JARABAWA TACE 141~145

JARABAWA TACE


yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)



                   1⃣4⃣1⃣➖1⃣4⃣5⃣

   Zaune ya tarda ta parlour tayi tagumi rab'ata yayi ya wuce sai da yakai bakin k'ofa ya juyo yace "zazzab'i ke damun Fu'ad kuma kisani duk abinda ya sameshi kece sila kuma dake iyayenshi zasuyi kuka" yana kaiwa nan ya juya ya tafiyarshi yana dariya...
   Tashi tayi ta nufi d'akinta fad'awa tayi kan gado tana kuka mai tsuma rai saida tayi mai isarta kana ta share hawayenta..
   Wayarta ta jawo ta kira besty ringing biyu Zainab ta d'auka, hello besty kina ina? Banji mi akace ba shikenan dama ina san ganin kine, kuma gashi baki gari saikin dawo kenan, kashe wayar tayi ta wurgata kan gado ta sake fashewa da sabon kuka..
   Ita dai tasan basan Fu'ad take ba kuma haka bata k'inshi amma rashin lafiyarshi yana d'aga mata hankali...

   Tafe yake cikin motarshi yana sauraron wak'ar Karode bello Godwin a hankali yake bin wak'ar yanabi yana murmushi kamar bakinshi akayi wak'ar...
   Bakin gate d'in gidan ya tsaya horn yayi gate man ne ya lek'o ganin Aflan yasa ya wangale gate d'in yana mashi murmushi, parking space ya samu yayi parking fitowa yayi daidai mai gadi ya k'araso wajenshi gaisawa sukayi cikin girmamawa Aflan yace "Baba suna nan ko?" Eh suna nan ya bashi amsa, kud'i ya zaro daga aljihunshi masu yawan gaske ya mik'ama maigadi, godia yafarayi mashi bai ko amsa ba yayi cikin gidan..

   Sallama ya dingayi amma babu wanda ya amsa mashi dan haka shiga yayi parlour yana sallama amma shiru, waya ya zaro yayi dialing number kafin tafara ringing Ammi ta fito da sauri ta k'araso cikin parlour tace "Aflan kaine?" K'asa yayi da kanshi yace "wlh kuwa Ammi ina wuni ya mai jiki?" Lafiya lau yaji sauk'i banji shigowarka ba inacan ina fama da Fu'ad kasanshi da fitina yak'i cin abinci bare yasha magani, karki damu Ammi yanzu zai sha maganin kuwa, dariya tayi tace "Kashiga yana d'akinshi" ba musu ya nufi d'akin Fu'ad..
    Shiga yayi d'akin da sallama, kwance yake bisa gado k'arasawa yayi bisa gadon tausai yabashi ganin daga jiya zuwa yau ya rame sai fari da yayi girgiza kai yayi tabbas yana tausayin Fu'ad kuma haka kawai yaji yanasan Fu'ad har cikin ranshi..
   Farkawa yayi ganin Aflan kusa dashi ya mik'e zaune yace "Aflan kaine?"..
   Dariya Aflan yayi yace "ah ah kaine"..
   Zumb'ure baki yayi yace "kai dama ai haka kake"..

   Kunnenshi Aflan ya kama yace "ayi hak'uri ban k'arawa" ina Lady nah? Ita miyasa baza tazo ganina ba? Batace tana gaidani ba? Aflan dagaske Lady ta tsaneni? Dagaske wai bata sona? Gaba d'aya ya jero mashi tambayoyin nan..
   Tausayin Fu'ad ya kamashi yace "wayace maka bata sanka?" Ita tafad'aman ko ka manta?..
   Tafad'a cikin b'acin rai ne amma nasan tana sanka, kuma tace "a gaida ka da jiki ka tabbata kana shan magani kana cin abinci"..
     Ammi ce tsaye tana jinsu ba k'aramin tausayi d'anta ke bata ba..
   K'arasowa tayi tace "ah toh gara da Lady tace ya ci abinci ya sha magani dan baiyin ko d'aya amma tun da ita tace yayi zaiyi, yanzu haka yak'i cin abinci bare yasha magani..
   Aflan yace "aiko bari na kirata na gaya mata" daidai yana zaro waya daga aljihunshi...
   Dasauri ya kwace wayar yace "kayi hak'uri so kake tak'ara fushi dani? Wlh zanci kuma zansha magani yanzu, Ammi ki kawoman abincin naci" dariya Ammi tayi tace "Allah dai ya sakama Lady da albarka data canjama yarona hali." Dariya Aflan yayi yace "Amin Amminmu"..

   Dawowa Ammi tayi da plate ta mik'a mashi k'in karb'a yayi tasan mi yake nufi tace "Aflan ka kirata kaga yak'i karba" dasauri yace "nifa bak'in karb'a nayi ba ina nufin kibani" bazan bakaba kai zakaci da kanka..
   Dan dole ya karb'i yaci abincin yanaci yana yatsine fuska amma ba yanda zaiyi saida ya kusa cinyewa kana ya aje kallonsu yayi yace "nak'oshi" murmushi Ammi tayi tace "kayi k'ok'ari saura magani"..
   B'allo mashi maganin tayi ta mik'a mashi karb'a yayi ya saka baki yabi da ruwa, yana gama sha Ammi ta kwashe komai tabar d'akin..

   Sai dare Aflan yabar gidansu Fu'ad ya dawo gida....

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245