MATATA GIMBIYATA 1-2

🌸💦  MATA TA , GIMBIYA TA!! 🌸💦
    💘 MY WIFE ,MY PRINCESS 💘

Story by
JEEDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

Bamu yarda wani ko wata ya juya muna labari ba yin haka babban kuskure ne, kuma muka kama mutum zai fuskanci hukunci..

BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM

         1⃣➖2⃣ dole sai kin aure shi

     Attitude miss DEENAH ISMAEEL!! am talking to you right here as a father! Idan da uban ki ne yayi wannan maganar ai babu musu zaki yarda , amma dayake ni kin raina min wayau tunda ba ni na haife ki ba ,shine bari ki nuna min halin ki na y'an duniya ko? Shegiya da ido kamar dattijon biri!!"
     Uncle Khamis ne ke maganar cikin hasala , daga gani ranshi a b'ace yake.

    Amma Uncle how can you make such drastic decision without my consent? Maganar aure na fa kuke yi! Kuma hakan ma da mijin da ban tab'a gani ba! That too mai shekaru irin na ubana!" Deenah ta fad'a tana mai d'aga hoton wani dattijo wanda zai yi about 49 yrs ,idanun ta taf da hawaye.

     Ke uwaki! Kin ci uwaki nace!! Har yanzu ashe baki rufe bakin ki ba? Munafuka ke a yanda kike har wani zab'e zakiyi ? Mutum a kod'e kamar fentin white house. Aure de kamar anyi an gama! In ma zaki mutu a chan ne kije ki karata ,Yarinya ta d'ebo duk munafurcin uwarta, Tashi ki bani waje ko nayi majejewa dake a nan wajen Shashasha!" Cikin tsawa Uncle yayi maganar hakan ya tsoratar da Deenah ba kad'an ba kamar zata kifa ta mik'e da gudu ta fice daga falo idanuwa sharbe sharbe da hawaye.

DEENAH ' s POV ....

        Da gudu na shigo d'aki kaina babu abunda yake yi se uban sarawa , fad'awa nayi a kan gado gami da bunne fuska ta cikin pillow babu abunda nake se faman kuka!
Shikenan nima haka rayuwa ta zata kasance kenan? Babu y'ancin kai babu sukuni ,tabbas k'unci ya aure ni , a rayuwa ban san lokacin da farinciki zai dawo min ba, gashi ina cikin kadaici babu kafad'ar da zan dafa in yi kuka , babu uwar da zata rungume ni yanda uwata ta fad'i ta mutu a cikin wahala da k'uncin rayuwa haka nima zan kasance.

    Kuka na ne ya tsananta sosai na mik'e zaune na nad'e kafata gami da d'aura kaina a gwiwa, My dreams are shattered already ! My dreams of being a physiotherapist is no longer trending! Am gonna end up like my own late mother! Married! Becomes the cook of the family , get pregnant, have no time for herself but for the husband and then after some times she end up heart broken by the man she called husband and in the end! Died and left me in the hands of the most wicked step mom! Bayan wannan kuma nima Y'ata ko yayan da zan haifa zasu kasance a hannun wata uwar daban kamar yadda na kasance ,daga nan kuma suma ayi forcing musu auren dole kamar dai ni ,haka abun zaita zagayawa! Tir da wannan rayuwar!"

      Jin an k'ira sallar azahar yasa na mik'e ina k'ok'arin bud'e kumburarrun idanuwa na da 'kyar na fad'a bayi ,bayan nayi wanka na dauro alwala sannan na fito direct closet na wuce na d'auko wata long sleeve Anarkaali dress na zira sannan na d'aura hijabi na fuskanci kibla domin gabatar da sallah! Na dad'e sosai a sujjada ina kai kuka na ga Mahaliccin mu ,ina rok'on yasa wannan auren da za'a min in babu khairan cikin sa yayi watsi da shi ya kuma sauya min da alkahairi " bayan na idar da sallah sannan na koma kan katifa ta na kwanta naci gaba da business d'ina wato kuka"

  UNCLE  KHAMIS POV........

     Deenah tana shiga ya dubi Aunty Hadiza ( his wife)

    Wallahi ba don gudun bakin jama'a ba! Da sai na batar da wannan yarinyar! Wai yanzu har tana da bakin da zata iya sa in sa da ni? Har zata iya musayar miyau da ni tsabar rainin hankali? Shegiya fuska kamar an silala karas! Lallai seta yaba wa aya zakin ta!  Aure kamar an d'aura "

    Aunty Hadiza se yanzu tai magana " ai Alhaji ka barni da ita! Kafin a kaita ma sena sauya mata kamanni! Ni d'in de take ji yanzu zan nuna mata true colors d'ina"

   Ai nasan zaki yi fiye da haka! Mudai mu tura ta  chan ko zamu samu hujjar cin wannan makudan kudaden da yaya ya bari , ni bazan bari wannan kyanwar ta kwashe min dukiyar d'an uwa ba,ai da kika ga ina sassauta mata kwana biyu ai sassautawar ta raka taki gona ce! Kinsan idan muka sake wani abu ya gifta Baba Yaji cewar bata son auren komai zai lalace!" Sosai Aunty Hadiza ta kufce da dariya sannan Uncle ya mik'e domin zuwa masallaci...........

   ***************

    Deenah! Deenah!! Kut amma wannan yarinyar anyi y'ar kwal uba!  Shine ina ta kwala mata k'ira kamar bata nan? Ni wallahy satin ma yayi yazo mu tura ki chan! Mu yada kwallon mangwaro mu huta da kuda! "
     Da gudu ta shigo kitchen d'in jiki na rawa kamar zata mutu se haki take yi " kiyi hak'uri aunty wlhy sallah nake yi shiyasa b....."

    Ta dakata sanadiyyar wata tsawa da A Hadiza ta yi ,jiki na b'ari tayi gum da baki . " Sannu sayyada wato zaki nuna min kin fini iya addini ko? Ke gaki musulma! Munafuka kawai ,tsabar renin hankali ni zan d'aura girki a gidan nan yau? Shine har kina son yin k'arya d'a addini " ta kwada mata ludayi a tsakiyar kai , wannan ya sanya Deenah rik'e  kai hannu biyu tana hawaye tsananin sara mata yake yi amma babu yanda zata yi ,don in da sabo ta riga ta saba"

    Tunkude ta tayi da k'afa ta wuce zuwa falo tana ta banbami ita kuwa Deenah babu b'ata lokaci jiki na rawa ga uban yunwa ga ciwon kai ta mik'e ta hau k'ok'arin daura dinner.........,



©M@J@H
F💘J💘R💘

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245