JARABAWA TACE 96~100

JARABAWA TACE


yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                        (NWA)



She isn't my mother, She isn't my sister, she's one of d family, who's more like a friend. she has fun with me, laughts with me, listens to me, encourages me, she spends time with me, believes me. Share with me, cheers for me. She understands me like a mother, she's there for me like a sister. And perhaps best of all she loves me like a daughter... She's ANTY MAIJIDDAH

*This page is for you Anty Maijidda Musa*


               9⃣6⃣➖1⃣0⃣0⃣


   Cikin shirinta na Abaya tafito Abayan brown and purple sai tayi rolling da purple scarfs, d'akin Deeyerh ta wuce Deeyerh na ganinta ta saki baki, hararanta tayi cikin tsokana tace "miye kika saki baki kina kallo na?" Dariya Deeyerh tayi tace "Anty Lady kinga kyanki kuwa? Wlh kamar wata tauraruwa" harara ta sakar mata tace "karki ida shiryawa ki tsaya surutu" dariya Deeyerh tayi tace "ai nama gama muje"..
   Haka suka jera suka fito gwanin sha'awa nikaina *yar_ficika* sun burgeni. Parking space suka nufa, kallon Deeyerh tayi tace "mufita da motar Aflan?" Dariya Deeyerh tayi tace "kinfasan baisan ana tab'amashi mota muje da taki" nikuma key d'in motarshi na d'auko, murmushi Deeyerh tayi tace "shikenan muje" haka suka shiga mota tayi horn maigadi ya bud'e masu, cinna kan motanta tayi suka fita sai da ta daidaita kan motarta bisa titi..

   Kallon Deeyerh tayi tace "yanmata ina zamu muje Sallys ko Royal joint?"  Duk inda mukaje Anty, b'ata fuska Lady tayi tace banfa san haka" yi hak'uri Anty muje Sallys. Murmushi tayi tace "kokefa"..
   Juya kan motanta tayi suka nufi mani house suna tafiya suna fira cike da k'aunar juna..
   Suna isa tayi parking daidai bayan wata black marsandi, fitowa sukayi suka shiga ciki suna shiga suka samu wuri suka zauna..

   Tun da suka zauna ya kafa mata ido yake kallonta ita kuma batasan yanayi ba, waiter ne yazo ya tambayesu abinda sukeso, kallon Deeyerh tayi tace "mi zaki ci?" Duk abinda zakici shi zanci, toh nima duk abinda zakici shi zanci nan suka fara rigima, tagumi yayi yana kallon su yana dariya shikam sun burgeshi. Murmushi Waiter yayi yace "hajia kece babba keya kamata ki zab'a" murmushi tayi tace "idan bata zab'a ba saidai mukoma gida"..
   Sanin halinta da tayi yasa Deeyerh tace akawo masu white rice da stew sai salat, hak kuwa akayi shikam sun gama burgeshi dan tun sanda suka shigo yake kallonsu har suka fara rigima. *kowaye shikuma? wannan*..
   Sunaci suna fira har suka gama, suna gamawa ta kira waiter ta bashi kud'inshi ta mik'e kallon Deeyerh tayi tace "muje ko?" Allah Anty Lady na kasa tashi kibari muhuta, "Wow Lady! what a nice name" abinda naji d'an saurayin nan ya fad'a kenan
   Allah zan barki nan tana fad'an haka ta juya, da sauri Deeyerh ta tashi ta bita, shima mik'ewa yayi ya bi bayansu..

   Ta bud'e mota kenan wayanta ya fara ringing d'aukowa tayi daga cikin jikarta sunan data ganine yasata murmushi, d'agawa tayi tace "yaro nah yadai?" Banji mi akace ba. Haba yaushe? Olryt zanzo d'aukarka in shaa Allah, bankwana sukayi ta kashe wayan..
   Kallon Deeyerh tayi tace "rigimamme zaidawo gobe zamuje d'aukarshi" dariya Deeyerh tayi tace Allah ya kaimu" amsawa tayi da Amin suka shiga mota..

    Fizgar motarta tayi da gudu sukabar wurin. Dafe kanshi yayi yace " oh God mike damuna ne? Ya akayi na kasa mata magana? Ina zan sake ganinta kuma?" Duk shikad'ai yakema kanshi tambayoyi, haka yaja jiki ba kwari ya shiga motarshi yabar wurin da sauri...
   Kallonta Deeyerh tayi tace "Anty Lady kinsan wani abu?" Girgiza kanta tayi alamar ah ah. Wani guy keta kallonki tunda muka shiga yake kallonki nikuma ina kalloshi amma baisan ina kallonshi ba, da muka fito ya fito bayan motarshi mukayi parking kafin...tsawa ta daka mata wanda nikaina saida biro na ta fad'i tace "ya isa haka" shiru tayi tace "kiyi hak'uri". Daga nan babu wanda ya sake magana har suka isa gida..

   Suna isa gida Lady ta fito ko kulle motar batayi ba ta nufi cikin gida, Deeyerh ce ta kulle motar ta nufi cikin gida...
   D'aki ta tardata kwance tayi rubda ciki, sallama tayi ta shiga duk'awa tayi tace "Anty Lady kiyi hak'uri bansan ranki zai b'aci ba" d'agowa tayi ta kalleta da idanuwanta da suka rine tace "bakomai Deeyerh nah nima kiyi hak'uri da tsawar da namaki"..
   Murmushi Deeyerh tayi tace "karki damu Anty" rungumeta Lady tayi tace "datz my Deeyerh" sakinta tayi suna dariya sun d'anyi fira daga k'arshe sukayi bankwana kowa ya kwanta...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245