JARABAWA TACE 176~180

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)



                     1⃣7⃣6⃣➖1⃣8⃣0⃣

   Gudu sukeyi Allah kad'aine ya karesu saboda irin gudun da sukeyi ya shahara bakin gate d'in Alheri clinic suka tsaya, sungumarta Aflan yayi ya nufi ciki yana kwalama Nurse kira dasauri nurses suka taso suka amsheta suka sakata cikin gadon marassa lafiya, emergency aka nufa da ita, biye suke ana zuwa k'ofar emergency aka tsaidasu..
   Wani irin kuka Fu'ad ya fashe dashi babu wanda bai ba tausayi ba kowa kuka yakeyi in ka cire Uncle dake ta faman lallashinsu...
   Zama Fu'ad yayi ya dafe kanshi yana hawaye, dafashi Aflan yayi d'agowa yayi ya sakar mashi wata muguwar harara, murmushin k'arfin hali Aflan yayi yace "kayi hak'uri nasan laifi nane dana san haka abun zai faru wlh da ban bada shawarar haka ba" d'aga mashi hannu Fuad yayi yace "malam ya isheni haka dama nasan baka san Lady shiyasa ka b'ullo da haka gashinan ta bar maka duniyar hankalinka ya kwanta ko?"..
   Ran Aflan yayi mugun b'aci dan a tunaninshi duk wanda zaiso Lady bayanshi ne amma yau wani bare yake fad'a mashi haka...

   Kwallanta Inteesar ta share ta kalli Fu'ad tace "kayi hak'uri a iya san da Aflan kema Lady banyi tunanin zaiyi abinda zai sa ta rasa ranta ba" tsawa ya daka mata wanda saida yan cikinta suka juya yace "malama dan Allah sauraraman hakanan"
   "Wai mike faruwa?" Uncle ne ya tambaya yana  duban Aflan da Inteesar, cikin dasasshiyar murya Yaya tace "nima abinda zan tambayesu kenan mike faruwa ne wai?"...

   Kallonsu Uncle Fu'ad yayi yace "gasu nan suna da hannu cikin mutuwar Lady duk su suka tsara komai gashi nan yanzu ta bar masu duniyar".
   Dafe kanshi Aflan yayi ya rasa abinda ke damunshi in banda kuka ba abinda yakeyi..
   Une yace "Aflan yimana bayanin miyafaru?"
   Ya kasa cewa komai in banda kuka...

   Tsawa yaya ta daka mashi tace "ba magana ake maka ba?" Shiru yayi ya kasa cewa komai, Inteesar ce tace "wlh Mummy Aflan bai da hannu cikin mutuwar Lady dayasan zata mutu wlh da baiyi abinda yayi ba." Kuka yaci k'arfinta ta kasa ida maganarta...
  Uncle ne ya dubesu yace "yakamata kumana bayani yanda zamu gane amma yanzu kam bamu san ina kuka dosa ba"...

  D'agowa Aflan yayi yace "wlh Daddy banyi sanadiyar kashe Lady ba taya zan kashe abinda nafiso sama da rayuwata? taya zan iya kashe abinda na shak'u dashi sama da kowa? Taya zan iya kashe farin cikina? Wlh banda sa hannu cikin mutuwar Lady" sai kuma ya fashe da kuka.
   Jawoshi Uncle yayi yace "nasani Aflan ba Lady ba ko wani baka iya sanadiyar kasheshi da gangan bare kuma Lady"...

   Duk'awa Aflan yayi wajen Fu'ad dafashi yayi yace "kayi hak'uri tabbas da nabi shawararka da baka zargeni ba sai dai abinda baka sani ba shine Allah ya riga da ya k'addaro da sai haka ta faru amma kai kanka shaida ne irin san danake ma Lady bazan iya sanadiyar rabata da numfashinta ba"..
   Tabbas jikin Fu'ad yayi sanyi rungumo Aflan yayi yana kuka su duka kuka suke cikin kuka Fu'ad yace "kayi hak'uri Aflan raina ne ya b'aci amma tun farko da kabi shawarata da haka bai faru ba" nasani amma haka Allah ya k'addaro babu yanda zamuyi..

   "A fusace Yaya ta kallesu tace "wai mike faruwa ya kamata ku fitar damu daga cikin duhu mana kuna yaren da bamu gane inda kuka nufa ba" kallonta Uncle yayi yace "calm down a hankali ya kamata ki bisu bawai da masifa ba ku tuna asibiti muke bawai gida ba"..
   Zama Aflan yayi kusa da Fu'ad yace "Daddy kuyi hak'uri ku zauna za muyi maku bayani" ba musu suka zauna...

   Dama bawani abu bane ba illa... Ganin an bud'e k'ofar Emergency yasa ya kasa ida maganarshi..
   Doctor ne ya fito gaba d'aya suka mik'e suka nufi wajenshi, doctor ya ake ciki mike faruwa? Kowa da kalar tambayar dayake mashi...

   Kallonsu yayi ba yabo ba fallasa yace "kune kuka kawo wata patient?" Yana cire handglop d'in hannunshi, su duka suka amsa da
         "Eh"
   Am sorry to say wadda kuka kawo... Tarin da yakeyi ne ya hanashi k'arasa maganar da yakeyi..
   Fashewa Aflan yayi da kuka yace "shikenan na rasata tabbas nima zaku rasani" gaba d'aya suka juyo suna kallonshi harda Doctor..
   Girgiza kanshi Dr keyi yana tausayama Fu'ad ga tarin da yakeyi ya k'aru..

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245