MATATA GIMBIYATA 3-4

🌸💦  MATATA  GIMBIYATA!! 🌸💦
    💘 MY WIFE  MY PRIINCESS

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

         3⃣➖4⃣

      Zaune suke kan brown mahogany wood dinning table yayinda Deenah ke faman serving d'in su , duk idanun su a kanta ne ita kuwa jiki na rawa take faman zuba abincin.
Wani dogon saurayi ne ya shigo ak'alla zai kai 23 yrs ya sha kayan thugs harda knuckles ring , ya baje a falo yana kallon su a dining area

   "Ke"! Ke Munafuka zo nan!  sunan kenan da kowa ke k'iran Deenah dashi shima ya k'ira ta , luckily ta kammala zuba musu abincin dan haka ta saka gudu ta nufi inda yake ta durk'usa gaban sa
    An gaya miki kyau ne dake da zaki wani zo ki zaune min a gaba? Kazama tashi min ki had'o min coffee yanzun nan!  Ba b'ata lokaci ta ruga zuwa kitchen su A. Hadiza kuwa se dariya suke yi khairat ma tana ta aika loma ko d'ago kai bata yi ,idan akwai worst mak'iyan Deenah toh bai kai khairat ba.

DEENAH's POV .......

    Cikin minti uku na kammala masa komai na d'aura coffee mug d'in a kan saucer sannan na saka teaspoon a gefe na ajiye two cubes of sugar na fito cikin rawar jiki na mik'a masa

   Kurb'a d'aya kawai yayi kafin na ankara se ji nayi an watsa min hot coffee a jiki Allah yaso  bai sami fuska ta sosai ba. Wurgi yayi da kofin in my direction hakan yasa na sunkuya cike da tsoro yayinda cup d'in yaci karo da marble floor a take ya yi dagadaga , ban ankara ba naji anyi Ball dani da k'afa hannaye na biyu duk na dafe su kan fashasshen kwalban ,kuka na ya tsananta naji duk na tsani wannan rayuwar .
    ke wato kin maida ni sa'an ki ko? Munafuka! Wato ni kike so in zuba sugar a coffee d'in da hannu na? Wannan d'in sabon falli ne ko kuma me? Sa'an ki d'aya yau y'an mutunci na suna nan Amma ai kin sanni sarai! Zan had'u dake anjima!  Duk maganganun da Yaya SAEED yake fad'a kawai jin su nake domin na saba ,bayan ya juya ya fice ne na mik'e na d'aure hannu na sannan na fara aikin kwashe kwalaben , ban jima da gama wa ba Aunty ta kwala min k'ira

   Tana daga zaune kan dining chair tana d'aukar sauran abincin da suka rage a plate ta had'a a plate d'aya sannan ta  ajiye a k'asa tayi wurgi da shi da k'afa , da sauri na d'auka na keb'e a lungu ni kad'ai se daka loma nake! Wannan ma yau d'in taga dama ne don wata rana abincin da ake dafawa karnukan gida shi take cewa naci amma duk muguntar ta babu abunda ya sameni har mayya take k'ira na!

***********

    Yau jumma'a yau ake shirin d'aura min aure da mijin da ban san shi ba balle halayen shi, keep maganar ko yana kaunata aside don nasan ba  makawa wannan auren ba na soyayya suka had'a min ba, sannan hoton da suka bani dattijo ne mai kimanin 49 yrs who knows mata nawa yake da su?  This taught filled my heart to the extend that yau ko kuka ma na kasa yi, tear duct d'ina ya daina zubar da ko d'igon ruwa, babu abunda nake banda dua ina kai kuka na ga mai duka mai kowa mai komai!

        Yayinda kowa yake murna a cikin gida , ina k'unshe a d'aki na had'a kai da gwiwa. Wata tsohuwa ce ta shigo tare da Aunty , ta inda suka shiga ba nan suke fita ba wai nasiha , " In har kikayi wani kuskure auren ya mutu toh lallai ki nemi wani wajen ba nan ba!" Kalaman ta kenan na k'arshe daga nan tsohuwar ta d'aga ni muka fita.
    Wani ikon Allah ban tab'a ganin aure haka ba! Babu kayan daki babu komai daga ni se ni kamar wanda suka bada ni sadaka , daga nan ne kuka na ya karu ban san cewa akwai sauran hawaye a idanuwa na ba se lokacin da ake fitar da ni daga gidan ubana mahaifi kamar ana kora ta! Babu wanda zan yi wa kuka yaji ni! Haka suka saka ni a mota ba tsimi babu dabara Aure de an d'aura!  Ango of which i regard to as mr unknown!!

     K'arfe 3:30 pm
At BEN KALIO HOUSING ESTATE
DAMATURU YOBE STATE......

      Wani makeken gate muka ratsa driver ya yi parking daidai entrace ,jiki na rawa yake yayinda na sako k'afa daga mota ,daga cikin dupatta na ( gyale na ) ina iya hango fuskokin su d'aya bayan d'aya

    Cikin zuciya nace " What a family ! Look how happy they seems ! Basu san yadda nake ji ba wlh da sun sani non of them will give such a wide grinn

     Har cikin main falour akayi leading d'in mu finally na tsinci kaina zaune kan lallausan italian carpet , haka dai suka sani a gaba suna ta surutu wancan yace kaza wancan ma haka

    Hmmm da kun san yadda nake ji a raina game da auren nan lallai baza ku b'ata lokaci ba! I mean like seriously? Har ma farin ciki sukeyi wanda na kasa fahimtar me yasa , uwar ango harda hawaye.
  A raina nace " amma de wannan matar ai d'an nata indai shine nagani a hoto ai yafi ta tsufa!"

Maganar mahaifiyar sa ne ya dawo dani daga nannauyan tunani da na tsunduma 

   Y'ata ya kamata ki huta , gobe in sha Allah zaku wuce a kaiki d'akin ki! Na gode miki sosai domin mata irin ku kad'an ne a duniya wanda duk da kunji yanda mutum yake kuke amincewa kuyi abu don Allah! Ni na san in Allah ya yarda Allah zai baki ladan abunda kika yi"

    Ba tare da na fahimce ta ba nayi murmushi gami da  amsawa da Ameen daga nan aka kaini wani d'aki inda nan ne na zauna nida wasu y'an mata biyu muna ta hira har bayan isha muka kwanta!

Zan iya cewa yau ne rana ta farko bayan rashin iyaye na da na tab'a kwana cikin dad'in rai da kwanciyar hankali! Amma tunani d'aya tak ya hana ni sukuni!

   Is it because d'an nata tsoho ne? Ko kuma dan  na yi auren dole ba tare da wani musu ba? Or akwai wata matsala ce? Kuma how sure am i, wannan Dattijon shine wanda aka aura min?" Wannan tunani dashi nayi bacci ...............

© M@J@H
F💘J💘R 💘

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245