JARABAWA TACE 151~155

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)



                1⃣5⃣1⃣➖1⃣5⃣5⃣

   Horn sukayi maigadi ya bud'e masu gate cinna kan motar yayi cikin harabar gidan, saida yayi parking kana suka fito su duka sukayi cikin gida..
    Zaune take tayi ta gumi  sallama sukayi amsawa tayi tare da d'ago kanta, "sannunku da dawowa" abinda tace masu kenan, Uncle kad'aine ya amsa mata Aflan da Yaya kuwa ko kallonta basuyi ba...
   Da sallama tashiga d'akin kwance yake bai amsa ba haka kuma bai d'ago ya kalle ta ba, zama tayi tace "Aflan magana nakeso muyi dakai",  d'agowa yayi ya kalle ta "inajinki" abinda yace kenan...
   Mina maka? Miyasa ka canja miyasa ka sauya daga Aflan d'in dana sanka? Idan har wani abu na maka yakamata ka fad'aman bawai kadinga man haka ba, kasani kaine komai nawa ban cancanci irin haka daga gareka ba ban cancanci rashin ko in kula da kake man ba..

   Kallonta yayi yace "kingama?" D'aga kanta tayi tace "eh nagama" baki komai ba kawai naga banga amfanin mukoma kamar yanda muke ba saboda baki d'aukar shawarata kina zaton zan cuceki kina ganin kamar zan kaiki ga halaka, dasauri ta d'ago tace "Aflan miyakawo wannan maganan?"..
   Murmushi yayi yace "haka kike tunani mana, saboda idan ba haka kike tunani ba bai kamata na baki shawara akan Fu'ad ba ki kasa d'auka wlh da kinsan irin san da Fu'ad ke maki da baki gujeshi ba, duk wani naki idan yaje wajenshi magananki Fu'ad yakeyi Anty Lady Fu'ad bai cancanci kimashi irin wannan hukuncin ba yana sanki san da zai iya rasa ranshi akanki ni shaida ne"..
    Ya isa ka kyaleni hakanan tana share kwalla dama nasan kafisan farin cikin Fu'ad akaina baku damu da halin da zan shiga ba kaida Yaya, Uncle kad'aine ya damu da halin danake ciki, sai a yanzu nasan nayi rashin iyaye saboda da iyayena na da rai da su sun saurareni tabbas babu abinda yakai maraici d'aci"  saukar marin dataji har  guda biyu shiya hanata k'arasa maganarta, d'agowa tayi  dafe da kuncinta "Yaya?" abinda tace kenan..
    Shi kanshi Aflan saida ya girgiza a yanda yaji marin ..

   Ashe ke butulu ce Nafeesah duk irin rik'on dana maki kirasa da abinda zaki sakaman sai butulci miye ban maki ba? Miye kika nema kika rasa, inaga rik'on da namaki ko iyayenmu keda rai iyakar wanda zasuyi maki kenan..
   Hawaye tashare tace "Yaya saboda wani banza kika mareni? Kin fifitashi akaina, toh kusani bansan Fu'ad na tsaneshi na tsani duk wani wanda ke sanshi" tana kaiwa nan ta bar d'akin da gudu tana kuka...

    Fita Yaya tayi daga d'akin tana kuka, rik'e kanshi Aflan yayi yana kuka duk shi yajawo wannan matsalan dayasan Mummy zata shigo dabai ma Lady maganan ba...

   Afalo suka had'u da Uncle hannunta ya kama yace "Lafiya kike kuka?", wuri tasamu ta zauna tace "ni Lady zata cemawa tayi maraicin iyaye da iyayenta na nan da bata shiga halin datake ciki ba yanzu"..
    "Miyafaru? Kiman bayani ban gane maganarki ba" kwashe komai tayi ta gaya mashi..

   Dasauri ya mik'e kallonta yayi yana nunata da hannu "kika mareta? Akanmi zaki mareta mita maki? Tabbas magananta gaskiya ne tayi maraicin iyaye inda iyayenta nada rai da baza suyi mata abinda kuke mata keda d'anki ba, gabana ta maku sannu da zuwa babu wanda ya kalleta cikinku da wani ya gayaman dana k'aryata duk irin sanda Aflan ke mata amma kuka had'u kuke k'untata mata, kun fifita wani akanta, kinci amanar da aka baki yau kece kika d'aga hannu kika mareta akan wani, inasan da kike mata, kin ban kunya"..
    Wucewa yayi yana huci kamar mayunwacin zaki...
   Dafe kanta tayi tana kuka tabbas tayi danasanin marin da tama tilon k'anwarta gashi sanadiyar marin yasa mijinta yayi fushi da ita..

   Knocking yakeyi amma tak'i bud'ewa Uncle yace "Lady ki bud'e nine" amma tak'i bud'ewa haka ya hak'ura yabar k'ofar d'akin....
    D'akinshi ya wuce, dasauri ta bishi tana kira amma ko juyowa baiyi ba gabanshi tasha tace "kasaurareni" girgiza kanshi yayi yace "bazan saurareki ba har sai randa Lady ta bud'e k'ofarta" yana fad'ar haka ya shige d'akinshi ya maida k'ofa ya rufe. D'akinta ta wuce tana kuka tare da danasanin marin da tama Lady...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245