JARABAWA TACE 66~70

JARABAWA TACE



yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                        (NWA)

Wannan shafin nakune masoya na, nagode sosai da k'aunarku akaina Allah yabar zumuci. Naji sauk'i kuma in sha Allah zan dinga typing kamar kullum, da wanda suka kirani da wanda sukaman SMS da wanda Allah bai basu ikon kira ba duka nagode...love u more sweetos❤ #1love💕💕





                      6⃣6⃣➖7⃣0⃣

      Yana fad'ar haka ya juya ya nufi hanyar fita, sanyi jiki na yayi nasan ban kyauta ba maganar da na fad'a mashi. Sameer abinda nace kenan tsayawa yayi cak bai matsaba kuma bai juyo ba. Tashi nayi na isa kusa dashi  nace "Sameer kayi hak'uri akan maganan dana gaya maka ni kaina nasan ban kyauta ba" juyowa yayi da murmushi d'auke a fuskarshi yace "karki damu" yana kaiwa nan ya fita...
      Komawa nayi na zauna nikaina nayi danasanin maganan dana fad'a mashi, amma ba yanda zanyi ne, haka su Yaya suka dawo suka iskeni, kallo na Yaya tayi tace "Lady lafiya dai?" Murmushi nayi nace "mikika gani?" Naga ba yanda muka barki ba kodai wani abun ya faru? Mik'ewa nayi tsaye nace "kaina ke d'an ciwo amma nasha magani" Allah ya sawak'e abinda tace kenan, ban amsa ba nayi hanyar d'akina..
      Tun daga ranan ban sake ganin Sameer ba duk nabi na damu saboda gani nakeyi na mashi wulak'anci wanda kuma ba halina baneba...
      Bayan sati biyu ina kwance d'aki na gama waya da Aflan kenan, naji sallamar shi da sauri na d'auki gyale na nayi hanyar falo ina isa muka had'a ido murmushi na sakar mashi,  shikuma d'auke kai yayi kamar bai ganni ba. "Ina wuni" abinda nace kenan.. lafiya ya amsa da ita. Tab'e baki nayi cikin raina nace "kaji dashi"..

      Inasu Anty abinda naji yace kenan, sun fita na bashi amsa. Juyawa yayi zai fita nace "bazaka tsaya kasha ruwa ba?" Kallo na yayi yace "nak'oshi"...
     Juyawa yayi zai fita komi ya tuna ya juyo ya kalleni, waike bakisan kinma mutum laifi ba kibashi hak'uri? Ni maganan dariya tabani cikin raina nace ashe dani ake fushi bansani ba, a zahiri kuma nace "laifin mi nayi da zan bada hak'uri?" Bakima sani ba? Gaskia a iya sanina bansan na maka laifi ba..
     Takowa yayi yazo gab dani, kallo na yayi yace "Lady k'awance fa kawai nace muyi amma kink'i amince man pls kiyi hak'uri" kallon shi nayi saikuma na sadda kaina k'asa nace "Sameer bansan taya zanfara k'awance dakai ba tunda na taso a rayuwana da mutum biyu kawai nake k'awance daga Aflan sai k'awata Zainab" yanzu kuma kin samu na uku cewarshi kenan...

     Duk'awa yayi yace "please Lady accept my request" naji amma kabari sai nayi tunani, babu wani tunanin da zakiyi nidai yanzu nakeso, dan dole na amince mashi, tsalle yayi tare da ihu nidai binshi nayi da kallo ina dariya...
     Falo muka koma muna ta fira kamar dama mun saba, fira muke yana ban labarin school d'insu in banda dariya babu abinda nake, a haka su Uncle suka shigo shida Yaya..
     Sallama suke amma bamuji ba saboda yanda muke fira, takowa Yaya tayi tazo gabana, duka ta d'akaman da sauri na juyo ganin waye. A shagwab'ance nace minayi kuma? Ana ta sallama amma kuna can kuna fira, b'ata fuska Sameer yayi yace "Uncle kaga Anty ta duka Lady ko?" Dariya Uncle yayi yace "lallai Sameer u're lucky kaine ake fira dakai har ana dariya" dariya shima yayi yace "nima dakyar akayi firan dani" dariya suka saka, nikuma na tashi nayi d'aki da gudu ina dariya. Bansan sanda Sameer ya bar gida ba...

    Aflan nakira a waya bayan mun gaisa nace mashi yaro na kasan mi? "Ah ah" yace, kasan wani Sameer wai babanshi mutumin Uncle ne, ah ah bansan shiba miya faru?..
     Dama yana zuwa gida kusan kullum... Nan dai na kwashe komai na gayama Aflan ban rage mashi komai ba har fushin da Sameer yayi sai da na fad'a mashi..
     Murmushi Aflan yayi yace "shikuma ta haka yazo maki? Lallai wannan ya san hannunshi" bangane mi kake nufi ba fa? Aww sowee toh miye a ciki dan yace kuyi k'awance nifa banga wani illarshi ba dan haka kawai ki amince kinga kinsamu aboki tunda bana nan..

    Ya zanyi tunda ya nace na amince mashi, yauwa kokefa Ladyn Uncle, Allah yabada sa'an abota. B'ata fuska nayi kamar yana ganina nace "nifa wannan magangannun bansan mikake nufi dasu ba" murmushi yayi yace "ai dama bazaki sani ba yanzu amma time will tell" tsoki nayi na kashe wayana dan nasan so yake ya b'ataman rai....

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245