JARABAWA TACE 146~150

JARABAWA TACE


yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                         (NWA)


                     1⃣4⃣6⃣➖1⃣5⃣0⃣

     Yana isa gida, parlour ya tardasu Uncle da sallama ya shiga amsa mashi sukayi zama yayi kusa da Uncle, shafa kanshi Uncle yayi yace "my Boy ya jikin Fu'ad?" Dasauk'i sosai Yaya tace "Allah ya k'ara sauk'i" Amin Mummy mungode...
   Tashi yayi yace "bari naje d'aki nayi wanka" sai ka fito suka bashi amsa...
    Corridor suka had'u da Lady rab'ata yayi ya wuce ko inda take bai kalla ba, Aflan ta kira sunanshi juyowa yayi yace "yadai?" Amm...dama... Sai kuma tayi shiru, baki da abun fad'a ryt? Girgiza kai tayi tace "mina maka haka?" Murmushi yayi dan yasan ba abinda zata tambaya ba kenan, "babu komai kinsan rayuwa komi canjawa yakeyi" yana kaiwa nan ya fad'a d'akinshi yana dariya..

   Girgiza kanta tayi ta wuce parlour tana share kwalla, "Lady"
    Juyowa tayi tace "Naam" mi aka maki kike kuka? Murmushi tayi tace "bakomai Uncle" ah ah da komai zonan..
   Kusa dashi taje ta zauna miya faru dake? Allah Uncle bakomai, akwai komai, Yaya tace "tun da tace babu ai bakoman" d'agowa tayi suka had'a ido da Yaya harara ta wurga mata k'asa tayi da kanta tana goge hawayenta, kifad'aman abinda ke damunki Lady, Allah Uncle babu inda akwai zan gaya maka. Murmushi yayi yace "toh shikenan tashi kitafi"...

                   *Washe gari*
   Fitowa yayi cikin shirin k'ana nan kaya kallonshi Yaya tayi tace "haka zamu dakai?" Eh mana Mummy miye a ciki, indai haka zaka kabarshi kawai ka bamu address d'in sai mutafi, Daddy kanafa jinta kuma kayi shiru, ai gaskia ta fad'a maka ya kamata kasan kadawo mahaifarka, dan haka indai zaka rakamu jeka canja shigarka, tafiya yayi yana gunguni...
   Dawowa yayi cikin kaftan sun mashi kyau sosai, rungumeshi Uncle yayi yace "kaga kyan da kayan suka maka kuwa?" Dariya yayi yace "bawani kyau Daddy" hmmm tambayi mamarka gatanan kaji, Mummy wai sun man kyau? Hararashi tayi tace "bansani ba" dariya yayi yace "dayake ba twinse bane ba" murmushi tayi tace "ai bazaka had'a kanka da yara na ba, yakamata ma suzo hutu hakanan dan nayi missn d'insu" tab'e baki Aflan yayi yace "baki tab'a cewa nadawo hutu ba" bakuma zance ba..
    Daddy kasan me? Ah ah Aflan! jiya da mukaje asibiti kai Fu'ad naga wata yar k'aramar yarinya Doctor ce na maka sha'awarta kawai kayi ta biyu da ita, dariya Uncle yayi yace "Aflan dagaske kake? Yaushe zamuje na ganta dama kasan inasan k'ara mata" kafin ya bashi amsa Yaya ta bishi da gudu fita yayi da gudu yana dariya. Zama tayi ta cire gyalenta, zama yayi kusa da ita yace "miye kuma?" D'agowa tayi da hawaye a idonta tace "yanzu dagaske aure zaka k'ara miye ban maka?" jawota yayi ya goge mata hawayenta yace "wasa nake maki kin isheni rayuwa bana buk'atar k'ari, ko wata ta shigo kinsan ban iya adalci dan haka ke kad'aice" shiga tayi jikinshi tana dariya, hancinta ya lakuta yace "ashe kina da kishi haka?" Dariya tayi ta mik'e daidai Lady na shigowa parlourn...

   Lady tace "ina kuma zaku?" ganin Fu'ad zamuje uncle ya bata amsa..
   Bata k'ara cewa komai ba ta wuce d'akinta..
   Nafeesa Yaya ta kirata "Naam" ta amsa, yanzu dan bak'in hali baki cewa kina gaidashi da jiki? Murmushi tayi tace "Yaya ina gaidashi" tab'e baki tayi tace "kedai baki da hali" ita dai Lady bata k'ara cewa komai ba tabar parlourn..
   Yanzu dan Allah mita maki haka? Na lura fa keda Aflan kun sama Lady ido gaskia bazan shirya daku ba, ayi hak'uri mun daina gaskia ce dai ba'aso kuma mun daina fad'a...

   Atare suka fito kallon Yaya Aflan yayi ganin ta d'aure yasa yayi murmushi bud'ema Daddy gaban mota yayi ya bud'ema Yaya, kabarshi banso zaro ido yayi yace "Mummy miyasa?".
     Kabari har ka auro ma Daddynka mata sai ka bud'e mata..
   Dariya yayi yaza gayo kusa da ita d'ora kanshi yayi bisa bayanta yace "Mummy wake k'in abokin zama" tureshi tayi tace "kana jinshi fa?"..
   Dariya Uncle yayi yace "Aflan kaga kana neman jaman aiki zaka had'ani da matata wayace ma zan k'ara aure?"..
    Dariya Aflan yayi yace "Mummy na tuba ke kad'aice gidan Daddy daga ke ba wata"  hararshi tayi tace "kadai bari amarya tazo" kanshi ya d'ora bayanta yace "in shaa Allah babu wata mai zuwa" dariya sukayi gaba d'aya suka shiga mota...

   Tafiya suke suna fira har suka iso gaban gidansu Fu'ad, horn yayi mai gadi ya wangale masu gate cinna kan motarshi yayi ya samu wuri yayi parking fitowa sukayi gaba d'aya Uncle yace "Aflan sai ka mana izinin shiga ko?" Toh Daddy..
   Shiga yayi yana sallama, fitowa tayi daga kitchen tana amsa sallama, ah ah Aflan kaine? Eh Ammi ina wuni, lafiya lau, ya mai jiki? Dasauk'i sosai Aflan, kashiga ah ah dama dasu Daddy muke yace "nashigo na gayamaki" haba Aflan kabarsu waje? kace su shigo mana...

   Da sallama suka shigo, amsa masu Ammi tayi cikin sakin fuska zama sukayi suka gaisa cikin girmamawa da tambayar mai jiki, masu aikine suka cika masu gabansu da kayan shaye shaye da lashe lashe, Ammi tace "Fu'ad ya tadoku ko?" Dariya Yaya tayi tace "ah ah bakomai" ..
    Ina Fu'ad d'in? Uncle ya tambaya, gani nan daidai yana fitowa ganinsu Uncle yasa ya k'araso da sauri..
    Zama yayi kusa da Uncle yace "Daddy Mummy kune? Ina wuninku?" Gaba d'aya suka amsa da lafiya lau ya jiki? Dasauk'i sosai..
    Kallon Aflan yayi yace "yauma tak'i zuwa ganina ko? Daddy minama Lady ta tsaneni?" Tausayinshi ya kama Yaya, jawoshi jikinshi Uncle yayi yace "bakai ta tsana ba kaji Fu'ad wasu mazan ne ta tsana kuma Aflan ya maka bayanin komai" toh Daddy aini ba haka nake ba Allah bazan tab'a b'ata mata rai ba..
   Nasani Fu'ad amma kabi komi a hankali in shaa Allah Lady rabonka ce inaji a raina, kabi komai a hankali kaji ko? Dariya yayi yace "shikenan Daddy" Mummy ke baki ce komai ba? Aflan yace "Mummy fushi take da Lady saboda kai". zumb'ure baki yayi yace "Mummy bafa laifinta baneba" mamaki yakama Yaya lallai ta yarda Fu'ad ba k'aramin so yakema Lady ba..
   Ammi ce tayi magana tace "indai takura mata zakuyi zanje na d'aukota ko  rigimar Fu'ad kad'ai ta isheta gashi ke kuma kina fushi da ita"..
    Dariya Yaya tayi tace "nifa ba fushi nake da ita ba"..

    Nan dai suka dinga fira sai yamma suka wuce gida cikin so da k'aunar junansu, da fatan Allah yasa Lady rabon Fu'ad ce, dan duk wanda ya zauna da Ammi sai yaso had'a zuri'a da ita saboda kyawawan halayenta...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245