MATATA GIMBIYATA 5-6

🌸💦  MATATA GIMBIYATA!! 🌸💦
    💘 MY WIFE MY PRINCESS 💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         5⃣➖6⃣

        Kiran sallah ne ya tashe ni , a hankali nake bud'e idanuwa na ina mai k'arewa d'akin kallo wanda yanzu kam duhu ne cikin sa a kasalance na kai hannuna kan switch na bedside lamp ina zaune bakin gado ina tuna abubuwa da dama da suka faru yayinda hannaye na suke shawagi cikin messy gashin kai na  bayan nayi alwala nai sallah na rok'i mahalicci ya min jagora a wannan alamari , ban tashi daga sallaya ba wata mata ta shigo d'akin da sallamar ta tace " Amarya ga abinci nan ki ci sannan ki shirya da wuri don yanzu zaku wuce " kai kawai na girgiza domin bani da wata ja akan maganar se yanda aka yi dani. Da murmushin ta tafita yayinda na maida dubana ga abincin! Tunda na taso ban tab'a ganin ranar da aka had'a min breakfast irin wannan ba hasalima sedai in ci ragowar yan gida Tsakanin jiya da yau se naji am like free! Yau gashi na wayi gari na tashi cikin nutsuwa babu tsawar Aunty hantara daga yaya Saeed da kuma khairat ! It feels new to me!......
     Bayan na kammala breakfast sannan na shiga bayi na sakar wa kaina shower ban d'auki dogon lokaci ba na fito just to find out kaya na yana jira na a kan gado had'e da tsadadun turare guda biyu ga kuma wani simple gold jewelry ajiye a gefe ban san wanda ya ajiye su ba don haka na shafe jiki na da mai na zauna ina jiran shigowar wani, and luckily se ga matar d'azu ta dawo .

" Yawwa kin fito ashe?"
Tace, "eh nafito"

    Wad'annan kayayyakin ki ne driver is almost ready ki shirya bari inyi magana da umma kafin nan,  nan ma dai kai na girgiza fuska ta d'auke da murmushi sannan ta fice.

    Doguwar riga ce long sleeve "ja" bodice d'in kuwa black and golden lace ne haka ma boader d'in hannun da kuma borderline na rigar , rigar ba karamin had'uwa tayi ba ni kaina saida nai kauyanci sannan na saka ba wani heavy makeup nayi ba yafa black and gold kashka dupatta nayi sannan na fito zuwa falo bayan yan nasiha da kuma godiya daga mahaifiyar sa wanda ni kaina ban san dalilin yin su ba finally na tsinci kaina cikin wata bak'ar Mercedes Benz muka hau hanyar Maiduguri  abun takaicin ma shine daga ni se driver , an saka ni a owners kamar wata matar shugaban k'asa ! To be frank wannan rayuwar bak'uwa ce a gareni...........

       Bayan tafiyar Awa d'aya da yan mintina suka iso garin Maiduguri direct Airport driver ya direta , to her surprise  wai Abuja za'a kaita thank God i know something about Flight and stuffs ! Abunda ta iya fad'a kenan, cikin minti goma jirgin su ya d'aga zuwa Abuja ................

***************

     A yayinda motar ta tsaya idanuwa na rufe suke ina tuna irin abubuwan da suka faru da ni a baya, tabbas nasha wuya gashi kuma an had'a min aure an katse dukkan mafarki na maganan driver ya dawo dani daga tunanin danake yace "Ranki shi dad'e mun iso "   kafin na bud'e k'ofar har ya bud'e min karo na farko a rayuwa ta naci karo da Mansion wanda ya amsa sunan shi Mansion ! Daganan zuciyata ta fara raya min abubuwa guda biyu! Kodai sun aurar da ni don su kwashi arzik'i ko kuma sun aurar da ni don in zama baiwa! Domin ban ga me mai kud'i wanda ya ajiye wannan masarauta in the name of mansion zai yi da low class gal iri na ba! Gaba na fad'uwa ya fara yayinda na juya naga nisan dake tsakanin gate da main House d'in.
   Gida ne nagani na fad'a tall French windows ne suka fara min sallama ya d'auke ni lokaci kafin na fahimci k'ofar gidan daidai lokacin ne wannan tsohon da ke jikin hoton nan ya fito daga cikin gidan yana washe hak'ora " Barka da zuwa ranki shi dad'e ! Ki k'arasa ciki master yana jiran isowar ki tun d'azu , kiyi hakuri da kalaman sa, ba haka yake ba kafin yanzu, larura ce, kuma magana d'aya master yake yi bai cika son shishigi ba. Ummmm kiyi hak'uri madam amma dole ne inyi miki sharar fage a kansa domin he's hard to be with ina son ki kasance mai hak'uri don Allah! Zaki iya shiga.."

     Like seriously? Wai sharar fage aka yi min akan Master? Wai wane irin game ne wannan? Tsohon da nake tunani shi aka malkala min ba shine miji na ba wani ne daban? Yanzu kam na tabbatar ko daga maganar tsohon nan cewa zaman bauta nazo yi ba na aure ba.......

        Mahmoud i told you for the last time i don't need any body's help! Ni bana son wannan auren! Naji am paralyzed amma kuma i can use my hands banga amfanin kawo min wata mayaudariya a matsayin mata ba! Ko baka gani ba yadda Zeenat ta watsa min 'kasa a ido? To hell with this married! Now get the hell out of my sight! Ka b'ace min da gani nace!!!"  Abubakar SADEEQ IMAM  kenan yayi maganar cikin tsaya yayinda ya yi watsi da tray d'in abincin dake gaban shi yana mai k'ok'arin juya akalar wheelchair d'in shi. Mahmoud PA d'in shi ne , tunda larurar ta samu Sadeeq yake iya k'ok'arin shi don yaga ya samar wa mai gidan shi kuma Aminin shi kulawa ta musamman ,amma with every day  temper d'in Sadeeq karuwa yake a yanzu babu kalmar da ya tsana irin ya mace.....
     Daidai lokacin na shigo falon kenan hasalima tray d'in abincin saida ya kusan fad'o min  a fuska domin da iya k'arfin shi ya wurga, ban san lokacin da na saki ihu ba gami da sunkuya wa jiki na yana rawa, " What the jahannam"  Wannan shine master d'in? Allah sarkin Halitta tabbas ko daga zaunen da yake yi bai bani wahala wajen tantance cewa shi dogo ne ba yanayin fuskar sa square shape ne mai d'auke  da madaidaitan oval shaped eyes, hanci kuwa kamar zai shige baki, gashin kansa bak'i ne ga dukkan alamu mutum ne wanda yake barin suma a ka ga wani side box bak'in k'irin , gashin idonsa kuwa badon namiji bane zance fixing yayi ga kuma cikar gira  daga hannun sa zaka gane cewa maji k'arfi ne kuma ga dukkan alamu baya wasa da nutrition nashi, tabbas Sadeeq yakai namiji ta fannin sura ina ma ace zuciyar shi haka take da kyau? Domin yayin da na had'a ido dashi karo na farko kallon da yayi min ji nayi kamar an jefa ni cikin wuta, a take naji zufa ya karyo min duk da de yaya Saeed mugu ne tabbas wannan ya fishi razanar wa!!

    Cikin husky voice nashi yace " Dubi Tray d'in ba kanta yayi ba amma tana cilla ihu wannan ne kake tunanin zata kula da ni?" Oh! For God sake me kake tunani Mahmoud? Mace will remain mace in as much as am concerned so pls before i vomit ka d'auke min wannan dirty figure  d'in a gaba na !!" Jiki ba kwari Mahmoud ya nuna wa Deenah hanyar d'akin ta......

   Cikin kuka mai tsanani na zube a kan makeken gadon dake d'akin ina zubar da k'walla ga uban yunwa da kishirwa amma sam babu abunda nake tunawa se irin wahalar da zan sha a wannan prison d'in don lallai ba makawa am in a dungeon! Wannan shi ake kira ba'a rabu da bukar ba an haifi Habu!!
       Kiran sallar Azahar ne ya tasheni daga nannauyan baccin da nake wanda bashida maraba da baccin dole  a lokacin ne idona yayi capturing view d'in d'akin  Masha Allah shine kalmar da bakina ya fara furtawa yayinda k'afafu na suka saukaa a kan lallausan posh italian carpet ja dake d'akin , daga glass ne dogin French windows ina iya hango had'adden balcony wanda akayi decorating karamin space d'in shi da Arabian lamps da kuma Arabian darduma lallai kudad'e suna inda suke.!

   Bathroom na shige direct don gabatar da alwala ta amma me? Yayinda naci karo da full length mirrows ga wani chandelier a tsakiya me golden light ,k'ark'ashin sa kuwa jacuzzi ne makeken gaske infact da kyar na iya yin alwala na fito don i prefer the bathroom than the bedroom seriously! Its breathtaking!! And mind blowing!!!.............

© M@J@H
F💘J💘R💘

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245