JARABAWA TACE 136~140

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                         (NWA)



             1⃣3⃣6⃣➖1⃣4⃣0⃣

    D'akin Lady ya nufa suna biye dashi da sallama ya shiga d'akin kwance take ta kasa amsa sallama sai faman kuka da takeyi "Lady" ya kira sunanta tashi tayi zaune ganinsu tsaye yasa ta mik'e ta fad'a jikin Yaya tana kuka...
   Bubbuga kafad'arta Yaya tayi tace "ya isa haka nan kukan" d'agata tayi ta share mata hawaye...
   Hannunta taja suka zauna, zama Uncle yayi yakira sunanta d'agowa tayi ta kalleshi, miyasaki kuka? Kallon Aflan tayi, kauda kanshi yayi gefe. Sadda kanta tayi tana hawaye, yace "ba kuka na tambayeki ba"...

   Hawayen ta goge tace "Fu'ad ne yace yana sona" nan ta kwashe komai ta gaya masu tana kuka...
    Numfasawa Uncle yayi yace "toh miye laifin Fu'ad? Inaga yau nafara ganin yaron nan amma na yaba dana tsuwarshi  Nafeesa ya kamata kisan abin da kikeyi kinsan dole kiyi aure ba zamu zuba maki ido akan wani ra'ayinki ba tabbas munsan kin had'u da *JARABAWAR* maza amma ki d'auka k'addararki ce haka, shikuma wannan daya shigo rayuwarki ki amshe shi hannu biyu bakisan irin Alherin daya zo maki dashi ba.."
   Tunda yafara magana take kuka, "nidai banaso ku kyaleni ban sanshi na tsaneshi na tsani duk namijin da zaice yana sona dan duk halinsu d'aya ku rabu dani wlh banso" tana kuka take fad'ar haka...
   Girgiza kai Uncle yayi yace "bakiso?"
                "Eh banaso".
   Shikenan ki daina kuka, takaici yasa Yaya takasa cewa komai fita tayi tabar d'akin binta Aflan yayi dan Lady haushi take bashi...

                   *washe gari*

   Zaune take tayi ta gumi tana jiran fitowarshi, har k'arfe sha d'aya bai fito ba d'akinshi ta nufa dan tasan bai kai sha d'aya bai fito ya gaidata ba. Da sallama ta shiga d'akin amma shiru ba'a amsa ba saima duhu data gani d'akin, wutar d'akin ta kunna haske ya gauraye d'akin can ta hangoshi k'udundune bisa gado...
   Dasauri ta k'arasa bisa gadon tace "Fu'ad lafiya mike damunka miya faru dakai" tana yaye blanket d'in  jikinshi...
   Zafin dataji jikinshi ya d'aga mata hankali "Fu'ad mike damunka?" Hawaye suka gangaro mashi ya kasa magana. Ganin ya kasa magana ta fashe da kuka tace "Fu'ad so kake ka kasheman kanka? ashe da gaske kake dan Allah ka fitar da yarinyar nan cikin ranka wlh ban iya ganinka cikin wannan halin"  da kyar ya d'ago yace "Ammi ba laifi baneba ki taimakeni kai na kamar zai fashe"...
   Tashi tayi ta fita da sauri tana kuka. Wayarta ta d'auka ta kira family Doctor d'insu ta gaya mashi tana gama gaya mashi ta koma d'akin Fu'ad kanshi ta d'ora bisa cinyarta tana kuka...

   Doctor ne ya shigo gidan da sallama fitowa tayi ta shiga dashi d'akin Fu'ad dubashi Doctor yayi  tare da d'aura mashi k'arin ruwa 'yan rubuce rubuce yayi. Juyowa Dr yayi ya kalleta yace "Hajiya bawani abu bane ke damunshi illah damuwa itace ta sakar mashi ciwon kai da zazzabi mai zafi amma in shaa Allah daya tashi zaiji sauk'i ga wannan magungunan a siyo idan ya tashi a bashi in shaa Allah zaiji sauki." Amsa tayi tace "nagode doctor" bankwana ya masu ya wuce..
        Tagumi tayi tana kallon Fu'ad dake bacci yana fitar da numfashi a hankali tausayinshi ya kamata. Hawayen da suka gangaro mata ta goge. Wayan Fu'ad ce tafara ruri tana neman agaji, d'auka tayi ta kai wayar a kunnenta sallama tayi, banji mi akace ba tace "Aflan aiko Fu'ad bai lafiya amma yasamu sauk'i bacci yakeyi" banji mi akace ba, tace
             "AMIN"...

                      ★★★★★★
   Dasauri ya fito falo wajensu Uncle, kallonshi Uncle yayi yace "Aflan lafiya?" Girgiza kai yayi yace "Fu'ad ne bai lafiya yanzu nakira mamarshi ta d'auka take gayaman" daidai Lady na fitowa...
   Assha kuwa Allah ya bashi lafiya, Yaya tace "can zakaje yanzu ko?" Eh ya bata amsa, Allah ya bashi lafiya muna mashi sannu..

   D'akinshi ya nufa dan shiryawa, biyoshi tayi Aflan ta kira sunanshi daidai zai shiga d'aki, bai amsa ba ya juyo ya kalle ta, "mike damun Fu'ad?" Kallon raini ya mata yace "ina ruwan kifi da kaska? Ina ruwanki da Fu'ad ai cewa kikayi kin tsaneshi toh da lafiyarshi da rashin lafiyarshi inaga ba damuwarki baneba" yana kaiwa nan ya juya ya shige d'aki yabarta tsaye sake da baki...
   Yana shiga d'aki ya buga tsalle ko banza ya gano Lady nasan Fu'ad, dasauri ya shirya ya fito dan tafiya gidansu Fu'ad....

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245