JARABAWA TACE 131~135

JARABAWA TACE


yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                         (NWA)


                      1⃣3⃣1⃣➖1⃣3⃣5⃣

   A falo suka had'u da Ammi ta fito daga kitchen rik'e da plate da sauri ta aje plate d'in hannunta, tazo ta kamashi ganin halin da yake ciki yasa hankalinta yatashi "Fu'ad miya faru dakai? Wani abu aka maka? Baka da lafiya?" Duk a tare ta jero mashi wannan tambayoyin..
   Hawayen da suka gangaro mashi ya share, wuri ya samu ya zauna ya dafe kanshi zama tayi kusa dashi tace "Fu'ad wai miye? Kaman magana dan Allah ko naji sanyi mana"...
   D'agowa yayi yana hawaye yace "Ammi bata sona tace bata sona ta tsaneni ba zata tab'a sona ba wlh Ammi inasanta santa yaman illa ki taimakeni karki rasani" kuka ya fashe dashi mai tsuma jiki..
   Shiru Ammi tayi tana mai tausayin halin da d'an ta ya shiga tabbas tasan yana san Nafeesah amma bata d'auka san yakai haka ba in shaa Allah zata san ya zatayi  taga ya mallaki Nafeesa saboda batasan ta rasashi...

   D'agoshi tayi ta share mashi hawaye tace "kasan bansan kukanka ko? Kaifa ba yaro baneba akanmi zaka zauna kana kuka haba mana shekara talatin amma kana abin yara banaso ka daina" kallonta kawai yayi baice komai ba..
   Fu'ad inasan kayi hak'uri da yarinyar nan koda itace autar mata kabarta mana baka rasa komai ba in shaa Allah zaka samu wadda ta fita, da sauri ya d'ago yana girgiza kai bazan iya rabuwa da ita ba ita nakeso ita nake k'auna ban tab'a so ba sai akanta kinga ban iya rabuwa da ita, kuma ba laifinta baneba "laifin waye?" Ammi ta tambaya, yace "Ammi Lady tana da hujjar da zata k'i saurare na".... Nan ya kwashe komai ya gayama mata..

   Shiru Ammi tayi na kusan minti goma, kallonshi tayi ta sakar mashi murmushi tace "tabbas Nafeesah ta had'u da *JARABAWA* ta wasu mazan tana da damar da zatak'i kowane namiji gudun karta koma halin da ta shiga sai dai abinda batasani ba shine yarona daban yake da sauran mazan bai tab'a soyayya ba sai akanta sakayya ce Allah ya mata dashi". Kayi hak'uri ka cigaba da adua in shaa Allah Nafeesah rabonka ce inaji a jikina kaji Auta nah...
   D'agowa yayi ya kalleta yace "yaushe ne zata zama rabona? Tafa tsaneni tace bata sona" kacigaba da adua nidai nasan ba macen da zata ga d'ana tace ta tsaneshi itama tsoron halin maza ne yasa ta furta hakan kayi hakuri kacigaba da adua in shaa Allah everything will be fine kaji ko..
   Mik'ewa tsaye yayi ya ce "naji Ammi ki cigaba da man adua amma zuciyata zafi takeman gab take da bugawa Ammi gab kike da rasani" yana kaiwa nan ya wuce d'aki, tagumi Ammi tayi cikin ranta tace "wannan wace irin yarinya ce da Fu'ad keman barazanar zan rasashi" hannu ta d'aga sama tace "Allah idan yarinyar nan alkairi ce ka juyo da hankalinta kan Fu'ad idan ba Alheri kasa mashi dan gana". bisa gado ya fad'a kanshi na sara mashi ga zazzab'i mai zafi da ya rufeshi...

                 ★★★★★★★★
   Aflan na shiga gida bai tarda kowa falo ba, hanyar d'akin Uncle yayi da sallama ya isa d'akin can ya tarda Yaya da Uncle wuri ya samu ya zauna kusa da Yaya, kallonshi Uncle yayi yace "Malam yadai ina Ladyn na ganka kai kad'ai?" Tana d'akinta nima daga gidansu Fu'ad nake na maidashi gida ne. "Baida lafiya ne?" Su duka suka tambayeshi..
   Zama ya gyara ya kwashe komai ya gaya masu. kallon iyayenshi yayi yace "wlh ina tausayama Fu'ad saboda yanama Lady san gaskia amma takasa fahimtar haka, duk namijin da zai maka kuka ba k'aramin so yake maka ba."
   Uncle ne ya kalli Aflan yace "kafi kowa sanin miyafaru da Lady ya kamata ayi mata uzuri".
   Yaya ce tayi magana tace "haba Uncle miyasa kullum baka ganin laifin Lady ne? Itafa ba yarinya baceba kuma dole tayi aure kuma koma miye ya faru da ita ai ya riga da ya wuce sai tayi hak'uri ta d'auki k'addaranta wannan kuma da ya shigo rayuwarta saita karb'eshi hannu biyu batasan alherin dake tare dashi ba.."
   "Hakane" amma kuyi mata uzuri" Uncle ne ya fad'i haka yana kaiwa nan ya mik'e ya nufi hanyar fita, mik'ewa sukayi su duka suka bi bayanshi..

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245