RASHIN GATA 141-145

🌼🌼RASHIN GATA🌼🌼

```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

*NAH*
```FOUR STAR'S```✨✨✨✨

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI SHEHU
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HASSAN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

Hello y'all sweetos

Muna mai baku hakuri na rashin jinmu da kuka dai nayi wannan yafaru ne  sakamakon dauke wayar yar_ficika da akayi, Yanzu kuma Alhamdulillah ta dawo dan haka zaku dinga jinmu kullum mungode da irin kaunarku akan wannan littafin namu #team RGT #1love♥

141-145

    D'agota yayi ya share mata hawayenta "kidaina kuka kigayaman damuwarki kinga yanda kika rame duk kinyi bak'i kifad'aman damuwarki namaki alk'awarin zan taimaka maki" kallo ta bishi dan gaskia bazata iya gaya mashi mamarta zata mata auren dole ba....
   "To ai kaima ka rame na kuma tambayeka Amma ka kasa fad'aman, murmushin k'arfin hali yayi yace "nagaya maki banjin dad'ine amma na samu sauk'i", to ai nima rashin lafiya nayi amma naji sauk'i...
   Murmushi yayi wanda yasan ba gaskia ta fad'a mashi ba, jawota yayi ya rungumeta k'am jikinshi suna jin bugun zuciyan junansu, sun kusan minti goma a haka rad'a ya mata a kunne wanda nikaina banji miyace ba..
   Dasauri ta d'ago tana kallonshi, ido ya kashe mata yana dariya, sunkuyar da kanta tayi k'asa dariya yayi ya shafi kuncinta ya barta nan tsaye...
   K'afafuwanta taja ta k'arasa cikin gidan da sallama ta isa d'akin Mummy dan tasan Umma bata nan, amsa mata tayi ta bata izinin shiga...
   Tana shiga ta gaida Mummy amsa mata tayi cikin sakin fuska tare da tambayanta Mama "lafiya lau take" ta bata amsa, magunguna ta bata ta mata sallama  dan tana da patient asibiti...

*BAYAN SATI D'AYA*
  Nana! Nana!! Nana!!! D'agowa tayi tace "Mama minene?" Zama Mama tayi kusa da ita tace "tun d'azu mai gyaran jiki ke jiranki Ummarku ce ta turo ta" nifa Mama bawani gyaran jikin da zanyi kubarni haka..
   Jawota tayi jikinta tace "haba Nana aikam baki ma Umma adalci ba ta d'auko mai gyara tun daga Abuja har yola kice bakiyi Dan Allah ki daure kije ta maki"....
   Tashi tayi batare da tace k'ala ba tabar d'akin ta nufi d'akin da mai gyaran jikin take...

   Gidajen biyu sai shirin biki suke idan ka fitar da Sameer da Nana da basusan mi ake ciki ba na bikin....
   Umma ce ta kira Nana a waya ta shaida mata ba zasu samu damar zuwa ba dan zasuyi tafiya, sunyi hakane dan karta fahimci mike faruwa...
  Haka aka cigaba da shirin biki amma Nana bata gayyaci kowa ba kuma ba abinda zatayi dan tace auren so ne akema shiri ba auren sadaka ba...

  Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya, a yau aka d'aura auren Nana Kadeeja da Sameer akan sadaki naira dubu d'ari da hamsin, inda dubban mutane suka shaida....
    Tunda aka tafi d'aurin  aure take kuka...
   Shigowar mutane  gidan yasa ta nufi d'akinta da gudu kulle kanta tayi ta fashe da sabon kuka mai tsufa rai....

   "Yanzu Sameer ka kyauta kenan? Kama kanka adalci kenan? Ace d'aurin aurenka ka kasa zuwa kuma ka kasa gayyatar kowa?" Umma ce ta tsareshi tana tambaya...
   Yak'e yayi wanda yafi kuka ciwo yace "Umma badai aure kukeso nayi ba? Nakuma yarda zanyi to tunda ga Daddy ga sauran dangi inaga aiba sai naje ba sun isa su wakilceni zuwan nawa ai baida wani amfani" yana gama fad'ar haka yabarta nan zaune sake da baki....

   Girgiza kai tayi tace "Yanzu kuma ya rage naka aure dai an d'aura in yaso ka mutu saboda k'iyayya" juyowa yayi ya kalleta girgiza kanshi yayi ya bar falon...

   Nana ki bud'e d'akin nan yan kai amarya suna jiranki shiru tayi kamar bata jita ba haka Mama ta dinga magiya da kyar ta samu ta bud'e d'akin...
   Shiga Mama tayi gannin bata shirya ba bai bata mamaki ba dan tasan za'ayi haka, toilet ta wuce ta had'a ruwan wanka fitowa tayi ta kalleta tace "jeki wanka ana jiranki" ganin fuskan Mama ba wasa yasa tasha jinin jikinta ta wuce toilet....

Four stars 🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245