MATATA GIMBIYATA 19-20

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         1⃣9⃣➖2⃣0⃣

     Shiru har k'arfe Tara na dare Deenah bata fito ba tun Mr Imam yana daurewa har ya kai mak'ura don haka ya d'auki telephone ya k'ira line na cikin gida luckily Sadeeya ta d'auka , cikin hasala yace
" Tell your Madam in akwai abunda yafi b'ata min rai bai fi delay ba, kada ta kuskura ta k'ara ko da minti d'aya kan hour d'aya da ta tsallake"
    Jiki na rawa ta fice bata zame ko ina ba sai d'akin Deenah inda ta iske ta a baje kan gado tana sharara bacci da alama duk na sauk'e gajiya ne. Da kyar Sadeeya ta iya tashin ta sannan ta Isar da sak'o ta fice , nan fa mutumiyar tasan cewa dubun ta ya cika Amma mafitar shine ta je kawai don dai masifar sa a wajen ta ba wani sabon Abu bane.
   
    Na dad'e bakin k'ofa hannuna ya kasa bud'e k'ofar balle nai tunanin shiga, at last nayi ta maza na bud'e ban shiga ba Sai da na lek'a kwatsam mukayi ido hud'u ,hah! Come see yadda na fara muzurai kamar tsohuwar munafuka shi kuwa ya zubamin na mujiya ko kyaftawa babu, ba tare da ya ce komai ba nayi sallama na shige ko ya amsa ma ni ban Sani ba ,direct na nufi bedside drawer na ajiye tray d'in dana d'auko ruwa da glass ,a kai . har na bud'e ruwan zan 6alli maganin naji muryar shi cikin sigar da bai taba min magana da ita ba tunda na zo gidan shi
  Indeed the sweetest ever!

" You never listen do you? , nace miki k'arfe takwas and here you are k'arfe Tara da Kusan rabi zaki bani magani , yanzu in na miki fad'a zaki ga laifina ko?"
A hankali na girgiza kai nace
" Kayi hakuri I slept in "
     Hakuri! Hakuri!! Hakuri!!! Ya daka tsawa sannan ya dawo normal muryar shi yace
" meyasa dukkanin ku hali d'aya gareku? "
    Cikin sauri na d'ago kaina na aza idanuwa na cikin nashi tartare da alamar tambaya baki na rawa nace
" Dukkanin mu? Ni da wa?"
    Da alama bai ma San yayi magana ba don haka ya d'ago yana kallo na kafin yace
" Get lost! "
cikin damuwa nace
"Toh maganin fa?"
  "YOUNG LADY BAKI JI ME NACE BANE? GET LOST !!;"

cikin firgici na fice a guje na bar d'akin na fice ma daga cikin gidan zuwa jikin wani window na zauna , wasu zafafan hawaye suka fara tsere daga idanuwa na.

    Daga kan gadon da yake zaune yana hango ni ta glass na windon shi ,yasan bansan a nan yake ba Amma fuskar shi ya nuna ji yake ya tashi ya bata hakuri and of course give her a warm hug......
    Ina nan bakin window har bacci ya d'aukeni, nice ban farka ba sai k'arfe shida da rabi na safe (6:30am) firgigit na tashi zaune amma abinda na gani yaban mamaki tuni nafara tunanin waya kawoni d'aki nidai iya sanina a waje nake har bacci ya d'aukeni amma gashi na ganni d'aki harda rufeni da blanket da kunna man Ac kodai Sadeeya
ce ta maidoni? Haka na dinga ma kaina tambayoyin da nikaina bansan amsarsu ba...
   Haka na tashi jiki ba kwari na fad'a toilet wanka nayo da yake ina fashin sallah, turare kawai na saka na d'auko doguwar riga ta material na saka. Down stair na nufa ina sauka muka had'u da Sadeeya da sauri ta duka
"Ina kwana Anty?"
"Lafiya lau"
Na bata amsa, tashi tayi zata wuce
"Sadeeya"
"Naam Anty"
"Dama tambayarki zanyi ke kika kaini d'aki jiya bayan nayi bacci?"
"Ah ah Anty bani bace ba"
"To waye ya kaini d'aki?"
"Wallahi ban sani ba Anty"
  Juyawa nayi na nufi kitchen zuciyata cunkushe da tunani kala kala..
    Abinci na tusa gaba ina kallo ina wasa da spoon, Sadeeya ce ta k'araso inda nake zaune tace
"Anty ya kamata kici abincin nan"
Murmushi nayi nace
"Karki damu Sadeeya nama k'oshi kedai had'oman break din yallabai"
Mik'ewa tayi ta nufi kitchen..

   Mik'aman tray d'in tayi karb'a nayi na nufi kofar gabana yana dukan uku uku, sallama nayi har sau uku amma ba amsawa kaina na kutsa ciki, tsawar daya dakaman yasa na kusa yada tray d'in hannuna, ke jakar inace? Da zaki fad'o ma mutum d'aki batare da izini ba? Ko an angaya maki idan kai sallama shigowa kake batare da ance ka shigo ba kodayake ba mamaki k'ila bakije makarantar Islamiyya ba...
   Bak'in ciki yasa nakasa koda d'agowa in kalleshi, cikin tsawa naji yace
"Get out of my room"
Ba musu na juya zan fita
"Ke ugly"
Tsayawa nayi amma ban juyo ba dan in akwai abinda na tsana bai wuce wulakanci ba shiko naga mutumin nan bai aje komi ba sai wulakanci..

   Zokiyi aikin daya kawoki marar kyau da ke, shiga nayi na samu wuri na aje tray d'in tare da goge hawayen da suka gangaro man..
   Gaida shi nayi amma ko kallo na baiyi ba bare nasa ran zai amsa...
   Plate d'in soyayyen dankali da kwai sai tea na d'auka na isa gabanshi, fara bashi nayi ba musu ya bud'e baki na fara bashi sai da ya k'oshi kana na b'allo magani na bashi had'awa yayi da hannuna da maganin ya taune saida na saki k'ara kana ya sakar man hannuna hawaye na share cikin raina nace kaida Allah mugu Azzalumi kuma indai haka zaka cigaba a zaune zaka k'are rayuwarka bazaka mik'eba...
"Idan kin gama zagin nawa sai kiyi sauran aikinki kitashi kiban wuri nagaji da ganin fuskarki tun banyi amai ba.."
"Ido na zare nace wallahi ba zaginka nayi ba"
Ba rantsuwa na tambayeki ba kiyi abinda zakiyi ki b'aceman dagani ugly dai ke.."
    Massage nafara yi mashi inayi yana lumshe ido sai da na gama mashi komi kana na mik'e da zumar barin d'akin..

   Hannuna ya fizgo har sai da na fad'i amma ko kallo ban isheshi ba.
"Miya hanaki zuwa jiya da wuri?"
"Bacci nayi na bashi amsa a takaice dan na fara gajiya da wulakancin shi.."
  Kunnena yaja yace
"Wakika ma rashin kunya jiya?"
Hawaye na farayi nace
"Dan Allah kayi hak'uri"
Tsawa ya dakaman wadda yasa saida na kusa sakin fitsari
"Dake nake ubanwa kikama rashin kunya nace?"
  Kuka na fashe dashi, kallona yayi yace
"Kigama kukan sai kin gayaman ubanda kikema rashin kunya.."

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245