JARABAWA TACE 116~120

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 

                         (NWA)



                 1⃣1⃣6⃣➖1⃣2⃣0⃣


   Tunda ya shiga gida Ammi tasan ba lafiya, kusa da ita yasamu ya zauna kanshi ya dafe, d'agoshi tayi ta sakar mashi murmushi tace "ba'asan namiji da tsoro ba lallai wannan yarinyar mai tsada ce tunda take saman my one nd only tunani" d'agowa yayi ya kalli Ammi fuskarshi da kaganta kasan yana cikin damuwa yace "Ammi na ganta, amma ganinta baiman dad'i ba Ammi, tak'i saurarena"...... Nan yakwashe komai ya gayama Ammi dayake itace abokiyar shawararshi...

   Zama Ammi ta gyara tace "Auta kayi wauta miyasa zakace zaka kawo mata wata wayan? Konice abinda zan maka kenan" Ammi nafayi hakane saboda nasamu contact d'inta, Allah Ammi inasanta idan ban sameta ba saidai na fasa aure. kallonshi Ammi tayi tace "karkadamu in shaa Allah yarinyar rabonka ce" turo baki yayi yace "Ammi sunanta Nafeesa ko kice Lady" dariya tayi tace "aiman haku'ri zan gyara" da haka ta dinga janshi da fira harya sake yana dariya..

   kallon Ammi yayi yace "bari naje d'aki na kwanta" bai jira mitace ba ya mik'e yayi hanyar d'akinshi..

   Tunda ya shiga d'aki yake juyi bisa gado suffar Lady ke dawo mashi da lokacin data harareshi, komai nata burgeshi yake, duk abinda ya tuna sai yayi dariya, da haka har bacci yayi gaba dashi...

   Tunda suka taho babu wanda yace ma wani komai har suka iso gida, kowa fushi yake da d'an uwanshi. Baiko ida parking ba tafita kallonta yayi ya girgiza kai...

   Deeyerh jeki cema Aflan yazo muci abinci, dan tinda suka dawo bata k'ara ganinshi ba, ba musu Deeyerh ta tashi ta nufi d'akin Aflan da sallam ta shiga d'akin amsawa yayi amma bai d'ago ba, ya Aflan wai kazo kuci abinci, "nak'oshi" ya bata amsa a tak'aice, juyawa tayi taje ta gayama Lady, murmushi tayi dan tasan fushi yake da ita, mik'ewa tayi ta nufi d'akinshi...

   Sallama tayi amma yak'i amsawa, wuri ta samu ta zauna, tace "yanzu Aflan kan mutumin da bamu sani ba kake fushi dani?" Sai a sannan ya d'ago "Anty Lady kenan amma kinsan abinda kika mashi baki kyauta ba, ni banga amfanin k'iyayyar da kikema maza ba kefa mace ce kuma dole ki aure ya kamata ki bud'e idonki ki farka daga wannan nauyayyen mafarkin da kikeyi, dole watarana kiyi aure, kuma ba duka maza suka zama masu hali d'aya, yanzu miye bawan Allah nan yamaki a girme ya girmeki amma kiga yanda kika mashi wlh banji dad'i ba. Kuma shi baice yana sanki ba amma kika wulak'antashi"

   Kallonshi tayi tace "nasan ban kyauta ba amma miye zaice zai kawoman waya?" Murmushi yayi yace "saiki ce mashi yabarta" amma ba.. naji yanzu kayi hak'uri kai dashi shikenan..

   Murmushi yayi yace "ba shikenan ba sa kin bashi hak'uri da kanki" zaro ido tayi tace bazan iya ba, zaki iya, nace bazan iya ba nikuma nasan zaki iya, rigima suka farayi dataga ba yanda zatayi ta amince. Ihu yayi ya mata peck yace "datz my Anty" murmushi tayi tace "muje muci abinci" gani nan zuwa bari nayi waya da my love. dundu ta d'aka mashi ta fita...

   Tana fita yaja waya number Fu'ad yayi dialing, saida ta kusa tsinkewa ya d'auka, Fu'ad kana ina? Daga d'ayan b'an garen yace ina gida, zaka iya zuwa gidanmu yanzu? "Miyafaru ne?" Ya tambaya, kwashe komai yayi ya fad'a mashi yace "Fu'ad inasan kafara shige mata da haka zaka sace zuciyarta. Wani ihu Fu'ad ya saki yace yiman text na Address d'in gani nan zuwa...
   Yana kashe wayan ya mashi sending address, fita yayi falo ya sameta tana ganinshi ta wurga mashi harara, dariya yayi yace "minayi?" malam kazo muci abinci kabarni ina jiranka. Murmushi ya sakar mata daidai ya zauna yace "ki bari zamuyi bak'o yanzu zai zo sai muci abincin tare dashi" hararshi tayi tace "sai na zauna har sai wani yazo?" Marairaicewa yayi yace "Pls Anty Lady Allah yanzu zaizo". Naji abinda tace kenan..

   Wayanshi ne yayi ringing d'auka yayi yace "hello" bansan mi akace ba yace "gani nan fitowa" tashi yayi ya kalleta yana murmushi yafita, binshii tayi da harara..
   Bakin gate suka had'u, yana ganin Aflan ya fito da murna rungume juna sukayi  kamar sun dad'e da sanin juna, kallonshi Fu'ad yayi cikin damuwa yace "Aflan Anty d'inka bazata maka fad'a ba?" Murmushi yayi yace "fad'anmi? dan nayi inviting d'inka? Karka damu bazatace komai ba" nidai ina tsoron karta man masifa Allah banasan fad'a dariya Aflan yayi sosai har yana rik'e ciki saboda dariya, saida ya gama dariya mai isarshi ya kalleshi yace, "Fu'ad sai kazama namiji idan har kanason kasamu soyayyar Lady, sai kayi hak'uri ka jure ka aje tsoro gefe guda kayi hak'uri duk abinda zaka gani daga wurinta ba laifinta bane ba" laifin waye? Kar kadamu zan gayama amma ba yanzu ba, naji abinda yace kenan

   Hannunshi ya kama suka nufi cikin gida, da sallama suka shiga zaune take kan kujera tana latsa waya amsa sallamar tayi tare da d'agowa ganin mutumin d'azu yasa ta razana, kallonshi tayi ta sauke idonta k'asa, dan tasan k'aramin aikin Aflan ne..
   Ina wuni gaisuwar da aka matace ta dawo da ita daga dogon tunanin da takeyi, kallonshi tayi ta amsa ba yabo ba fallasa. Sai a sannan ta k'are mashi kallon lallai dogo ne kuma komai nashi daidai shine sanye yake cikin k'ana nan kaya na max farare, abinda yafi jan hankalinta muryanshi..
   kazauna Aflan ne yace mashi haka, Wuri yasamu ya zauna, komawa Aflan yayi kusa da ita, tana ganin haka tasan miyake nufi, zama ta gyara tace "dan Allah kayi hak'uri da abun da yafaru dazu" tunda tafara magana yake kallonta bai masan ta gama ba,  Aflan yace "Fu'ad kayi shiru?" ajiyar zuciya yayi ya saukar da kanshi k'asa yace "bakomai nima kiyi hak'uri" murmushi tayi tace "karkadamu..

   Mik'ewa tayi tace "bismillah kuzo muci abinci" ba musu ya tashi yabi bayan Aflan, zuba masu tayi ta ajema kowa gabanshi, ci suke suna fira shida Aflan k'ala bata ce masu ba, amma ganinta kusa dashi yana sashi nishad'i..
   Kallonta yayi yace "Anty Lady ina masu gidan?" Dariya ya bata dan saida tayi dariya tace "sunje kd amma gobe in shaa Allah zasu dawo" Allah ya mai dosu lafiya "Amin ta amsa dashi..

   Suna gamacin abinci suka fara fira, duk yanda yaso yaja Lady da fira tak'i amincewa, daga k'arshe saida safe tamasu ta nufi d'akinta ba haka yaso ba amma ba yanda zaiyi..
   Tana tafiya ya mik'e ya kalli Aflan yace "ni zan wuce" dariya Aflan yayi yace "tunda madam d'inka ta tafi d'aki dole ka wuce" duka ya kai mashi ya goce yana dariya. Haka dai suka fito yarakoshi har wurin mota, kallon Aflan yayi yace "ga amanar matata nan pls ka kula da ita" dariya Aflan yayi yace "ban iyawa da masifanta" marairaicewa yayi kamar zaiyi kuka yace "dan Allah", toh naji abinda Aflan yace kenan. Ban kwana sukayi yaja motarshi ya nufi gida cike da nishad'i...

   Yana isa gida bai tsaya kulle mota ba yayi cikin gida yana kwalama Ammi kira, da sauri ta fito a falo suka had'u tace Auta lafiya?" Dariya yayi yace "lafiya lau Amminah zauna kiji" ba musu ta samu wuri ta zauna tace "ina jinka"...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245