Nana batasan komai dagane da auran ba saboda duk wani shagali ba a gidansu sameer a keyinsa ba gudun kada yaran su gane. Itama Chan gurin mamanta babu wani shagali datakeyi Mata.

Driving yake, baisan mai ke damun saba, baijin zai iya karasawa office saboda yarda  gabansa ke faduwa Gawani matsanacin zazzabi da ciwon kai, jikinsa har rawa yake, Allah ne kawai yasa zaije gida lafiya saboda irrin gudun da sameer yayi ga idon shi yayi mungun jah, direct part dinsa yayi ya kwanta sai kuka yake, yana fadin iyayansa ba siyi masa adalici ba, kankame jikinshi yayi yana rawar sanyi, domin wani mugun zazzabi daya sake rufeshi.

*WASHE GARI*

Nana tashiga gidan aman bata tarar da Kowa a palon ba hakan yasata yin part din momy da Sauri duk tunanita killa jikin momy ne yatashi duk da itama ba lafiyar tacika ba, dan ko kwarin jikinta bataji.

Sameer tagani shima yana kokarin fitowa daga part din, idanuwa suka zubawa juna, kowa yana mamakin ramar Kowa daku Wanda kagani a cikinsu kasan yana cike da damuwa,  kallonta tadauk'e daga garesa, sanan tayi kokare bin gefansa ta wuce, batayi tsamani ba sai gani tayi sameer yajawo hannuta da karfe yajata zuwa kirjinsa, cak zuciyoyin junasu sai da suka tsaya ta second ne, yayinda Kowa yakasa yiwa dan uwansa magana, ita kanta nana takasa kwace jikinta daga nasa batasan kuma dalili ba, shine yayi karfen halin yin magana, maike damunke haka? Shiru tayi masa bataci komai ba, sake tambayarta yayi a karo na biyu, nanma shiru tayi masa, cikin tsawa yake fadin answer mee, batasan lokacin datakara rungumesa ba, sai kuma tasamasa kuka, dubanshi take idanuwanta cikeda kwalla hankalinta atashe aman ta kasa furta koda kalma daya sai hawayen dake sharara akan kuncinta, dan batajin zata iya fada masa mamanta tanason yimata aure dole........

FOUR STAR'S✨✨✨✨

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245