JARABAWA TACE 51~55

JARABAWA TACE


yar_ficika




NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                     (NWA)


                       5⃣1⃣➖5⃣5⃣


        Shigowa sukayi suka samu wuri suka zauna, d'agoni Yaya tayi ta share man hawaye. Uncle yace "Nafeesah ki saurareni magana zanyi dake" shiru nayi ina kallonshi, nayi magana da Saleem yace man iyayenshi ne suka had'a shi aure da yarinyar ba yanda zaiyi ya bijirema maganansu, kuma baida k'arfin da zai aure ku duka biyu, dan haka kiyi hak'uri bayaci amanarki bane ba ba yanda zaiyi ne. Kallon shi nayi nace "yace yaci amanata mana miyasa ya shigo rayuwata miyasa zai maidaman farin ciki bak'in ciki" sai na sake fashewa da kuka...
      Uncle yace "Kiyi hak'uri hakan baya na nufin zaki dawwama cikin bak'in ciki ba i know akwai ciwo kuma bai maki adalci ba amma kiyi hak'uri in shaa Allah sai kinyi dariya" yaushe ai banga ranan da zanyi dariya ba, jawoni Yaya tayi jikinta tace "kidaina fad'in haka Lady ki d'auka Jarabawar kice haka kuma kinsan Allah nasan masu hak'uri"..
       Girgiza kai nayi nace "iyakar abinda zakuce kenan? Iyakar abinda zaku iya yiman kenan? Da kunsan yanda zuciyata ke tafasa yanzu da bakuce inyi hak'uri ba, ni kad'ai nasan yana keji Uncle wlh ina sanshi shine ya koyaman yanda zan so shi shine namijin dana fara so taya zan iya rayuwa babushi wlh I can't" fashewa nayi da sabon kuka, su kansu sun tausayaman amma ba yanda zasu iya...

      Haka suka dinga lallashi na amma suka kasa ciwo kaina har suka gaji sukabar d'akin..
       Haka gidan ya koma shiru, kowa ya shiga damuwa dalilin halin da nake ciki. Idan aka kawoman abinci banci, idan aka matsaman saina saka kuka dan dole aka kyaleni...
      Bayan kwana biyu, na rame nayi bak'i duk wanda yaganni sai na bashi tausai. Babu walwala kwata kwata araina na daina fitowa falo kullum ina d'aki kwance.. ina kwance naji sallama amma nakasa d'agowa na kuma kasa amsawa, takowa yayi yazo gabana ya tsaya, "LADY" abinda yace kenan da sauri na d'ago dan nagane mai maganan, tashi nayi na fad'a jikinshi sai kuma na fashe da kuka..

      Hannuna yaja ya zaunar dani shima zama yayi kusa dani, yace "Lady mike faruwa ne? Daddy jiya yaman waya yace idan nasamu hutu inzo gida sai akayi sa'a ranan nake gama exams shine nazo yau" kuka na fashe dashi b'ata fuska yayi yace "banasan wannan kukan please kiman bayani dan babu wanda yaceman komai."
      Aflan Saleem ya cuceni ya yaudareni saida ya koyaman sanshi kana ya gujeni Aflan Allah inasan Saleem i can't do without him,  sai yanzu na gane mikake gayaman lokacin da nafara sanshi ashe dama so akwai d'aci, shidai Aflan bina yayi da ido dan baisan inda maganar ta nufa ba...
     Zama ya gyara yace "naji amma kidaina kuka kiman bayani mike faruwa" nan na kwashe komai na fad'a mashi. Girgiza kai yayi yace "tabbas Saleem ya cuce ki kuma ya yaudareki amma kiyi hak'uri hakan baya na nufin bazaki samu wani ba in shaa Allah zaki samu wanda yafishi wanda zai saki farin ciki."

      Yaushe? Haka kuke cewa dan kunsan baku ke cikin halin danake ciki ba, murmushi yayi yace "hak'uri dai shi zakiyi" yana kaiwa nan ya mik'e. Hannuna yakama yace "muje falo" tashi nayi na bishi...
      Muna isa falo kowa na nan, guri na samu na zauna na gaida su Uncle,, amsawa sukayi cikin sakin fuska kowa yayi mamakin ganina falo, kallo na Uncle yayi yace "lallai wani aiki sai Aflan" dariya akayi gaba d'aya ban dani, ita dai Yaya bata ce komai ba, Hassan ne yace "please Unty Lady ki dinga fitowa wlhi gidan ba dad'i ko Hussain?" D'aga kai Hussain yayi yace "dan Allah kiyi hak'uri ki koma kamar da wlh duk bamu cikin walwala" tausai sukaban nace "in shaa Allah kudai tayani da adua" gaba d'aya sukace dama munayi ai...
      Kiran Deeyerh Aflan yayi yace ta had'o mashi abinci, ba'a d'auki lokaci ba ta kawo abinci, zubawa yayi a plate ya dawo kujerar da nake mik'aman yayi yace naci, nan na b'ata fuska nace na k'oshi, kallo na yayi yace "mikikaci?" Shiru nayi nan muka fara rigima da yaga banda niyar ci, tashi yayi ya kalli su Uncle "yace inaga gobe zan koma makaranta saboda zuwana baida wani amfani."
       Sai a sannan Yaya tayi magana tace "gaskia kam tunda ita tak'i maganar kowa sai a saka mata ido kawai."
      Uncle yace "Lady haka zamuyi dake? Ke bazaki d'auki k'addarar kiba toh nima na kusa fidda hannuna akanki..
     Kuka na fashe dashi nace "dan Allah kuyi hak'uri Allah ba da san raina bane ba." Idan har kinasan muyi hak'uri to kici abinci cewar Uncle kena..

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245