JARABAWA TACE 91~95

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                        (NWA)



                       9⃣1⃣➖9⃣5⃣




     Tun da na rufe babun soyayya na maida hankalina ga karatu na har Allah yasa muka gama bansamu wata matsala ba tunda na fara karatu har Allah yasa nagama ban tab'a samun matsalaba..
     Kusan tare muka gama da Aflan koda yazo yaga halin danake ciki bak'aramin tausayaman yayi ba shi keban shawara akan na d'auka *JARABAWA TACE* haka nakuma amince da hakan..

   Ranan da kika dawo kikazo gida koda kika ganni saida hankalinki yatashi ganin yanda na rame, kinyi kinyi na gaya maki damuwata amma na kasa saboda bansan nasa kaki cikin damuwa, kuma bansan na dinga tuna abinda yawuce..
   Duk da nakasa mance abinda yafaru dani dan wani lokacin idan ina ni kad'ai na kan fad'a cikin tunani har kuka nakeyi..
   Su Uncle suna k'ok'arin suga sun kyautataman saboda basu rageni da komai ba duk abinda nakeso shi sukeman, ko ban fad'a ba indai sun san abun zai sani farin ciki toh suna k'ok'arin suman...

     Numfasawa tayi ta d'ago hawayen da sukayi kwance bisa kuncinta ta share, kallon Zainab takeyi da tunda tafara labarin take kuka, murmushi tayi tace "Besty kinji labarina da kuma abinda yafaru dani, bawai inasan na b'oye maki baneba ah ah inasan na manta da komai ne"....
   D'agowa Zainab tayi da idanuwanta suka rine suka zama jajur saboda kuka, hawaye ta share tace "lallai Lady kin gamu da jarabawa tabbas na tausaya maki kuma basu maki halarci ba amma kamar yanda su Uncle suka ce maki kiyi hak'uri Jarabawarki ke haka nima abinda zance maki kenan in shaa Allah zakiyi dariya nan gaba.."
   Murmushi tayi ta goge hawayenta tace "Besty kenan ai banyi zaton akwai ranan ba nikam na hak'ura da soyayya"
   Dafata Zainab tayi tace "karkice haka ba'a cire rai da rahaman ubangiji abinda nakeso dake ki rik'e adua ki fitar da komai a ranki kiyarda dani in shaa Allah watarana zaki dariya.."
  Murmushi Lady tayi tace "inama zanga wannan ranan dana jawota tazo da sauri" ba Zainab ba koni yar_ficika Lady taban tausai saida na mata hawaye...
   Murmushi tayi tace "trust me ranan na zuwa zakice na gaya maki..
  
   Agogon hannunta ta kalla taga aftr 4 da sauri ta mik'e tace "Besty bari na wuce gida sai na sake zagayowa tunda ke kin yanke zumunci baki zuwa gidanmu" murmushi Lady tayi tace "aiman hak'uri ina nan zuwa" haka kike cewa kuma bazuwa kikeyi ba, tana kaiwa nan ta mik'e...
  Har gaban motarta ta rakata nan ma k'ara kwantar ma Lady tayi da hankali daga k'arshe sukayi bankwana taja motarta tabar haraban gidansu Lady...

   A kitchen ta iske Deeyerh na faman wanke wanke rungumeta tayi tace "sowee yar k'anwata nabarki da aiki ke kad'ai kiyi hak'uri kinji" lah Anty ba komai ai bak'uwa gareki, bari na tayaki d'auraya, kibarshi Anty, ah ah Deeyerh kibari na tayaki haka dai suka dinga wanke wanke suna fira har suka gama..
   Anty mizamu dafa yau da daddare ne? Kinga marece nayi saina d'aura yanzu..

  Murmushi Lady tayi taja kumatunta tace "karki damu yau ba gida zamuyi dinner ba zamu fita ne" da sauri ta kalleta d'aga mata gira tayi tace "i mean it" murmsuhi tayi tace "wlh Anty inajinki a raina kamar yar uwata"..
   Jawota tayi ta rungume tace "Deeyerh yanda kikeji a ranki haka nakeji nima kedai ki cigaba da zama damu da amana in shaa Allah zamuyi maki komai na kyautatawa" angama Anty..

    suka cigaba da gyaran gida sunayi suna fira kamar yan uwa, suna gamawa Lady ta kalli Deeyerh tace "kije ki shirya da anyi isha zamu tafi" d'aga kai tayi tace "ur wish is my command Anty Lady" dariya Lady tayi sosai...
   Itama d'akinta ta koma ta fad'a kan gado rub da ciki tayi tana hawaye, da sauri ta goge hawayen komai ta tuna oho....

*toh masu karatu the battle is yet to start tighten ur belts*

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245