MATATA GIMBIYATA 11-12

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

            1⃣1⃣➖1⃣2⃣

       Suna fita suka ga wasu mutane su biyu sai kuma mutum kwance k'asa, ga Khamees sai rusa kuka yakeyi, matsowa tayi tace "miyafaru?" Babu wanda ya amsa ta, saidai taji d'aya daga cikinsu yace "hak'uri zakuyi accident ya samu kafin ya k'arasa mutuwa shine ya bamu address d'in gidannan" da sauri ta k'arasa dan taga waye...
      Tana bud'ewa ta ganshi kwance kamar yana bacci idonta ta k'ara murzawa taga kodai mafarki take, tabbas ba mafarki bane ba Ismaeel d'inta ne. Kuka ta fashe dashi tace "haba Ismaeel ya zaka mana haka? Ya zaka tafi kabarmu cikin duniyar nan mai cike da k'unci pls katashi nasan baka mutu ba" kuka take sosa ashe dama mutuwa kakeyi shiyasa kake ban amanar Deenah. Matsawa Deenah tayi inda gawar baban take ta kwanta bisa shi tace "please Daddy wake up nasan baka mutu ba wasa kake mana", saboda malaminmu yace duk wanda ya mutu bazai dawo ba, kai ko nasan ba zaka mutu yanzu ba baza ka mutu kabarmu wajen su Uncle ba dan zasu cigaba da zalintarmu  please Daddy ka tashi, babu wanda Deenah bata saka kuka ba, jawota Falmata tayi jikinta tace "kiyi hak'uri Deenah Daddynki ya rigamu gidan gaskia" yanzu zamu shiga wata jarabawan, d'aga hannu tayi sama tace "Ya Allah kabani ikon cinye wannan jarabawan, ka bani ikon cikama Ismaeel burinshi na ganin naba Deenah ilimi mai amfani...

      Haka aka shirya Ismaeel suna gani aka d'aukeshi aka tafi dashi gidanshi na gaskia. Yan maiduguri sunzo saida akayi sadakan uku kana suka sami Khamees dan shaida mashi suna so su tafi da Falmata, Khamees yace "ba matsala amma ba zasu tafi da Deenah ba saboda shine babanta" tunda Falmata taji bazata tafi da Deenah ba tace "bazata je ba itama saboda tanasan cikama Ismaeel burinshi" , dan dole suka tafi suka barsu..
      Rasuwa  Ismaeel da kwana bakwai Khamees yazo ya karb'e duka takardun k'adarorin Ismaeel, acewarshi shine ya dace da ya rik'esu ba Falmata ba, haka Falmata ta bashi ba tare da ta nuna wata damuwa ba, burinta kawai taga ta cika ma mijinta burinshi na ganin Deenah tayi karatu...

      Haka rayuwa ta cigaba kullum su Falmata cikin k'unci suke sunyi bak'i sun lalace kullum da azabar da ake masu ita da d'iyarta. Abinda yafi d'aga mata hankalin yanda Khamees ya cire Deenah daga private school ya mai data LEA ba yanda ta iya haka ta hak'ura amma abin burgewa tun da Deenah ta taso mai k'ok'ari ce komai da an fad'a mata take d'aukewa sab'anin Khairee da bata gane komai....

      Bayan rasuwar Ismaeel da shekara biyu, kwance take k'udundune Deenah ce kusa da ita tana mata fita da kyar ta d'ago ta kalli Deenah kamo hannunta tayi ta matse cikin nata ta kusa rabin awa haka, can ta sake kallonta kiranta tayi da "DEENAH" amsawa Deenah tayi da naam, kiyi hak'uri da duk halin da zaki tsinci kanki, na tabbata Allah na tare da ke ba zai bari ki wulak'anta ba, ki rik'e mutuncinki duk inda kika samu kanki, ki rik'e ibada in shaa Allah zakiyi dariya watarana cikin kuka Deenah tace "Mummy miki keson gaya mani? Kema zaki barni kamar yanda Daddy yabarni dan Allah Mummy ki zauna dani karki barni" hawaye Falmata ta share tace "Allah bai barin wani dan wani yaji dad'i" da Allah na barin wani da mahaifinki ya zauna damu  inaji araina na kusa barin dunia kamar yanda mahaifinkin yabarta, dan ciwon zuciyar nan ba zai barni ba shiyasa nake maki nasiha da ki kula da kanki da mutuncinki dan nasan babu wanda zai damu dake...
      Kuka Deenah keyi sosai, cikin sheshek'ar kuka tace "ya rayuwata zata kasance babu iyayena a duniya?" Inama mutuwa zata d'aukeni nima dana fijin dad'i, jawotw Falmata tayi jikinta tace "kidaina fad'an haka d'iyata Allah na tare dake kuma yasan halin da kike ciki shi zai kareki"..
      Tashi ki d'auko man ruwa, jiki ba kwari Deenah ta mik'e, tana tashi taji mahaifiyarta ta fara kalmatush shahada, da sauri ta k'araso inda take amma kafin ta iso rai yayi halinshi tabbas a yan k'ananan shekarunta tasan mahaifiyarta ta mutu. Kuka ta saki mai tsuma rai tace "shikenan na dawo banda kowa" mutuwa ya zakiman haka kin rabani da iyayena miyasa baki bari na rayu da su ba? miyasa baki had'a dani ba? Haka ta dinga sabbatu, tafiya tayi part d'in Hadiza tana kuka tana isa ta daka mata tsawa dole Deenah ta had'iye kukanta, cikin kuka tace "Mummy ta rasu" da sauri Khamees ya mik'e ya nufi hanyar fita binshi sukayi, yana isa ya tab'ata, tabbas ta rasu abinda yace kenan....

      Haka aka shirya Falmata aka kaita gidanta na gaskia, duk wanda yaga Deenah sai ta bashi tausai dangin Falmata sunzo, sunyi sunyi Khamees ya basu Deenah amma haka yak'i amincewa sukayi fushi suka tafi... Tunda Falmata ta rasu Deenah ta koma gidan Khamees da zama...

      Haka rayuwan Deenah ta cigaba kullum da sabuwar azabar da suke mata, wankin khairat ita keyinshi ga duka da Saeed ke mata, da ta d'anyu mistake zasu fara dukanta...
      
     Kullum cikin nacin karatu take saboda burinta ta cikama mahaifanta burinsu, amma ba kullum ake barinta zuwa makaranta ba.
     Shekarar da sukayi SSCE Uncle Khamees yace aure zai mata dan baiga amfanin karatun ta ba, tayi kuka ta rok'eshi akan yabarta ta cika burin mahaifanta tazama cikakkiyar likita, ranan saida tasha duka dan taron dangi suka mata shida Anty Hadiza saida suka ga bata, motsi kana suka kyaleta, kuma ya shaida mata aure babu fashi, da kanshi ya nuna mata hoton mijin da zata aura, cikin kuka tace "Uncle wannan ai ya girmi babana pls karka aura manshi" dariyar k'eta Anty Hadiza tayi tace "wlh aurenki da wannan mutumin babu fashi" ke ko gawarki ce sai an kai mashi,
      Tashi tayi ta shiga d'aki tana kuka, cikin kuka tace "naso na cika maku burinku na ganin na zama likita" amma gashi hakan bai yuwa saboda za'a aurar dani ga mutumin da ya girmi mahaifina, Allah ka kawoman mafita....

       Tanaji tana gani aka d'aura mata aure da tsohon da bata sani ba.. Abun mamaki tana zuwa taga ba tsoho baneba, amma yanda taga tsanarta a cikin idon mijinta ya d'aga mata hankali dan tabbas tasan wata uk'ubar ce zata shiga...

Shin ya zaman Deenah da Abubakar Sadeek Imam zai kasance? Shin zai so ta ko kuma zasu rabu da juna? burinta zai cika naganin ta zama babbar likita?  Ku cigaba da binmu in shaa Allah zakuji amsoshinku....

© M@J@H
F💘J💘R💘

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245