MATATA GIMBIYATA 21-22

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         2⃣1⃣➖2⃣2⃣

   Shiru nayi ina kuka a hankali, ina jin yadda ya damk'e hannu na nasan bazan iya wafce wa ba don haka na fara tuno dabaran da zan yi ya sake ni.
   Da gangan na saki k'ara kamar Wanda naga abun tsoro ba shiri ya sake Mani hannu yana fad'i
"Me ne?"
   Ban ko saurare shiba Sai da na isa bakin k'ofa na juyo fuska ta d'auke da exclusive dariya Wanda of course na manta ranar da nayi irin ta a hankali nace
"Catch me if you can!!"
   Sannan na fice ina murza inda ya damk'e d'in
   Sosai ya dinga dariya shi kad'ai harda rik'e ciki yace
"yau na farko you tried to fight back in your own style"
  ya d'aga gira sannan ya d'auki wayar shi yana danna wa.....

  Yau haka na wuni tun dana gudo ban sake had'e ido da shi ba, kuma hakan yayi min dad'i sosai don at least na samu peace  yau.
  Horn na mota da naji ne yasa na mik'e na nufi window Matace tare da wata budurwa kyakkyawa kam babu yabo ba fallasa. Matar zata kai shekaru Arba'in plus ta sha liffaya kai kace daga Borno take Amma fuskar nan ba annuri ko kad'an da alama ma masifa take yi gata Masha Allah tana da k'iba Amma ba na tashin hankali ba.
    Da sauri Sadeeya ta iso inda nake tace
"Tab'l yau kam na shiga uku! Yau Hajiya ce a gidan nan?"
   Deenah ta juyo da alamar tambaya a fuskar ta tace
"Kamar ya kin shiga uku? Wacece ita?"

   "Uwar Ki ce! Nace Uwar Ki ce! Hummp! Wato tsabar tsegumi tun kafin na k'ariso har an gama k'are min kallo, Munafukan banza"
   Ta juya gefen Sadeeya tace
"Toh Munafuka! Sai Ki kai kayan mu ciki ai."
Jiki na rawa Sadeeya ta fice don d'auko kaya ni kuwa k'asa na durk'ushe ina mai gaida su, ba tare da ta amsa ba ta ja tsaki ta wuce tana fad'in
"Oh ni Halima! Y'an aiki se tsegumi, munafukai Ke kuma Ramlah je Ki duba yayan Ki don nasan bai San da zuwan mu ba"
   Tana magana tana nishi kamar Wanda taci gudu wai hakan stairs take hawa.....
  Tun da muka rabu da su a Falo na dawo d'aki Jiki na rawa a rai na nace
"Tab ba'a rabu da Bukar ba an haifi Habu! Wannan wacce irin K'addara ce? Ni Wollah matar nan ma tafi Mr Imam bani tsoro, don Rashin mutunci ma a y'ar aiki ta d'auke ni, like serious? Do I really look like a maid? Ko dai kawai zagi na take yi?"
   Na dad'e ina sak'e -sak'e ban ankara ba naji an chafko wuya na kamar Wanda nayi wata gagarumar sata idanuwa a waje cike da mamaki na juyo ina kallonta ido cikin ido tana taunar chewing gum kamar y'ar tasha
  "Uban wa ya baki izinin shigo min d'aki, kina y'ar aiki da Ke har kin samu hurumin shiga min d'aki har kisa min kaya?"
Ramlah kenan

   Zaro idanuwa nayi waje kamar an mahaukaciya baki bud'e nace
"kamar naji kin ce kayan Ki? Toh mesa Mr Imam ya barni a Wannan d'akin, koda yake daman shima ba mutunci gareshi ba I don't blame him"
Duk cikin zuciya nake wad'annan maganganun
    Ban ankara ba naji tayi snapping yatsun ta a fuska na tace
"Wake up stupid! Kafin na bud'e ido na Ki cire min kaya kuma Ki bar min d'aki"
    Gudun janyo magana yasa nayi maza maza na kwashi flamingo legs d'ina na fice ban zame ko ina ba se d'akin Sadeeya , sai a lokacin haushin Mr Imam ya kama ni , don haka na mik'e da zummar zuwa d'akin shi..........

   Ko sallama babu ta banke k'ofar d'akin ta shiga , idanuwan ta basa ma gani balle taji shakkar sai huci take..
"Hey! I did not remember you asking for my permission kin wani shigo min d'aki babu ko sallama"
Ya fad'a kansa a kan laptop screen.
  "Sallama? Sallama ai a mutanen da suka san ma'anar ta ake yi wa? Kai da you do not ever want to maintain peace dalilin me yasa zan maka sallama? You have humiliated me to the  extend that naji na tsani kai na yau! First ka bani d'akin da ba nawa ba sannan na saka kayan da ba nawa ba duk ka Sani ka bari Yarinya tazo ta ci Mani mutunci Wollah ban tab'a jin anyi downgrading d'ina haka ba, yau naji cewa dama an barni a inda nake cikin bauta da takura ko ba komai jini na ne su ,Wollah if you had known da baka b'ata lokacin ka har ka bani d'aki ba, nida na kwana a kitchen, na kwana a filin gida ina ne bazan kwana ba,  now I want you to explain this to your sister that I did not wear her clothes Intensionally"
Tana kaiwa nan ta fice gami da banko k'ofa har Saida Mr Imam ya tsorata gami da ajiye laptop d'in ya bi k'ofar da kallo cike da mamakin what she just did.
  
  "How can I tell you My Darling,Cewar kayan sun miki kyau?, bazan iya cewa Ki cire ba coz they seems like they are meant only for you"
Cikin sanyin murya yake magana bai ma San da mutum tsaye a kanshi ba.........

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245