JARABAWA TACE 156~160

JARABAWA TACE


yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                         (NWA)



                    1⃣5⃣6⃣➖1⃣6⃣0⃣

   Aflan ne ya shigo d'akin Yaya da sallama waje ya samu ya zauna kusa da ita yace "Mummy kiyi hak'uri dan Allah" d'agowa tayi ta kalleshi tace "karka damu Aflan nayi danasanin marin dana ma Lady gashi Daddynku yayi fushi wai dagaske na kasa rik'e amanar da akaban ta Lady?" Girgiza kai Aflan yayi yace "Mummy baki kasa ba kina iya bakin k'ok'arinki komi yafaru nine sila" sai kuma ya fashe da kuka lallashinshi ta dingayi itama tana nata kukan...
   Tunda Uncle ya shiga d'aki ya kulle kanshi ya rasa dalilin dayasa Yaya take matsama Lady yanzu, kota manta amanace wajenta? Dole ya d'auki mataki akan abinda suke mata, dan abinda suke mata shi zai sa ta k'ara tsanar Fu'ad wanda shi kanshi yanasan aurenta da Fu'ad, yana tunani a haka har bacci ya d'aukeshi..
   Yunwa taji zata lahanta ta  dan duk ranan bataci komai ba fitowa tayi taje kitchen ba kowa falon sai k'arar fan haka ta wuce kitchen ta had'a abinci ta koma d'akinta loma guda tayi ta ture abincin in banda kuka ba abinda takeyi...

   Kanta ta sak'a cikin cinyarta tana kuka sosai, kamar daga sama taji an dafata da sauri ta d'ago ganin waye tsaye yasa ta mik'e ta fad'a jikinta tana kuka sosai...
    Hannunta taja suka zauna bata hanata kukanta ba bakuma ta lallashe ta ba dan aganin ta kukan kad'ai zai iya sakawa taji sanyi a zuciyarta, saida tayi mai isarta dan kanta ta daina...

   "Besty" ta kirata dashi amsawa tayi da naam, kiban hankalinki nan magana zamuyi dake..
  Hawayenta ta share tace "inajinki" gyara zama Zainab tayi tace "miye matsalarki yanzu?" Hawayen da suka mak'ale mata ta goge ta kwashe komai tun daga farkon had'uwarta da Fu'ad har kawo yanzu ta bata labari...
   Kallon Zainab tayi tace "besty ki taimakeni zan raba auren da aka gina cikin amana da so da k'aunar juna Uncle yayi fushi da Yaya ta dalilina Besty ya zanyi?" Fad'awa tayi jikinta tana kuka sosai..

   D'agota Zainab tayi ta share mata hawaye tace "miyasa bakisan Fu'ad? baki ganin sakayya ce Allah yayi maki dashi ya kamata ki bud'e idonki kisan abinyi ni aganina Allah ya kawo maki Fu'ad ne saboda yazama Alkairi agareki dan Allah kiso Fu'ad wlh yana sanki a yanda kika ban labari yana sanki yakamata ki farka daga mugun baccinki kisan abinyi"..
   Yakamata ku fahimceni kunfi kowa sanin halin dana shiga amma kuke cewa na koma ma wani namijin anya kuna k'aunata kuwa? Dasauri Zainab ta d'ago ta kalleta tace "yanzu dan munce kiso Fu'ad zaki ce bamu k'aunarki?" Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace "kiyi hak'uri Besty in shaa Allah bazan k'ara saka bakina akan harkarki ba" tana kaiwa nan ta d'auki jikarta ta mik'e tsaye..

   Dasauri ta rik'o hannunta tace "kema tafiya zaki kibarni? Kema baki damu da halin da zan shiga ba?" Sai ta fashe da kuka..
   Tausayinta yakama Zainab zama tayi ta jawota jikinta tana lallashi dakyar ta samu tayi shiru...

   Kiyi shiru hakanan, hawayenta ta share kallonta Zainab tayi tace "Nafeeesa kisani munasanki wlh munfi kowa shiga damuwa akan abinda yafaru dake amma ki d'auka jarabawarki ce haka shi kuma Fu'ad daya shigo rayuwarki ki karb'eshi hannu biyu amman ba tilasta maki nayi ba kiyi tunani zaki gane idan munasanki ko bamu sanki"....
   Ita kuma Yaya ki tabbata da kin bata hak'uri saboda hak'urin da zaki bata shine zaisa su sasanta ita da Uncle, mik'ewa tsaye tayi tace "zan wuce ni sai naji daga gareki" tana kaiwa nan ta ficewarta ko juyowa batayi ba...
   Fad'awa Lady tayi kan gado tana kuka sosai "wannan wace irin rayuwace wane irin jarabawa ne haka? Kowa bai tausayaman? Kowa burinshi naso Fu'ad wai mi Fu'ad d'innan gareshi da za'ace dole saina soshi..
   Fu'ad na tsaneka natsani duk wani naka dalilinka yasa kowa nawa na neman juyaman baya bazan tab'a sanka ba...

   TURK'ASHI

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245