MATATA GIMBIYATA 7-8

🌸💦 MATATA GIMBIYATA🌸💦

💘 MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
          (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

           7⃣➖8⃣

ASALIN LABARIN

     Alh Umar haifaffen d'an damaturu ne yana da mata d'aya mai suna Zainab da yara biyu, Khamees ne babba sannan Ismaeel shine k'arami. Bawani kud'i Alh Umar  kedashi ba saidai rufin asiri, amma duk da haka yaba yaranshi ilimi boko da arabiya.
      shekarar da khamees yagama university Allah yayima mahaifinsu rasuwa ba k'aramin razana sukayi ba kwanan Alh umar talatin da rasuwa Hajia Zainab ta bishi sunyi kuka kamar zasu rasa ransu amma daga baya suka dangana suka barma Allah komai, daga nan Khamees yafara kasuwanci ganin yaba ma d'an uwanshi ilimi, ana haka Allah ya had'a Khamees da Hadiza bai tsaya bincike ba kawai ya aika neman aurenta kuma iyayenta suka amince, cikin kwanaki k'alilan akayi bikin Khamees da Hadiza..

      Kulawa sosai suke ba Ismaeel daga Khamees  har Hadiza, Ismaeel na 300level Hadiza ta haifi d'an ta mai kama da babanshi sak, zoka ga murna wajen Ismaeel ranan suna yaro yaci suna Saeed, tun daga nan rainon Saeed ya dawo hannun Ismaeel. cikin ikon Allah Ismaeel har yagama karatunshi bai samu wata matsala ba.
      Tunda Ismaeel yagama makaranta Khamees yabashi dukiyarshi ta gado nan Ismaeel yafara business import and export, ma'ana yana kai atamfofi materilas Ghana, South Africa yana kuma kuma shigo da nasu Nigeria cikin ikon Allah kasuwancin ya karb'eshi saboda yafi yayanshi nan fa Khamees da Hadiza suka fara yimashi hassada amma bai tab'a canja masu ba kuma komai nashi idan yasamu Saeed...

      Ismaeel ne tafe cikin motarshi saurayin d'an matashi kenan maiji da naira, tsaye suke bakin titi da Alama abun hawa suke jira, har ya wuce yadawo sallama yamasu amsa mashi tayi yace "yanmata ina zaku haka?" Murmushi tayi tace "wlhi kaganmu nan bak'ine mu biki mukazo shine muke neman abin hawa ya kaimu can gidan bikin" kallon su yayi tabbas ba yan garin baneba, daga wane gari kuke? Tambayar da yamasu kenan, Kausar tace "Maiduguri" murmushi yayi yace "toh kunsan gidan?" Girgiza kai tayi amma muna da address d'in, toh karku damu in shaa Allah zan kaiku godia ta mashi, sai a sannan d'ayar tayi magana, haba kausar taya zamu bi mutumin da bamu sani ba? Nikam ba inda zani, murmushi yayi karki damu yanmata niba mugu baneba trust me. Dakyar aka samu ta shiga motar...
      Tunda suka shiga mota Ismaeel ke masu surutu kausar na tayashi, amma d'ayar k'ala bata ceba, kallon Kausar yayi yace "wai yar uwarki bata magana ne? Ko maganan tsada takeyi" murmushi tayi karkadamu miskila ce haka take dariya yayi yace "aikam yau ta had'u da d'an naci" itadai bata ce komai ba, har suka iso gidan biki godia Kausar ta mashi girgiza kai yayi babu komai fita zasuyi yayi lucking motar juyawa yayi yace "baiwar Allah dan Allah ki daure ki gayaman sunanki" a dak'ile tace mashi "Falmata" lumshe ido yayi yace "nice name" bud'e motar tayi ta fita, exchaging contact sukayi shida Kausar kana sukayi bankwana....

     Falmata bata bar damaturu ba saida soyayya mai k'arfi ta shiga tsakaninta da Ismaeel, randa Ismaeel yajema Khamees da maganan auren Falmata nan yace mashi bazai aure ta ba akanmi zai auro yar maiduguri kowa yasansu da mallake namiji, nanfa Ismaeel yace "shikuma baiga matar aure ba sai Falmata"
     Bai ankara ba yaji saukari mari a kuncinshi dafe kunci yayi idon shi ya kad'a yayi ja kamar an watsa mashi barkono, tab'e baki Hadiza tayi tace "aidama nasan za'ayi haka tunda yace zai auro yar maiduguri komai zaiyi" saboda kowa ya sansu da mugun asiri, girgiza kai Ismaeel yayi ya fita daga gidan....

       Fitar Ismaeel bai zame ko ina ba sai gidan yayan babansu, cikin ikon Allah kuma ya sameshi nan ya gaya mashi komai, murmushi yayi yace "ka kwantar da hankalina in shaa Allah anyi auren nan angama" shida ya auro wadda yakeso wani ya hanashi? Gashi tunda ya auro ta ya daina mana abinda yake mana komai daga ita sai danginta, kaje kawai zanzo na sameshi har gida, godia Ismaeel yayi sosai bankwana yamashi ya aje mashi kud'i masu yawa ya tafi..
       Har gida kawu ya sami Khamees yamashi tatas, kuma ya shaida mashi aure ba fashi jibi ma in shaa Allah za'a kai kud'in neman aure kuma dashi za'a kai, ba yanda Khamees ya iya dan dole ya amince, kallon kawu yayi yace "Kawu amma dan Allah Ismaeel karyayi nisa dani ya zauna d'ayan part d'in can" Kawu yace "bakomai zan mashi magana Allah yamaku albarka" amsawa yayi da Amin,...

© M@J@H
F💘J💘R💘

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245