JARABAWA TACE 106~110

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                        (NWA)


                     1⃣0⃣6⃣➖1⃣🔟

   Takwas da rabi yatsaya gaban wani black gate, waige waige nakamayi dan nagano ma masu karatu wace unguwa ce, ba shakka Goruba road ne, horn d'in daya keyi shi ya mai doni cikin hankalina, da sauri get man ya taso ya wangale mashi gate, kan motarshi ya cinna cikin haraban gida, parking space ya samu ya faka motarshi bai tsaya kulle ta ba ya fito ya nufi cikin gida...
   Cikin falo ya kutsa kanshi bako sallama, tsayawa nayi na saki baki ganin yanda cikin falon ya had'u, nabarma masu karatu su auna da kansu..
   "Auta Lafiyarka ka shigo cikin gida ba sallama? Wannan ba d'abi'arka bace ba" wata dattijuwar matace wacce bazata wuce shekara sittin da biyar ba ba tayi magana..

   Wuri ya samu ya zauna kusa da ita yace Ammi kiyi hak'uri" murmushi tayi tace "to naji amma ina kashige haka da sai yanzu zaka dawo gida? Duk yau ban ganka ba, mike damunka na ganka haka?", a tare ta jero mashi wannan tambayoyin.
  Tab'e baki yayi yace "Ammi kano naje" kano? Ta zaro ido, eh kano naje. Mikajeyi kano Auta batare da sanina ba baka tab'aman haka ba sai yau..
   Ammi....nan ya kwashe komai ya gaya mata yace "kuma Ammi itafa nabi kano dan naji tana cewa zataje airport d'auko yaronta shine mind d'ina yabani kano ta nufa shine na bita, amma Ammi wanda naga taje d'auko shi kamar mijinta amma kuma bataman kama da matar aure ba.."
   D'ora kanshi yayi yace Ammi ki taimakeni wlhi ina santa ina k'aunarta tun randa na fara had'a ido da ita na kamu da santa pls Ammi a matsayinki na mahaifiyata ki taimakeni ki aura man ita itace farin cikina..

   Shafa kanshi tayi cikin tausayawa, tabbas tasan dagaske yake yana santa saboda tunda take bata tab'ajin yace yana san wata ba gashi kuwa shekarar shi talatin.
   Fu'ad ta kira sunanshi jiki sanyaye ya amsa da "naam" tashi muyi magana, ba musu ya tashi zaune ya kalleta. Yanzu Fu'ad in banda wauta miya kaika kano? to inda ba can taje ba, ya zakayi kadaina irin wannan wautar kaji ko? D'aga kanshi yayi alamar to..
   Ya sunan yarinyar wane gida take su waye iyayenta? Ammi wlh ban sani ba a Sallys muka had'u da ita, all i know ina santa pls Ammi ki taimaki d'anki. Dariya yabata saboda shi kanshi bai san komai nata ba amma yake cewa a bashi ita...

   Fu'ad yanzu ya kakeso ayi kai kanka bakasan komai nata ba taya zan fara nemanta dama kasan gidansu ne da abun yazo da sauk'i, kawai shawaran da zan baka kayi hak'uri ka rabu da ita, ido ya zaro yace "Ammi ashe zaki rasani wlh bazan iya rayuwa babu ita ba, inaji a raina RABONA CE dan Allah ki taimakaman.."
   Tsoro yafara bata dan taga dagaske yake, jawoshi tayi ta kwantar da kanshi a cinyarta tace "Auta yanzu bamu da abunyi, abinda zan iya cema keep praying idan har rabon kace zaku sake had'uwa sai dai abinda nakeso kasani idan har kasake had'uwa da ita ka gaya mata kana santa karka zama raggon namiji mana kuma mata basa auren raggon namiji, pls karka zama raggo a kanta you have to be strong kaji ko? "Naji Ammi" abinda yace kenan, kuma idan har baka gaya mata ba ka bari ta k'ara kufce maka toh kayi asara kenan saboda wani zai rigaka.."
   Ido ya zaro yace "Allah bansan na rasata in shaa Allah na sake had'uwa da ita zan gaya mata" yauwa you have to be a man, ta daina tsorataman Auta na. I trust my Auta nasan ba macen da bazai iya yima magana ba, Dariya yayi yace "zan baki mamaki my Ammi" Gud boy ko kaifa, bari nazo nafara shirin bikin Auta, dariya yayi ya tashi yabar falon...

                *******************
   Tara daidai suka shiga gida, falo suka baje kowa ya gaji, kallon Deeyerh Aflan yayi yace "Deeyerh d'auko plate muci abinci" ba musu Deeyerh ta mik'e ta nufi kitchen, plate ta d'auko da cups ta zuba masu abincin da lemu da sukayi takeway akan hanya, sunaci suna fira har suka k'are kwashe plates d'in tayi ta maidasu kitchen...
   Kallon Lady yayi yace "Anty Lady yanzu waye Uncle d'ina?" Shiru tayi kamar bata jishi ba, tashi yayi ya fizge wayar datake dannawa yace "magana fa nake" ban sani ba aikasan ban tare da kowa yanzu..
   Kinsan me? Saika fad'a Airport naga wani yana ta kallonki da alama sanki yake bakiga yanda yake kallonki ba, tsoki tayi ta fizge wayarta tace "kaji dashi aika dawo kenan" tana kaiwa nan ta mik'e ta nufi d'akinta...

   K'arasowa falon Deeyerh tayi tace "ashe ka lura kaima?" Au kingani murmushi tayi tace "ranan da mukaje Sallys yin dinner ranan yafara ganinta, idan kaga yanda yake kallonta zakayi mamaki amma ita bata sani ba har muka gama muka fito dana mata magana tsawa ta dakaman abinda Anty Lady bata tab'ayiman ba.."
   U mean a garinnan kuka fara ganinshi? Toh miya jeyi kano? Kodai Aljanine, murmushi tayi tace "baiyi kama da Aljani ba wata k'ila akwai abinda ya kaishi shima.."
   Allah Deeyerh guy d'in ya kwanta man kawai naji inasan Anty Lady dashi, amma yanzu kam is to late tunda ba lallai su sake had'uwa ba ke jekima sun had'u ba kulashi zatayi ba..
   Is not late Yaya Aflan, idan har mijinta ne zasu sake had'uwa saidai kafin ta amince akwai wahala, kawai mutayata da adua Allah ya mata zab'i mafi alkairi. Amin ya amsa daidai yana mik'ewa yace "na wuce d'aki" itama mik'ewa tayi ta nufi d'akinta...

IG: yar_ficika

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245