JARABAWA TACE 176~180
JARABAWA TACE yar_ficika NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) 1⃣7⃣6⃣➖1⃣8⃣0⃣ Gudu sukeyi Allah kad'aine ya karesu saboda irin gudun da sukeyi ya shahara bakin gate d'in Alheri clinic suka tsaya, sungumarta Aflan yayi ya nufi ciki yana kwalama Nurse kira dasauri nurses suka taso suka amsheta suka sakata cikin gadon marassa lafiya, emergency aka nufa da ita, biye suke ana zuwa k'ofar emergency aka tsaidasu.. Wani irin kuka Fu'ad ya fashe dashi babu wanda bai ba tausayi ba kowa kuka yakeyi in ka cire Uncle dake ta faman lallashinsu... Zama Fu'ad yayi ya dafe kanshi yana hawaye, dafashi Aflan yayi d'agowa yayi ya sakar mashi wata muguwar ha...