JARABAWA TACE 41~45

JARABAWA TACE


yar_ficika




NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                      (NWA)


                   4⃣1⃣➖4⃣5⃣

        Tana shiga kitchen ta tarda Deeyerh ta gama komi, rungume Deeyerh tayi tace "yar k'anwata sannu da aiki na barki ke kad'ai" dariya Deeyerh tayi tace "bakomai Anty nah ai kina da bak'uwa shiyasa, dama yanzu nake shirin kai maku abincinku." Gyad'a kai tayi ta d'auki tray d'in, da sauri Deeyerh ta karb'a dariya tayi tace "Deeyerh bakisan ina aiki ko" dariya Deeyerh tayi tace "Anty nah ban san ki wahala ne" tana kaiwa nan ta nufi d'akin Lady. Da sallama ta shiga d'akin tana aje tray d'in ta gaida Zainab, amsawa tayi cikin sakin fuska tace "mun barki ke kad'ai ko Deeyerh?" Dariya Deeyerh tayi tace "bakomai Anty.."
      Juyawa tayi ta fita, bin bayanta Lady tayi da ido, tace "wlh besty inasan Deeyerh jinake kamar ciki d'aya muka fito da ita" murmushi Zainab tayi tace "itama da Alama tanajin dad'in zama daku" munfita jin dad'in zama da ita saboda yarinya ce mai hankali ga ladabi duk yanda zan gayamaki halinta bazaki gamsu ba saikin zauna da ita, shiyasa nasa Uncle ya sakata makaranta yanzu kinga ss1 take Islamiya kuma ta kusa saukewa...
       "Wai ina kuka santa ne?" Cewar Zainab, Hmmm kedai bari Besty wata k'awar Yaya ta kawo muna ita, gaskia kunyi dace, wlhi abinda ke ban tausai da ita gata marainiya shiyasa nake k'ara janta jikina, Allah sarki Allah ya jik'an iyayenta "AMIN", Besty na cika ki da surutu ci abinci please..

        Murmushi Zainab tayi tafara cin abinci, tana ci suna fira saida ta gama tsaf kana ta dawo da ganinta kan Lady tace "yanmata na gama ke nake sauraro" murmushi Nafeesa tayi tace "baki bari ki huta?" Allah ah ah nidai ki cigaba. Numfasawa tayi ta cigaba...
       Haka muka cigaba da soyayya cikin aminci kowa yana gudun b'atama d'an uwanshi rai zan iya ce maki a lokacin bansan wani abu ba waishi matsalar so, saboda duk tattalin Saleem ya mai dashi kaina, idan Uncle yaso tsokana na sai yace "shi bai gane ba yaga Saleem na neman kwace mai fada" saidai nayi dariya kawai dan gani nakeyi a lokacin nafi kowace mace sa'a a duniya...
       A haka har muka shekara d'aya tare, kinga ina aji biyu kenan babu abinda ya canja kullum ma gani nakeyi yana k'ara sona, dangina babu wanda baisan da zaman Saleem ba. Dole na saka Aflan ya dawo 9ja dan yaga Saleem...

     Watarana ina zaune wayan Saleem ya shigo, a yangance na d'auka "Hello Prince Charming" da yake sunan dana ke kiranshi dashi kenan, amsawa yayi da naam "My Lady" kinsan me? Kai na girgiza kamar yana ganina nace "ah ah" ki gayama Uncle inasan iyayena suzo gidanku, gara a san dani. Cikin jin kunya na amsa mashi da "to" daga nan muka cigaba da firan soyayya...
      Da daddare na sami Uncle falo na gaya mashi sak'on Saleem, Uncle yace "bakomai duk sanda suka saka lokaci saiki fad'aman" amsawa nayi da to na tashi na koma cikin d'aki da murna...
      Tun daga randa Saleem ya kirani bai kuma kira na ba sai da akayi sati guda, abun yaban mamaki amma ban gayama kowa ba. Daya kira na mashi magana sai ceman yayi aiki ne yamashi yawa yanzu ma kira yayi yaji ya nake, ba wata fira mukayi ba ya kashe wayanshi...

      Tun kiran da Saleem yaman bai k'ara kira na ba tun kowa bai sani ba har kowa ya gane halin da nake ciki, hankalin kowa na gidan ya tashi ganin yanda na rame na daina walwala, kullum cikin yiman nasiha ake...
       Ranan ina zaune sai ga kiran wayan Saleem ya shigo, ina d'agawa nace "Prince charming idan na maka laifi ka yafeman" dariya yayi yace "bakiman komai ba abubuwa ne sukaman yawa amma yanzu komai ya zama normal"  bansan sanda na fara dariya ba. Fira muka dingayi kowa yana gayama d'an uwanshi yanda yayi missing d'inshi. Daga k'arshe mukayi ban kwana akan zaizo da weekend..
     bayan kwana buyi da yin wayarmu, ina kwance naji ina sha'awan chrtn data na kunna, Dandalin Autar Hajia direct na nufa da yake ina karanta books d'inta kuma ta iya books inajin dad'in books nata...
      Ina shiga banyi magana ba na fara neman books can wata naga ta shigo tanayin sallama aka fara amarya amarya, dariya ta turo tace "yanzu zakuga pre wedding pix, tana turowa naji ina sha'awan ganin pix d'in, bud'e pix d'in nayi, ido na zaro saboda abinda nagani ya razanani bansan sanda nafara goge ido na ba, tabbas abinda nagani gaskia ne.....

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245