JARABAWA TACE 16~20

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                        (NWA)


              1⃣6⃣➖2⃣0⃣

       Nafara karatu cikin sa'a ban samu wata matsala ba kullum driver ke kaini makaranta yana mai doni, kamar yanda kika sanni bani da tarkacen k'awaye, saike da Allah ya had'amu dake da farko naso nak'i amincewa dake da kikazo man kina sona da k'awance saboda bantaba k'awa ba amma dana ga yanayinki da hankalinki saina amince dake, zan iya cewa kece k'awata ta farko dana farayi tunda na tashi a rayuwa...
      Randa na fad'ama Arif nayi k'awa yayi mamaki har cewa yayi yaso ya ganki, dariya nayi nace "watarana zaku had'u" haka kowa na gidanmu yasan da k'awancen mu..

     Watarana na fito daga lectures ina sauri zan tafi gida saboda Uncle zaiyi tafiya kuma inasan naganshi, sauri nakeyi na isa gaban mota saboda driver yazo d'aukata, jinayi nayi karo da wani abu, waya samsung k'irar edge ce ta fad'i tana fad'uwa ta fashe takardun hannuna duk suka watse, da sauri nakai hannu shima yakai hannu a tare muka kai hannu kan wayan, d'agowa mukayi muka kalli juna wani abu naji ya ratsani saida na lumshe ido, sakar mashi wayan nayi ya d'auka, cikin natsuwa nace "dan Allah kayi hak'uri wlh ba da gangan bane ba" shhhh karki damu abinda ya fad'a kenan yana kaiwa nan ya saka wayan Aljihu ya kwasheman takarduna da suka zube..
     Mik'a hannu nayi na karb'i litattafai na, girgizaman kai yayi yace "bari na rakaki kinji" murmushi nayi nace "nagode"...

      Tafiya mukeyi yana taman fira nidai hankali na duk yatafi gida saboda inasan naga Uncle, muna isa wajen mota ya bud'eman mota na shiga murmushi namashi nace "nagode fa sosai" dariya yayi yace "ni banasan godiyarki" zaro ido nayi nace "miyasa?" Dariya  yayi sosai yace "inasan nasan sunanki sakamakon godian" NAFISA abinda nace kenan, numshe ido yayi yace "nice name" cikin k'aramar murya na nace "THANKS" hannu na mik'a mashi yaban takardu na, girgiza kai yayi yace "baki buk'atan sanin sunana?" Dariya nayi nace "kayi hak'uri miye sunan?" Murmushi yayi yace "ai kyawawa basa laifi sunana Salim" nice name abinda nace kenan, nagode abinda yace kenan driver ne yaja mota muka tafi har muka k'ure yana d'agaman hannu..

       Koda na isa gida ban sami Uncle ba yariga da yatafi amma nakasa jin haushi, trueout ranan murmushi nayi ni yi wanda nikaina bansan inayinshi ba, bansan dalilin yinshi ba..

      Yaya ce ta sameni d'aki bayan isha inafaman latsa waya ina murmushi, dafani tayi tace "Lady yadai?" D'agowa nayi nace "Yaya mikika gani?" zama tayi ta shafa kaina tace "naga yau yar k'anwata cikin nishad'i take zanso nasan abinda ya sakata nishad'i haka" dariya nayi nace "nikaina Yaya bansani ba kawai daiy natashi naganni haka" kallo na tayi cikin kulawa kodai Lady tafara soyayya ne? Da sauri na d'ago nace "wlhi ah ah Yaya" basai kin rantse ba aikin kai lokacin saidai ki kula ki kama mutuncin kanki nasan halin k'anwata bakuma ina zarginki ba amma kikama mutuncinki ki kula kuma da tarbiyanki kinji, dariya nayi na fad'a kanta nace "nifa Yaya ba soyayya nakeyi ba" dariya tayi ta mik'e tace "idan tayi wari munji" tana kaiwa nan ta fita tana dariya...
      Waya na d'auka na kira Aflan, ringing biyu ya d'auka hey Lil sis abinda yace kenan, dariya nayi nace "lallai ma yaron nan ka isa" dariya yayi yace "yadai?" Nasan akwai magana bakin nan naki, murmushi nayi nace "hmmm yaro akwaishi fa" nan na kwashe komai na fad'a mashi ban rage mashi komai ba..

     Dariya Aflan yayi sosai har saida nayi danasanin gaya mashi, saida yagama man dariya dan kanshi yace "Lady karki gayaman kinfara sanshi?" B'ata rai nayi kamar yana ganina nace "kaifa ba kada hankali daga had'uwa sai nafara sanshi" tunaninshi fa kika yini yi yau? Toh kinga dole nace kinfara sanshi, tabbas shima duk inda yake yana can yana tunaninki dan duk wanda yaga model d'in Uncle sai ya rud'e, dariya nayi kamar cikina zai fashe nace 'baka da hankali" zakizo kiceman yakasa bacci saboda ke, murmushi nayi nace "shiyasa nace bakada hankali mutumin da sunanshi kawai nasani bai tambayi gidanmu ba infact ko number na bai tambaya ba" karki damu idan har yana sanki zai nemeki, kedai Lady abinda zan gaya maki shine ki kula da kanki da tarbiyanki karki saki kiyi abinda zai b'ata tarbiyanki, tabbas nasan abinda Aflan ya fad'aman gaskiya ne...
       Numfashi naja nace in shaa Allah zan kare mutuncina ako ina, yauwa Lil sis agayama surukina ya biki ahankali cz ke mai tsada ce, dariya nayi nace "nifa ba soyayya nake ba" dariya yayi yace "zamaki kira kigayaman gaskiya" dariya nayi, fira muka d'anyi yawancin firan duk  akan karatunmu ne daga baya mukayi bankwana saboda dare yayi...

    Wayan na aje na ja bargo ina tunanin saurayin dana had'u dashi, har bacci b'arawo yayi gaba dani...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245