JARABAWA TACE 161~165

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)


                 1⃣6⃣1⃣➖1⃣6⃣5⃣

   Ganin kukan bazai mata magani ba ta tashi ta nufi d'akin Yaya a hankali ta tura k'ofar ji tayi k'ofar ta bud'e shiga tayi zaune suke ita da Aflan babu mai ma wani magana, da sauri ta k'arasa wajen Yaya fad'awa tayi jikinta tana mai rera sabon kuka itamaYayar kuka takeyi sosai..
   "Yaya dan Allah kiyafeman wlh bazan gafartama kaina ba idan kina fushi dani tabbas nasan ko iyayena nada rai iyakar rik'on da zasu yiman kenan dan Allah kiyi hak'uri bazan yafema kaina ba idan har ma auratan dasu ka gina aurensu kan amana da yardar juna sun sami matsala ta dalilina" duk Lady ce ke wannan maganan..
   D'agota Yaya tayi ta share mata hawaye murmushi ta mata tace "ba laifinki bane ba Lady laifi nane dana kasa rik'e amanarki har na d'aga hannu na mareki" da sauri ta d'ago tace "wlh baki kasa rik'e amanata ba hukunci kikaman akan abinda namaki dan Allah kiyafeman"..
   "Duk nike da laifi dan Allah Anty Lady kiyi hak'uri in shaa Allah hakan bazata k'ara faruwa ba" Aflan ne ke magana..
   Dafashi Lady tayi tace "baka da laifi nice mai laifi dan Allah kuyi hak'uri."
  "Ya isa shikenan" Yaya ce tayi magana..

   Tashi Lady tayi tace "ina zuwa" bata tsaya jin mizasu ce ba ta fita..
   D'akin Uncle ta nufa sallama tayi ta tsaya bakin k'ofa, jin muryar da yayi ana sallama ne yasa ya fito dasauri..
   Tana ganinshi ta zube k'asa tace "Uncle dan Allah kayi hak'uri ka daina fushi da Yaya idan  baka daina ba bazan gafarta ma kaina ba"..
   Murmushi yayi yace "karki damu my Lady"
   Dan Allah Uncle kayi hak'uri wlh Yaya ba tada laifi, nafi kowa laifi, shikenan nayafe mata.
   Dariya tayi tace "to muje d'akinta" dole ya bi bayanta...
   Suna isa Yaya ta ganshi tasowa tayi da sauri ta fad'a jikinshi tana kuka, d'agota yayi ya goge mata hawaye yace "ya isa hakanan"..
   Zama yayi, yamasu nasiha mai ratsa jiki daga k'arshe yace "su kyale Lady idan har Fu'ad mijinta ne to zasu daidaita kansu.."

              *BAYAN KWANA BIYU*
  
   Haka gidan ya koma kamar da cikin farin ciki da k'aunar junansu kuma tun daga ranan babu wanda ya k'arama Lady maganan Fu'ad, haka ba k'aramin dad'i yama Lady ba..

   Sanye yake da kayan Max farare kayan sun karb'i jikinshi kamar danshi akayisu k'afarshi takalmin Aldo ne Fu'ad kenan namiji maiji da gayu, cikin takonshi na k'asaita ya k'araso parlourn, "Amminah" abinda yace kenan, d'agowa tayi ta kalleshi tace "samari sai ina?" Dariya yayi yace "gidansu Lady kinsan na kwana biyu ban ganta ba"..
   Hakane mijin Lady sai kadawo kenan? In shaa Allah, peck yama Ammi yace "saina dawo" Allah ya kiyaye hanya d'an Albarka, Amin ya amsa dashi yasa kai ya fita daga parlourn..
   Tuk'i yake a hankaki ga k'ira'ar sudais na tashi daga gefe, bakin gate d'in ya tsaya horn yayi maigadi ya lek'o ganin Fu'ad yasa ya wangale mashi gate yana gaidashi, saida ya samu wuri yayi parking kana ya fito da sauri ya k'arasa wajen maigadi duk'awa yayi har k'asa yace "Baba ina wuni?" Lafiya lau d'an albarka ya yan gidan Lafiya lau suke daidai yana saka hannunshi cikin Aljihu, kud'i ya fito masu yawan gaske ya mik'ama Baba maigadi karb'a yayi yana  godia, bakomi Baba, yana fad'ar haka yayi cikin gidan..

  Da sallama ya isa parlour, zaune take tana karatun jarida ita bata amsa ba haka kuma bata d'ago ta kalleshi ba, wuri ya samu ya zauna yace "Lady bakijin ina sallama?" D'agowa tayi ta kalleshi a wulak'ance ta maida kanta k'asa ta cigaba da karatun ta..
   Shiru ya k'ara biyowa na kusan minti goma, ganin shirun bazai k'are ba yace "idan bazaki damu ba inasan magana dake" kanta k'asa tace "inajinka"..
   Girgiza kai yayi ya rasa gane wane irin haline da ita haka, dama akan maganar da namaki ce shine nakeso na k'ara yimaki, kisani wlh Lady inasanki san da bazan iya misaltashi da komi ba, ki taimakeni ki soni wlh nayi Alk'awarin zan baki farin ciki zan share maki hawaye  da sauran mazan can suka sakaki ki yarda dani pls...

   D'agowa tayi ta kalleshi "Ka k'are?" Abinda tace kenan "eh na k'are" ya bata amsa, toh Fu'ad kasani bazan tab'a sanka ba na tsaneka na tsani duk mai sanka, ta dalilinka Yayata da batasan b'acin raina ta mareni ta dalilinka Aflan dayafi kowa tausayaman ya juyaman baya taya zan soka wlh na tsaneka na tsani komi naka..
   Tashi yayi tsaye yace "bazan tilasta maki akan kisoni ba duk yanda kikayi daidai ne na barki lafiya" yana kaiwa nan ya juya ya tafi..

   Karo sukayi a bakin k'ofa "wash kaina" abinda tace kenan tana dafe kai, d'agowa yayi ya sakar mata murmushi yace "am sowee pls" dariya tayi wanda sai da fararen hak'oranta suka bayyana tace "issokay"
   Tsayuwa ta gyara wanda yabani damar k'are mata kallo sanye take da bak'ar abaya wadda ta fito da k'irarta, hips d'inta sun bayyana ga dukiyar fulaninta, farace sosai gata doguwa d'aure take da veil na abayan wanda sai da gashin kanta ya bayyana...
   "My Name is Inteesar" tana mik'a mashi hannu, mik'a mata hannu yayi yace "Fu'ad" murmushi tayi tace "wow what a nice name" dariya yayi sosai yace "nice meet you" same dear tana kaiwa nan tayi cikin falon shikuma yayi hanyar fita cikin farin ciki...

   Fad'awa tayi parlourn da ihu, kallo Lady ta bita dashi ga wani haushi daya kamata dan gabanta akayin komai, "waike Inteesar yaushe zakiyi hankali kiga yanda kike ihu"..
   Dariya tayi tace "Lady abun ihu nagani shiyasa, pls waye wancan?" Banza tayida ita ta kyaleta, tab'ota tayi tace "dan Allah wancan charming guy d'in waye shi?"..
   "Bansani ba" abinda tace kenan tana kaiwa nan ta mik'e ta bar parlourn daidai Aflan na shigowa tashi tayi da sauri taje ta rungumeshi tace "bruh i miss you so much" kuncinta ya shafa yace "Lil sis miss you more..
  Hannunshi ta rik'e tace "bruh kasanmi?" Ah ah sai kin fad'a..
   Hannunshi taja suka zauna tace "yanzu na had'u da charming guy cikin gidannan" dariya yayi yace "waye shi?" tsaya muga kamar Fu'ad sunanshi, yes Fu'ad sunanshi Allah..
   Dariya yayi yace "Fu'ad he's very nice person" dariya tayi tace "really?" I mean it, wani shu'umin murmushi ta saki "wai inasu Mummy? Sun fita amma nasan gab suke da dawowa, ya kika baro su Mamma?  Fari tayi da ido tace "lapia lau" ina rigima? Tana nan ta k'aru ko? Ihu tayi tace "sai abinda yayi gaba" dungurinta yayi yace "ainasan bazaki daina ihu ba Allah ya shiryaki" dariya tayi tace "bari naje d'aki nayi wanka kafin su iso" tana fad'ar haka taja trolley d'inta tayi gaba...
     Takaici ne ya kama Lady dan duk abinda yafaru tanajinsu abinda yafi d'aga mata hankali yanda take tambayar Fu'ad..
   Wata zuciya tace mata ina ruwanki da tambayar da take mashi keda ba sanshi kike ba miye ruwanki, tab'e baki tayi ta fad'a d'aki..
    Murmushi Aflan yayi ya tashi ya nufi d'aki..
  

   taufa ana wata ga wata tsakanin Lady da Inteesar zanga waye zaiyi winning heart d'in charming Fu'ad..

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245