MATATA GIMBIYATA 17-18

🌸💦MATATA GIMBIYATA🌸💦

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

            1⃣7⃣➖1⃣8⃣

     Zaman shiru ne ya ishe ni don haka na yanke shawarar zagayawa cikin gidan bak'in mayafi na d'auko na yafa sannan na fice gami da janyo k'ofar.
      Daidai step d'in k'arshe na d'ago idanuwa na wanda suka sha ado da Mascara by Mary Clair na aza su cikin makeken falon amma me? Idanuwan mu ne suka ci karo da na juna tuni jiki na ya d'au rawa na fara taking steps backwards.
   " Ke!! " ya daka mani tsawa hakan yasa na tsaya chak idanuwa na a rufe . Where did you think you are going? Ya tambaya "
  Cikin zuciya ta nace " Yaushe kuma ka fara karanta minds ?  Kuma ma me ya shafeka da inda zani!"
  Murmushi yayi yace " Nasan me kike tunani! Yes babu abunda ya shafeni da inda zaki! Kawai de bana son a lokutan da nake having peace a dinga shige man harkoki! Saboda haka go back in bana falon se kiyi abunda ya kawo ki! "

    Yanzu don kana zaune a falo tsabar bak'in hali shikenan kar kowa ya shigo? Allah ya sawwak'e !" Ta fad'a cikin zuciya kana ta juya zata koma fuska a murtuk'e kamar zatayi kuka ta koma d'aki ta fad'a kan gado tana ta sak'e sak'e........

      Zaune yake as usual kan wheelchair nashi yana kallon program na The Doctors. Shirun ne  ya ishe shi don haka ya k'ira Sadeeya ( Mai girkin gidan )  da sauri ta fito tana goge hannayen ta a jikin kitchen towel , durk'usa wa tayi a gaban shi tace "Gani Sir" ta fad'a kai a k'asa.
    Ajiye wayar sa yayi kan centre table ya ce " Ga ATM card nawa kije Shoprite zakiyi min siyayya ga list din a kan kujera " yana kai wa nan ya maida duban shi ga TV Sadeeya ta mik'e da zummar komawa kitchen ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa

      where do you think you are going?  Sir akwai abinci a kan cooker shine zan sauk'e kum..." Dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu sannan yace " Ki dawo ki d'auki abunda na saki ki wuce kafin raina ya b'aci , bana son ki 'kara koda second biyu!  Jiki na rawa ta d'auki card d'in da list ta fice domin kuwa tasan halin sa , a da can ba ita kad'ai bane mai aiki duk shi ya koresu don haka itama dole tayi taka tsantsan in ba haka ba yanzu yayi waje road da ita...........
      Ina kwance har k'arfe sha biyu sannan na yanke shawarar dawowa ko ya bar falon amma me?
  Kaurin k'one wan abinci duk ya mamaye downstairs d'in , zaune na hango shi ko a jikin sa duk warin nan ko a jikin sa , ganin yanda hayak'i yake fita daga kitchen yasa na sa gudu , har nakai bakin k'ofar kitchen d'in yace "
" Ke wace irin bagidajiya ce? Shin idonki bai nuna miki makunnin ruwa bane a k'ofar ? Toh in baki sani ba yanzu ki sani an saka su ne saboda emergency  na fire outbreak kuma automatically yake kunna kan shi ya kashe wutan , no need ki d'auki wata flamingo leg naki kice zaki shiga coz wutan ya mutu! Bak'auyiyar yarinya kawai!

        jiki a sanyaye na juya zan bar falon yace " Ina kuma zaki? Wa kike tsammanin zai goge mess d'in kitchen d'in?" Zaro idanuwa nayi Like seriously wai me wannan mutumin yake nufi da ni ne? "
   Ba tare da na furta kalma d'aya ba na koma kitchen d'in na fara aiki komai seda na tabbatar ya koma normal nayi mopping sannan na sauya tukunya bani na gama aikin ba se k'arfe biyu hakan ma na je nayi sallah sannan na cigaba, ina fitowa direct na wuce Upstairs na tube kayan jiki na gami da fad'awa bathroom nayi wanka , fitowa na ke da wuya naji ihun mutum, babu shakka muryar Sadeeya ne don haka na fice d'aure da k'aramin towel don ta tsorata ni . a d'akin shi naji tana k'iran suna na " Hajiya! ( kamar yadda ta saba )  a firgice na shige d'akin only to se Mr Imam a kwance k'asa ruf da ciki ya runtse idanuwa kamar yaji ciwo ga kuma wheelchair a jefe  guda.

       Hajiya nima Nazo kawo mishi orange juice kamar yadda ya buk'ata na same shi a haka"  cewar Sadeeya a rikice Ido na mata da  cewar ta fita , haka ta fice gami da rufe k'ofar , iya k'arfi na, na ciccibeshi  sai nishi nake domin kuwa nauyi ne dashi ba kad'an ba , da 'kyar na iya jinginar da shi jikin gadon sannan na sake k'ok'arin d'aga shi gami da maida shi kan gadon , Duk nayi gumi gashi k'arfi na duk ya tafi ,ina kwantar da shi na zube a kansa jiki ba kwari duk gashin kaina a fuskar sa numfashin mu na gogan na juna , yayinda 'kamshin fresh mint na bakin shi ya bugi hanci na lumshe idanu nayi.

     Ji yayi zan zame k'asa don haka ya yi wrapping hannun shi guda around my back yana shak'ar 'kamshin Bakhur dake mamaye cikin gashi na , wannan feelings d'in yau kad'ai na taba jin sa , sam ya kafe ni da idanuwa , mun kai mintina biyar a haka kafin na ce
" Excuse me" jin muryata yasa ya hankad'o ni k'asa yana watsa man harara duk jiki ba kwari na fita se kare jiki na nake yi..

      Ina fita ya lumshe ido, da sauri ya bud'e sakamakon k'amshin dayaji jikinshi nayi, cire riganshi yayi haryanzu k'amshin na nan, lumshe ido yayi yace "turaren yarinyar nan yana da dad'i how i wish na dingajin shi kullum" wata zuciyan tace Sadiq ka mance matsayin da ka ajeta? Da sauri ya kauda tunanin ya wurgar da riganshi yana huci kamar tsohon zaki....
      Ina shiga d'aki na fad'a kan gado wani irin farin ciki na shiga, tunano abinda ya shiga tsakaninmu na dingayi, rintse ido nayi ina k'arajin feelings, da sauri na tashi na shiga toilet nayo Alwalla na tada sallah  bayan na gama na nufi downstair...

      Ina sauka na had'u da Sadeeya har k'asa ta duk'a ta gaidani, cikin sakin fuska na amsa, tambayarta nayi Sadiq yaci abinci? Sadeeya tace "yace dai na kai mashi d'aki a can zai ci" amsawa nayi da "ok" na juya na tafi d'akin cikin tsoro. Ina shiga nayi sallama shiru akayi k'ara sallama nayi cikin zafin rai yace "malama ki shigo idan zaki shigo bansan yawan magana" tab'e baki nayi nace "shi duk yanda ka mashi baka iya ba...
      Shiga nayi zaune yake yana latsa waya, gaidashi nayi amsawa yayi  da lafiya, girgiza kai nayi na d'auko magani na mik'a mashi kallo na yayi yace "a k'auyenku ana shan magani ba'aci abinci bane?" Girgiza kai nayi nace "ai na d'auka kaci" banci ba abinda yace kenan, duk'awa nayi na zuba mashi abinci ina gamawa na mik'a mashi kallona yayi yace "ai yana daga cikin aikinki kibani abinci" da sauri na kalleshi harara ya wurgamani yace "zakiyi ko kuma zaki tsareni da mayatacce kallonki?"  zama na gyara na dinga bashi abinci har saida ya k'oshi na bashi ruwa yasha....

      magani na b'alla mashi na mik'a mashi, k'in amsa yayi bud'e baki yayi na saka mashi maganin na bashi ruwa, ina gamawa nafara mashi massage saida na tabbatar maganin ya shiga jikinshi sosai kana na mik'e na nufi hanyar fita..
      Ina kaiwa bakin k'ofa yace "ke mummuna" cikin b'acin rai na juyo, kallo na yayi yace "wajen takwas zakizo kiman cz zan kwanta da wuri" kuma kika k'ara koda second guda ne wlhi l'll show u my true color, cikin raina nace "yo akwai true color d'inka bayan wannan?" Murgud'a mashi baki nayi na fice d'akin da gudu...

      Murmushin mugunta yayi yace "zaki gane kurenki yarinya" zakisan kin murgud'aman baki...

©M@J@H
F💘J💘R💘

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245