JARABAWA TACE 101~105

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)



                       1⃣0⃣1⃣➖1⃣0⃣5⃣

     K'arfe tara na safe ta fito cikin shirinta na bak'ar abaya tayi rolling da bak'in veil, falo tasamu Deeyerh tana aiki, zaro ido tayi tace "Deeyerh baki shirya ba? Kinsan fa kano zamu kuma flight d'inshi 12:00pm ne" dariya Deeyerh tayi tace "Anty nafayi wanka kawai kaya zan saka idan munci abinci"..
   Dariya tayi ta zauna bisa kujera nan Deeyerh ta kawo mata dankali soyayye da tea murmushi tayi tace "Thanks amma tare zamu ci dan haka jeki had'a tea d'inki, ba musu Deeyerh ta tashi taje ta had'a tea d'inta...
   Nan suka fara break suna fira, kallonta Deeyerh tayi tace "Anty Lady waye zai kaimu?" Murmushi tayi daidai tana aje cup d'in tea tace "nimana" ke! tazaro ido dama zaki iya long journey?  Dariya tayi sosai tace "idan mun tafi zaki gani idan kuma kina tsoro na barki gida" tana kaiwa nan ta mik'e ta d'auko jakarta. Dasauri Deeyerh ta mik'e tace "jirani Anty Lady bari na saka riga."

   Cikin shirinta na abaya ta fito kallonta Lady tayi tace "eyyeh lallai yau zaki rikita yan kano" dariya tayi tace "Anty gaki awaje waceni" murmushi tayi tace muje..
   Haka suka jera suka fita zaka rantse da Allah yan uwan junane, nikam gaskia sungama tafiya da imanina lolzz..
   Parking space suka nufa gaban black lexus suka tsaya kallon Deeyerh Lady tayi tace "dafa motar Uncle zamu d'auko yarona" dariya Deeyerh tayi tace "ai dayake kece Uncle bazai ce komai ba dan kin hau sabuwar motarshi, wai yaushe zasu dawo?" Jibi sukace daidai tana bud'e motar...

   Shiga sukayi taba motar wuta suka d'auki hanyar kano, tafe suke suna fira, nikam dake lak'e saman taya duk sun gama burgeni, wayanta tafara ringing, kallon Deeyerh tayi tace "d'auka kiga waye?" Tana d'aukowa tace "besty" murmushi tayi tace "bani" mik'a mata tayi tace "hello Besty yane?" Banji mi akace ba, haba wlhi muntafi kano d'auko Aflan danasan zakizo dana tsayaki, ok toh shikenan idan nadawo zamuzo dashi ma, tana fad'an haka ta kashe wayan..
   Sha d'aya daidai suka isa kano, hanyar Aminu kano international airport suka d'auka.
   Suna isa airport daidai jirginsu Aflan na landing, a hankali aka fara fitowa. Hangoshi tayi cikin caftan sun mashi kyau sosai, da sauri ta k'arasa wurinshi rungume juna sukayi suna murna..

   Subahanallah kar dai ace matar aure ce abinda naji daga baya kenan, juyawar da zanyi naga saurayin da suka had'u restaurant ne, nikaina saida gabana yafad'i kodai Aljanine? Hmm mudai je zuwa..
   Rungume take a gefen kafad'arshi, k'uri yamasu da ido har sukazo gab dashi, ita dai Lady batasan mike faruwa ba, Deeyerh tace "Uncle Aflan sannu da zuwa" dungurinta yayi yace "ban amsawa tunda bakizo kikaman oyoyo ba" dariya tayi ta sunne kai k'asa..

   Akwatinshi Deeyerh taja suka wuce, kallo ya bisu dashi ya kuma kasa yi masu magana, ita kanta Deeyerh ta ganshi kuma abun yabata mamaki yanda ta ganshi kano amma shiru tayi saboda tasan abinda yafaru jiya.
   Murmushi Aflan yayi saboda tunda ya sauko ya lura da irin kallon dayakema Lady,  rab'ashi sukayi suka wuce, suna isa bakin mota ta mik'a mashi key, juya kanshi yayi gefe yace "bazan iya driving ba malama", dariya tayi ta bud'e suka shiga mota suka d'auki hanyar katsina....
   Motarshi ya nufa jiki ba kwari yana shiga ya had'a kanshi da sitiyari yace "mike damuna? miyasa kullum takeman kwarjini miyasa nakasa yimata magana?" Wata zuciya tace mashi kana ganin matar aure ce fa kuma kaga mijinta. No da k'arfi ya fad'a tare da buga sitiyari wannan ba matar aure bace ba in shaa Allah (RABONA CE) NA HAUWA JABO..
   Fizgar motarshi yayi da gudu yabar airport d'in sai fatan Allah ya saukeshi lafiya...
   Nima yar_ficika da gudu nabi bayanshi dan ganin waye wannan d'an matashin saurayin..

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245