MATATA GIMBIYATA 15-16

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         1⃣5⃣➖1⃣6⃣

       Ban farka ba sai da aka kira magrib, shima saboda kukan yunwan da cikina keyi ne da sauri na tashi na fad'a toilet nayi alwalla, nazo na kabbara sallah ina idarwa nafara adu'o'i ina nan aka kira isha tashi nayi na gabatar da isha ina gamawa nayi adua tare da neman nasara na nufi k'asa gabana na fad'uwa saboda bansan sake had'a ido da Mr Sadiq Imam...
      Luckily ina fita palorn ban ganshi ba hamdala nayi ga Allah, kana na k'arasa a daining table, ina zama na bud'e kuloli tuwon semovita ne sai miyan agushi da taji kifi, d'ayar kula kuma pepper soup d'in kayan ciki ne, zubawa nayi naci mai isata nikaina nayi mamakin abincin danaci, koda yake ba abin mamaki baneba cz tunda nazo gidan banci komai ba, sai azaba danake sha...

      Ina gamawa na dawo palor na kunna kallo na zauna, banjima da zama ba naji anyi sallama, amsawa nayi yayin da yake shigowa, k'arasowa yayi yace "Mrs Sadiq Imam right?" Saida  gabana yafad'i jin yakirani Mrs Sadiq Imam, murmushi nayi na sunne kai k'asa, dariya yayi yace "anyway congratz Allah ya baki miji kamili mai ilimi" amma fa saikin yi hak'uri da halin da kika tsinceshi yanzu saboda illar da mace ta mashi, tab'e baki nayi nace "wannan ne kamili? Mugu dai" duk a cikin zuciya nake magana, a zahiri kuma nace  "Thanks" in shaa Allah l'll try my best naga na kyautata mashi kudai tayani da adua, yace "in shaa Allah...

       Nacika ki da surutu baki san wayeni ba ko? Murmushi nayi nace "bakomai".. My name is Doctor Bilal, ni Aminin Mr Sadiq Imam ne and also nine doctor d'in dake kula da lafiyarshi, yanzu zamuje d'akin tare dake na dubashi sannan nabashi wasu methods na excersice which will help him recover fast, kuma kece zaki dinga taimaka mashi wajen excersice d'in. Da sauri na kalle shi nace "Ni?"
       Murmushi yayi yace "yes you" i know it's deficult amma daurewa zakiyi ina da yak'inin kece zaki canja shi ki daure Allah na tare dake. Ajiyan zuciya nayi nace "shikenan muje"...

     Da sallama muka shiga d'akin Dr na gaba ina biye, da murmushi ya amsa yace "Bilal na d'auka sai gobe zaka..." Bai k'arasa ba ganina da yayi bayan Dr d'aure fuska yayi kamar bashi baneba mai dariya yanzu...
      Dariya Dr yayi ya bugi kafad'ashi yace "Sadiq rigima" yanzu dai bari nayi abinda ya kawoni, nan yafara aikin dubashi tare da yan rubuce rubuce, yana gamawa ya kalleni yace "Madam zan tardaki palor yanzu kinji" d'aga kai nayi dama kamar yasan a tsorace nake..

      Ina fiya ya juya ya kalli Sadiq d'aure fuska yayi yace "haba Sadiq wai yaushe zaka daina abinda kake?" Kaifa ba yaro baneba yakamata ka san abinda kakeyi kamanta da abunda yafaru ka d'auka k'addaranka ce haka, yanzu kuma Allah ya maka canji da mafi alkairi dan Allah yanzu kaga yanda yarinyar nan ke tsoronka saikace taga zaki wlhi ka canja, dan da ganin yarinyar nan yar mutunci ce... Murya sanyaye yace "please abokina ka manta da komai ka sake sabuwan rayuwa kaji" tunda yafara magana Mr Sadiq baice komai ba kuma har yagama, yafi k'arfin minti ashirin da gamawa amma baice k'ala ba, murmushi yayi yace "nasan dama da fad'a zamu rabu amma kasani gaskia ce ko kanaso ko bakaso sai an fad'ama" yana kaiwa nan yaja briefcase d'inshi yayi gaba....
      Yana fitowa ya sameni zaune nayi tagumi, murmushi yaman yace "haba Amaryanmu miye na tagumi" kodai ciwon mijinki ne ke damunki? Dont worry in shaa Allah soon zai warke kinji, ajiyan zuciya nayi cikin raina nace "wannan mugun yanama zaune guri guda yana zalintata inaga ya samu k'afa"...

     Maganan Dr ce tadawo dani daga tunanin da nake, farar leda ya mik'oman yace "magunguna ne ciki ki tabbata yasha safe rana da dare" kuma kece zaki dinga bashi wannan kuma zaki dinga mashi massage dashi ne shima 3times daily har na tsawon sati guda kinga duk idan zaki bashi magani saiki mai massage, in shaa Allah nextweek zandawo. Karb'a nayi namashi godia bankwana mukayi ya tafi nikuma na kashe kayan kallon nayi d'aki ad'ua nayi na haye lafiyayyen gado na kwanta, banjima ba bacci mai nauyi yayi gaba dani....

      Ban tashi ba sai asuba ina idar da sallah na koma kan gado na cigaba da bacci, tara (9:00am) daidai na tashi wanka na shiga ina fitowa na bud'e wardrob d'in nan ma wata doguwan riga na jawo color d'in purple sai stones suma purple nd white ina sakawa ta zauna jikina cif cif dama kamar danni aka d'inkasu, downstaire na nufa cikin ikon Allah baya palorn nan na zauna nayi break fast ina gamawa na d'auki ledan magungunanshi na nufi d'akinshi gabana na dukan uku uku...
     Sallama nayi na shiga d'akin, bud'e baki yayi zai amsa ganina da yayi tsaye yasa ya zabura laptop d'in dake hannunshi ya wurgoman kad'an ya rage ya samu k'afana, duk ta tarwatse k'asa, niko sai kyarma nakeyi, ubanmi ya kawoki? Abinda naji yace kenan, cikin rawar murya nafara magana dama dama, tsawa ya dakaman wadda tasa na kusa sakin fitsari dama mi? Dama doctor ne yace nazo na baka magani kuma na maka massage a k'afafuwanka har na tsawon 1week kuma 3times daily...

       Shiru yayi can yace "ban amince ba kuma idan kece zakiyi banaso" dan haka aje magungunan ki ficema daga d'aki, wata zuciya tace mashi "Ah Ah" Sadiq kabari tayi kaga konan ka bautar da ita dama abinda tazoyi kenan gidan kenan...

      Ina aje magungunan na juya zanfita nakai k'ofa naji yace "dawo kiman" duk'awa nayi na d'auki ledan magungunan na k'arasa cikin d'akin,  harara ya wurgaman yace "da kin gama ko second karki k'ara a d'akina kinji ni? D'aga kai nayi alamar "Eh" b'alla mashi magani nayi na mik'a mashi amsa yayi baiko kalli inda nake ba, fridge d'in d'akin na bude na d'auko ruwa bud'ewa nayi na zuba a cup na kai bakinshi, harara ya wurga mani kana ya bud'e bakin, yana saka maganin na bashi ruwa yana gamawa ya wurgaman harara yace "miye kika tsareni da ido?" Nidai bance komai ba na cigaba da yimashi massage a k'afa....
      Ina mashi massage ina satar kalllonshi runtse idonshi yayi alamar yanajin dad'in abun saida nagama tsaf na d'ago da niyar nace mashi nagama, ina d'agowa muka had'a ido dashi, kunnena ya murd'e saida nasaki yar k'aramar k'ara yace "banace ki daina kallona da wannan ugly face d'in naki ba, ina cewa nace maki da kingama ki fitarman daga d'aki ko second kada ki k'ara shine kika tsareni da kallo...

      Ina hawaye nace "dan Allah kayi hak'uri dama zance maka nagama" idan akwai abinda kake buk'ata kafad'aman tsoki yayi "mtchw" mi zan buk'ata wajenki? Aibaki da dashi dan haka get out of my room, kafin ya ida na ruga da gudu....
      Dariya ya bushe da ita saida yayi dariya mai isarshi kana yace "matsoraciya" ashe haka take da tsoro? K'afafuwanshi ya kalla yaji duk sun d'an saki, murmushi yayi yace "ashe dai ta iya massage haka?" Dole ta zama mai man massage....

     Ina shiga d'aki na maida k'ofa na rufe fad'awa nayi kan gado nace "mugu azzalumi sai Allah ya sakaman, kuma anjima saina maka mugunta tunda kake cutata."

©M@J@H
F💘J💘R💘

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245