JARABAWA TACE 81~85

JARABAWA TACE


yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                           (NWA)



                       8⃣1⃣➖8⃣5⃣



      Dasauri na mik'e tsaye tafiya nafarayi sai kuma na tsaya, takowa yayi yazo kusa dani, "Lady" abinda ya fad'a kenan kasa d'agowa nayi saima hawayen da na cigaba dayi. Hankicif ya zaro daga cikin aljihunshi ya shareman hawaye, k'amshin da hankicif d'in keyi yasa na k'ara lumshe ido.
     Kallon shi nayi nace "Sameer miyasa zaka tafi kabarni? Miyasa zakayi haka hukuncin da ka yanke yaman tsauri" murmushi yayi yace "ba da san raina nabarki ba komi yafaru duk ke kika jawo kinsan ban iya nisa dake.."
       Uncle ne yace "toh kuzo ku zauna ni zan maki bayani" ba musu muka isa wajensu muka zauna...

     Bayan mun zauna Uncle yace "duk abinda yafaru agaban idon mu"............nan ya kwashe komai ya fad'aman ya k'ara da cewa "kuma mu mukace yayi hak'uri ya daina zuwa wajenki, shirun da mukayi munasan da kanki kigane kinasan Sameer shiyasa muka saka maki ido bawai dan bamu damu da damuwarki ba ah ah kawai munasan kiyarda da kanki kinasan Sameer, sai gashi kuma kingane hakan..." Lokacin da kika shigo mana da kuka lokacin nama Sameer text akan yazo gida yanzu..
       Kallona Uncle yayi yace "dan haka kuka ya k'are ga Sameer nan ba inda yaje," dariya nayi na sunne kaina k'asa saboda ni kaina naji kunyar abinda nayi..
      Tashi sukayi kallo na Yaya tayi tace "Yaya wlhi inasan Sameer" dariya akayi daga baya sukabar falon..

     Kallonshi nayi nace "Sameer ashe zaka iya zama baka ganni ba har natsawon sati biyu?" Girgiza kai yayi yace "kinsan bazan iya ba dole tasaka nayi haka amma wlh kullum sai nazo gaban gidannan.." tausai yaban nace "kayi hak'uri laifinane komi yafaru" ba laifinki bane ba yaudaranki akayi dole ko waye ya guji haka...
      Nan muka zauna kowa na gayama d'an uwanshi yanda yake sanshi a haka har aka kira magrib bamu sani ba sai da Uncle ya fito ya koremu kana muka rabu ba dan munso ba...

     Tun daga sannan soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanina da Sameer, duk inda zani yana biye dani ko fad'a mukai bai yarda mukwana duk abinda nace toh shi za'ayi, saidai abin da na lura maman Sameer kwata kwata bata sona amma wannan ban d'auke shi komai ba tunda shi yanasona..
     Kullum da salon soyayyar da Sameer yake man har na manta na tab'ayin soyayya da wani, a haka har nakai aji uku a makaranta, kuma in dai yana gari to shi zai kaini wani lokacin ma bai tafiya saina gama lectures, ni kaina ina mamakin irin san da yakeman...

     Ranan wata juma'a tun da na taso daga makaranta nake jin gabana na fad'uwa haka na k'araso gida da yake ranan ba Sameer ne yaje d'auka na ba, ina isa k'ofar falo gaba na ya fad'i sakamakon maganan da naji su Uncle nayi..
     Yanzu taya zamu fad'ama Lady zaiyi aure taya zata d'auki maganan? Nikaina bansani ba duk Uncle da Yaya ke wannan maganan...

     Dasauri na k'arasa falon nace "basai kunce man komai ba shima aure zaiyi kamar yanda Saleem yayi yabarni? Nikuma tawa k'addaran kenan shikenan duk wanda naso sai ya yaudareni yabarni?" Gaba d'aya suka juyo suna kallona dan basu san naji komai ba...
     Lady Sameer bai yaudare kiba saboda... Nasani basai ka k'arasa ba Uncle mahaifiyar Saleem bata sona nasan bata sona amma ban d'auka zata rabani da d'anta ba nikam mina aikata haka ake hukuntani, ya Allah idan laifi namaka ka yafeman...
     Tashi Yaya tayi ta kamoni tace "kiyi hak'uri ki d'auki k'addarar ki" ya zanyi Yaya dole na d'auka..

     Lady Uncle ne ya kirani juyawa nayi na kalleshi yace "ba laifin Sameer bane ba yajema mahaifiyarshi da maganarki tace bai isa ya aure kiba tana ganin tun kafin ki aureshi kin mallakeshi bare idan kin aureshi dan haka tabashi d'iyar yayarta, kuma baban baida abinyi cz duk abinda maman tace haka za'ayi. A yanzu maganan da nake maki Sameer yabar k'asar saboda abinda mamanshi tamashi..."

      Girgiza kai nayi ina hawaye nace "naso naga Sameer kafin yatafi naso nayi bankwana dashi naso na fad'a mashi shine namijin da bazan iya daina sanshi ba har k'arshen rayuwata amma hakan bai samu ba" sai na fashe da kuka...
      Jawoni Yaya tayi jikinta ta rungume tace "kiyi hak'uri ki cigaba da adua Allah zai kawo maki wani.."
     Kidaina fad'aman haka babu ranan da zanso wani nagama soyayya kubarni haka ina kaiwa nan na tashi na nufi d'aki da gudu ina kuka...

```NIKAINA YAR_FICIKA SAIDA NA ZUBDA MA LADY HAWAYE DAN TANA GANIN JARABAWA```

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245