JARABAWA TACE 121~125

JARABAWA TACE


yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                         (NWA)



                        1⃣2⃣1⃣➖1⃣2⃣5⃣

    Dariya yayi yace "Amminah kalli duk yanda kikayi" murmushi tayi tace "nidai inajinka". Zama ya gyara yace Amminah yau nayi magana da Lady" da sauri Ammi ta kalleshi tace "are crious?" Dariya yayi sosai yace "am serious" bani labari abinda tace mashi..
   Zama ya gyara ya kwashe komai ya gayama Ammi, yana gamawa ta kalleshi tafara dariya turo baki yayi ya mik'e, da sauri ta kamo hannunshi ta zaunar dashi b'ata fuska yayi yace "Ammi miye na dariya?" Dariya ta k'arayi tace "Allah Fu'ad baka gajiya da shirme yanzu ashe ba gaya mata kayi kana santa ba daga kaje gidansu kun gaisa shine kake ihu haka?" Turo baki yayi yace "Ammi ai da haka zamu saba" gaskiya ne abinda tace...
   Fu'ad Ammi ta kirashi, amsawa yayi da naam kaban hankalinka magana zanyi dakai, zama ya gyara ya d'ora hannunshi kan nata yace "inajinki Amminah" abinda nakeso kasani shine kabi komai a hankali kuma kabi abinda Aflan yace maka tabbas wannan hanyar ce zata sa kasamu Nafeesa cikin ruwan sanyi amma saikayi hak'uri ka jure inasan ka aje tsoro gefe guda idan har da gaske santa kakeyi, a yanda Aflan ke baka labari da Alama akwai abinda ya tab'a faruwa da ita to saika daure ka jure kaji yaro nah..
   D'agowa yayi ya kalleta yace "hakane Ammi kidai tayani da adua wlh dana ganta kasa komai nakeyi kwarjini takeman" murmushi tayi ta dafashi tace "shiyasa nace kabi a hankali"...

                    *washe gari*
   Tsaye yake gaban dressing mirror yana cumbing kanshi k'ana nan kayane na company HUGO BOSS jikinshi t-shirt d'in fara ce sai wandon bak'i, tsarki ya tabbata ga mahallicin wannan bawan abinda nace kenan, kayan sunyi matuk'ar karb'an jikinshi zan iya cema ma masu karatu ban ga wanda k'ana nan kaya sukema kyau ba irin Fu'ad..
   Da sallama ta shigo d'akin, amsawa yayi bai juyo ba wuri ta samu tazauna tace "Auta sai ina haka naga kaci gayu?" Dariya yayi yace "zanje gidansu Matata" dariya Ammi tayi sosai tace "matar da kake tsoro zakace zakaje gidansu"...
   Wuri yasamu ya zauna kusa da Ammi damuwa fal a fuskarshi "Ammi" ya kira sunanta amsawa tayi da naam yace "Ammi yau zan fad'ama Nafeesa abinda ke raina zan fad'a mata inasanta nagaji da dakon sonta gara tasan irin sanda nake mata" dasauri Ammi ta d'ago tace "Fu'ad bakayi gaggawa ba kuwa?" Banyi ba Ammi gara tasan irin sanda nake mata wlh Ammi kullum santa k'aruwa yakeyi gara tasan ina santa kona samu sukuni jiya na yanke shawaran yau zan gaya mata inasanta dan bansan rasata, shawaran Aflan gurguwan shawara ce Ammi banga ta yanda Lady zata bari mushak'u ba garatasan inasanta dan rasata daidai yake da rasa rayuwata ne Ammi, kedai ki tayani da adua, ajiyan zuciya tayi cikin ranta tace "shikuma kalar tashi *JARABAWAR* kenan" dafashi tayi tace "adua ina maka saidai na k'ara, kaje Allah ya baka sa'a" Amin ya amsa dashi...

                *Gidansu Lady*
   Waya ya d'auko ya kira Aflan ringing biyu Aflan ya d'auka. "Ina k'ofar gida" abinda yace kenan, banji mi aka ce ba ya kashe wayar...
   Aflan ne ya fito yana k'arasowa suka rungume juna, kallanshi Aflan yayi yace "sai kace wani ango" dariya yayi har fararen hak'oranshi suka fito yace "ango ne mana angon Lady dan yau bazan bar gidanku ba sai Lady tasan irin san da nake mata..
   Kallonshi Aflan yayi "yace kana ganin yadace tasani tun yanzu?" Yadace Aflan karnazo nayi biyu babu bansan na rasata gara na fad'a mata inaji araina Nafeesa Rabona ce, tabbas yasan gaskia Fu'ad ya fad'a, to saika jure dan ba lallai ta Amince dakai ta ruwan sanyi ba. Murmushi yayi yace "zan iya jure komai akanta banda rabuwa da ita" hannunshi ya kama sukayi cikin gida..

     Falo suka tarda su Uncle duk'awa yayi har k'asa ya gaidasu amsa mashi sukayi cikin sakin fuska, Aflan yace "Daddy shine Fu'ad" Allah sarki Fu'ad ya gida da kowa? Lapia lau, Yaya tace "tunda muka shigo gida ko hutawa bamuyi ba Aflan kebamu labarinka" dariya yayi yace "kundawo lafiya?" Lapia lau suka amsa..
   Tashi sukayi sukabar falon, Aflan inasan ganin my Lady ok bari na kirama ita...

   D'akin Lady ya nufa da Sallama ya shiga, bai jira ta amsa ba ya danna kai, d'agowa tayi tace "wai kai baka jira abaka izini saika dinga shigoma mutane d'aki" dariya yayi yace "to masu d'aki yi hak'uri" miye? Tace mashi, bak'o kikayi ya bata amsa a tak'aice..
   Bak'o waye? Idan kinje kingani. Bazan jeba abinda tace kenan, kiyi hak'uri kije Fu'ad ne yakesan ganinki. Mizan mashi ina cewa mun gama magana jiya akanmi zaizo nemana? Nima wlh bansani ba amma idan kinje kinji, kace mashi bazan zoba...
   Ido ya zaro yace "bazakije ba fa kikace? "Kana mamaki ne dannace bazan jeba? Kadaina mamaki dan babu wanda ya isa yasa naje" mik'ewa tsaye yayi kalleta yace "hakane babu wanda ya isa yasa kije Nafeesa" dasauri ta juyo ta kalleshi, dan yauce rana ta farko daya tab'a kiranta da sunanta...

©FEEDOD DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245