JARABAWA TACE 21~25

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                        (NWA)



            2⃣1⃣➖2⃣5⃣

       Koda na tashi da safe na kasa mance abinda yafaru dani jiya, haka dai na shirya na nufi makaranta da aduar Allah ya had'ani da saurayin jiya, ina shiga lecture hall dake na fara had'uwa tasowa kikayi muka rungume juna, muna cikin gaisawa lecturer ya shigo gaba d'aya muka maida hankalinmu wajenshi...
       Muna fitowa kika kalleni kika ce waini Nafisa lafiya na ganki cikin farin ciki haka? Murmushi nayi nace maki bakomai, girgiza kai kikayi can kikace Nafisa zanyi transfer na koma KD da karatu, cikin sanyin murya na d'ago na kalleki nace miyasa? Murmushi kikayi kikace hakanan kawai amma karki damu in shaa Allah kamar muna tare ne dan kinzama yar uwata, haka na hak'ura badan naso rabuwa dake ba amma ba yanda zanyi...

     Haka muka gama lectures muka fito zamu tafi gida amma hankalina duk bai tare dani, ina tunanin yanda zanyi zaman makaranta ba tare dake ba, kuma ina tunanin yanda zan sake had'uwa da saurayin nan, a haka har kowa ya tafi wajen motarshi inata waige waige amma ban ganshi ba...

     Washe gari na shigo makaranta duk ba dad'i saboda babu ke, haka na k'are lectures zan iya ce maki ranan ban gane komai ba, ina gamawa na fito tafe nake a tsanake kamar daga sama naji ance Mai kyau, da sauri na juyo tabbas shine murmushi na sakar mashi wanda bansan nayi shiba...
        K'arasowa yayi shima yana murmushi yace "haba princess saiki b'oye jiya naita nemanki ban ganki ba, kin saka zuciyata k'unci da kyar nayi bacci jiya" nidai binshi nayi da ido saida yakai k'arshe nayi fari da ido nace "toh ai bakaje inda zaka sameni bane ba shiyasa" hakane fa amma ai baki gayaman inda zan sameki ba, kasan department na computer science? Girgiza kai yayi yace "nifa ba makarantar nake ba nadai shigo ganin wanine"..

      Toh yanzu ya kakeso ayi? Number ki zaki ban, zaro ido nayi marairaicewa yayi kamar zai kuka yace "dan Allah karki ceman bazaki bani ba, Allah tunaninki na azabtar dani" ji nayi yaban tausai nace "shikenan zan baka" tsalle yayi yace "THANKS MY LADY" ido na zaro nace "ina kasan sunan?" Dariya yayi yanda yaga na tsorata yace "Relax hakanan sunan ya zoman amma miyasa naga kin rud'e haka?" Sadda kai na nayi k'asa nace "haka ake kirana gida shiyasa" wow gaskia sunan ya dace dake...
       Juyawa nayi zan tafi yace "My Lady number fa?" Dariya nayi nace "ai naga kamar bakaso" dasauri ya sha gabana yace waya gaya maki? Pls kiban, ba musu na bashi number saving yayi kana yace "thanks so much dear" welcum abinda nace kenan na juya natafi cikin murna....

       Ina shiga gida ban iske kowa ba saboda Yaya taje suna, d'akina na wuce ina shiga na aje jikka na jawo waya na kira Arif yana d'agawa yace "Lady yadai andace ko?" Dariya nayi nace "mi aka dace?" Oho bansani ba malama kiban labari kawai, dariya nayi na kwashe komai na gaya mashi, ihu yafarayi kamar zai fasaman kunne yace "bana gayamaki ba? Ai duk wanda ya had'u da Model d'in Uncle dole ya rud'e"

      Dariya nayi nace "waikai miyasa baka ganewa ne?" Mizan gane? Waya cemaka cewa yayi yana sona dariya yayi yace "ai dayake ke sabon shigane amma ga yanda kikaban labari sanki yakeyi" toh naji malamin soyayya dariya yayi yace "gani fa" kedai abinda zan k'ara gaya maki shine ki kula da mutuncinki kinji Lil sis, dariya nayi nace "wai yaushe ka koma malami?" Shima dariya yayi yace "bansani ba" haka dai mukayi bankwana na aje wayana...
       Wajen 11:00pm naji wayana na ringing dubawa nayi naga new number k'in d'auka nayi saida ta kusa tsinkewa na d'auka, cikin siririyan muryana nayi sallama Alhamdulillah akace kana ya amsa sallaman, yace "haba Lady baki d'aukan number da baki sani bane ba?" lumshe ido nayi kamar yana ganina nace "sorry na fara bacci ne" ya salam Allah yasa banyi laifi ba? Bakayi ba abinda nace kenan, ajiyan zuciya yayi yace "toh bari na kyaleki amma dan Allah kiman taimako gobe nazo gidanku saboda akwai muhimmiyar maganan da zamuyi dake" numfashi na ja nace "toh zanyi magana dasu Uncle komi kenan zan gayama gobe" dan Allah ki masu magana da wuri saboda inasan ganinki gobe, karkadamu abinda nace kenan bankwana mukayi na kashe wayan, ina kashewa naja bargo na rufe kaina ina murmushi.....

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245