JARABAWA TACE 126~130

JARABAWA TACE


yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)

THIS PAGE IS FOR YOU RAMLAH YUSUF AYAGI THANKS FOR D LOVE AND SUPPORT  #1love❤


                   1⃣2⃣6⃣➖1⃣3⃣0⃣

   Kallonshi tayi tace "yau ni kake kira da Nafeesa?" Murmushin takaici yayi yace "ai tunda bakisan ki girmama nagaba dake ba banga amfani baki girman ba kema" girgiza kanta tayi tana hawaye, juyawa yayi zai fita "Aflan" takira sunanshi tsayawa yayi amma bai juyo ba, tashi tayi tazo gab dashi tace "tun muna yara muke tare bamu tab'a samun matsala ba dan haka yanzu ma bazan bari musamu ba zanje naji kiran da Fu'ad yakeman indai hakan zai saka ka farin ciki.."
   Juyowa yayi yana murmushi ya kalleta yace "nagode sosai Anty lady" murmushi tayi tace "zan maka komai in har zai saka farin ciki" hawayenta ya goge mata yace "toh jeki d'an shirya kar yaga kinyi kuka" ba musu ta nufi toilet. Girgiza kai yayi yabar d'akin..
   Tana fitowa daga toilet ta tsaya gaban dressing mirror, tsaye take ta kasa komai, tsaki tayi ta d'auko turare ta fesa ta d'auki gyalenta ta nufi hanyar falo...

   Tunda ya hangota ya kafa mata ido, k'arasowa tayi da sallama saida ya daidaita kanshi kana ya amsa mata wuri ta samu ta zauna nesa dashi. Gaidashi tayi ba yabo ba fallasa amsawa  yayi cikin sakin fuska..
   Shiru sukayi na kusan tsawon minti goma babu wanda yayi magana, kanta k'asa tace "kace kanasan ganina" hakane, "gani to" abinda tace kenan..

   "NAFEESAH" jitayi tsikar jikinta ta tashi yayinda lion voice d'inshi ta daki dodon kunnenta bata amsa ba kuma haka bata d'ago ba bai damu da ta amsa ba amma yaso ta d'ago yaga yanda tayi amma tak'i d'agowa..
   Nafeesah kiyi hak'uri da abinda zakiji daga gareni bayin kaina baneba zuciya tane takasa hak'uri tazo ta tona asirinta..
    Lady tun ranan dana ganki a Sally's cuisine naji wani abu yaratsa jikina wanda ban tab'a jinshi wajen mace ba saike, tunda kuka shigo hankalina ya koma wurinki wanda ke bakisan ina kallon kiba har kuka gama abinda kuke kuka fita haka na biku amma na kasa maki magana sakamakon kwarjinin da ki kaman anan naji zakije airpot d'auko yaronki raina yabani kano zakije washe gari na biki kano kuma nayi sa'a can kikaje, na ganki saidai shakku da tsoro yasa na kasa yimaki magana har kuka taho, haka na dinga yawon nemanki cikin garin katsina har Allah yasa naganki a jifatu saidai ganin dana maki baiman dad'i ba saboda  yanda namaki b'arna amma wani b'an garen naji dad'i domin kinsan dani...
   Nafeesa bazan b'oye maki ba na kamu da sanki tun randa nafara ganinki, san da idan har kikace zaki barni to daidai yake da nabar duniya dan Allah ki taimakeni ki taimaki rayuwata ki soni namaki alk'awarin zan baki farin ciki.
   D'agowa tayi ta kalleshi tana kuka tace "dama nasan ta tsuniyar gizo bata wuce k'ok'i, kai kuma kalar taka yaudaran kenan?"  Ido ya zaro yace "yaudara?" Eh yau dara mana saboda maza dukan halinku d'aya kasani wlh ban sanka bazan tab'a sanka ba na tsaneka kai na tsani duk wani namiji babu gubar da ban had'iyaba ta d'a namiji dan haka banzan iya sanka ba saboda abinda wancan sukaman kaima shi zakaman tana kaiwa nan ta tashi tana kuka..
   Hawaye yakeyi yana kwalamata kira amma bata juyo ba, dafe kanshi yayi dayake faman sara mashi in banda hawaye babu abinda yakeyi..

   Jiyayi an dafashi d'aga kanshi yayi yaga Aflan da sauri ya tashi yace "Aflan ta tsaneni wai bata sona wlh Aflan zan iya mutuwa inasanta, santa yaman illah" sai kuma ya fashe da kuka shi kanshi Aflan saida ya goge hawaye..
   Zaunar dashi yayi yace "Fu'ad take it easy mana kaifa namiji ne wayace ma namiji na kuka?  kuma Bakai ta tsana ba wasu mazan ta tsana idan kashirya zan gaya maka miye dalilinta na tsanar maza" na shirya abinda yace kenan..... Kwashe komai Aflan yayi ya gayama Fu'ad bai b'oyemai komai ba. yace "kaga tana da hujjar tsanar maza saboda tasha wahalarsu"..

   Hakane amma wlh ni bazan yaudareta ba inasanta zan iya komai akanta dan Allah Aflan ka taimakeni kace tasoni Allah za'a iya rasani, dafashi yayi yace "kadaina fad'an haka inaji araina zata soka kabi komai a hankali yanzu tashi muje na kaika gida nasan baka iya driving na dawo bisa mashin" haka ya tashi yabi bayan Aflan yana goge hawaye...

   Tunda suka shiga mota babu wanda yace ma wani k'ala haka suka dinga tafiya har suka kai gidansu  Fu'ad horn Aflan yayi mai gadi ya wangale masu gate, cinna kan motar yayi cikin haraban gidan parking space ya samu yayi parking, fitowa yayi ya bud'ema Fu'ad k'ofa da yakasa komai sai hawaye...
   Fitowa yayi, kallonshi Aflan yayi yace "dan Allah kayi hak'uri Fu'ad kabi komai a hankali in shaa Allah Lady rabonka ce" nagode abinda yace mashi. mukullin motar ya mik'a mashi, "kaje da ita gobe ka maidoman" ba yanda ya iya haka ya juya ya shiga motar ya fita daga gidan..
   Hawayen da suka gangaro mashi ya goge yayi hanyar cikin gida...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245