JARABAWA TACE 171~175

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)



                  1⃣7⃣1⃣➖1⃣7⃣5⃣

                 *BAYAN SATI BIYU*
   Kwance take tana waya in banda shagwab'a ba abinda takeyi, tsoki Lady tayi tace "Intee kinsan k'arfe nawa yanzu zaki dameni da waya?" dariya tayi ta kashe mata ido ta juya ta cigaba da wayarta, cikin shagwab'a tace"nidai dan Allah kazo ina san ganinka wlh nayi missing d'inka" .
   Dariya yayi yace "karki damu My love ina nan zuwa wajenki" dariya tayi wadda sai da ta fito mata da fararen hak'oranta tace
     "Yaushe?"
   Murmushi yayi kamar yana kallonta yace "kedai ki saurareni nace zanzo" shikenan sai kazo, haka suka cigaba da firarsu ta soyayya, iya shak'a Lady ta shak'a dan gani tayi da gangan Inteesar ta mata haka...
   Nikaina na rasa dawa Intee ke waya haka..
  
  Sai k'arfe biyu na dare Intee ta gama waya, bargo taja zata kwanta, yaye blanket d'in Lady tayi juyowa tayi tace "Anty Lady minene?" Harararta tayi tace "basani ba"..
   Nidai dan Allah ki kyaleni wlh barci nakeji, girgiza kai tayi tace "dama dole kice haka amma kin iya takurama wani yanzu abinda kikayi kin kyauta kenan? Kin hanani bacci kin dameni da waya"..
   Hamma tayi tace "wlh bacci nakeji banda lokacin baki amsar nan" blanket taja ta rufe jikin, girgiza kai Lady tayi ta koma ta kwanta..

                *washe gari*
   Kwance take tana latsa waya, Instagram ta shiga tana duba pix d'in mutane, zumbur ta mik'e sakamakon wani pic data gani, idonta ta goge dan ta d'auka mafarki takeyi..
   Tabbas ba mafarki takeyi ba Fu'ad ne da Inteesar zaune yake cikin mota  yasha kaftan ita kuma tana sanye da abaya kallon juna sukeyi suna dariya sunyi matuk'ar kyau sosai, yaushe sukayi wannan pix d'in kodai dama yaudararta yakeyi ba santa yake ba, miyasa Inteesar zata mata haka?..
   Dasauri ta bar d'akin tana kwalama Inteesar kira
   Tsaye ta tarda ta falo, kallonta Intee tayi tace "yadai kikeman wannan kiran?"
   Wayarta ta mik'a mata tace "suwaye wannan?"
   Murmushi tayi tace "suwa kika gani?"...

   Dariyar k'arfin hali Lady tayi tace "kinsan wayeshi? Kinsan yanake dashi? Kinsan matsayinshi a gurina kirasa wanda zakiso sai wanda nakeso? Dama shiyasa kike shige mashi?" "Excuse mi Lady ina cewa kince baki sanshi? Banfara soyayya da Fu'ad ba sai da na tabbatar bai tare da kowa ko kin d'auka banda labarin abinda yafaru tsakaninku duk abinda yafaru nasani dan haka yanzu Fu'ad nawa ne nike da.." marin da ta mata ne yasa ta kasa ida maganar da takeyi..
   Daidai su Fu'ad da Aflan na shigowa dasauri suka k'araso wajen, "karya kikeyi yarinya Fu'ad danni aka halliceshi bai tab'a san wata ba saini kuma bazai so ba" dariyar takaici Intee tayi tace "ni kika mara?" An mareki kiyi abinda zakiyi..

    Kai kuma kabani mamaki kaban kunya ka kasa cinye jarabawar da nake maka tabbas maza duk halinku d'aya gashi tun ba'aje ko ina ba ka nunaman halinku d'aya ka rasa wacce zakaso sai k'anwata kaban mamaki, hawayen da suka mak'ale mata ne ta goge ta nufi d'akinta da gudu..
Lady! Lady!! Lady!!! Kwalamata kira Fu'ad yakeyi amma bata juyo ba ta nufi d'aki...

   K'arar yada abubuwa sukaji suka nufi d'akinta da gudu daidai su Yaya suma sun fito, dasauri suka isa d'akin, ganin tana ta zubda kayan d'akin tana kuka yaba kowa mamaki, dakyar Yaya ta rik'e tace "minene mike damunki?"
   Kuka tafashe dashi ta fad'a jikinta sai da tayi mai isarta kana ta d'ago, nuna Intee ta dingayi da Fu'ad,
           "Mi suka maki?"
            Uncle ne ya tambayeta...

   Fu'ad yace "Lady ki saurareni kij." Tasawar da ta daka mashi yasa ya kasa ida maganarshi..
   Mizaka gayaman? Baka da abinda zaka gayaman mayaudari maci amana, kaban mamaki ashe san da kakeman na k'arya ne tunda ka kasa hak'uri da abinda nake maka, har kafara neman k'anwata jinina, juyawa tayi wajensu Uncle tace "Uncle Yaya kunga abinda nake gaya maku ko? Duk halinsu d'aya"..
   Ba halinsu d'aya ba cewa Aflan" halinsu d'aya mana gashi ya kasa cin jarabawar da namashi, kallon Yaya tayi tace "ke kam kinji dad'inki bakisan wahalar so ba" babu wanda Lady bata ba tausai ba..

    Matsawa Fu'ad yayi kusa da ita yace "dan Allah ki tsaya na maki bayani" bayanin mi zakaman maci amana, na tsaneka na tsani komai naka, tana fad'ar haka tafara tari yanke jiki tayi ta fad'i...
   Gaba d'aya sukayi kanta suna jijjigata, d'agowa Yaya tayi tace "nashiga uku bata numfashi" girgiza kai Fu'ad yayi yace "bazata mutu ba wlh bazata mutu ba sai munyi aure" Uncle ne ya d'auko ruwa ya watsa mata amma shiru babu numfashi "wlh ra mutu nashiga uku shikenan ku taimakeni wlh bansan na rasata" sungumarta Aflan yayi suka fita suna kuka...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245