JARABAWA TACE 26~30

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                      (NWA)




                   2⃣6⃣➖3⃣0⃣


     Ban farka ba sai (10:00am) da yake ranan ina fashin sallah kuma ranan week end ce, ina tashi na shiga wanka ina fitowa nayi simple makeup wadrobe na nufa doguwan riga na saka ina gamawa na nufi hanyar parlour, a daining table na iske su Yaya da murmushi na k'arasa wajen, ina zama na gaidasu amsawa sukayi cikin sakin fuska, abinci na zuzzuba ma kowa kana na zuba nawa, nidai tunda na zuba na kasaci sai juya spoon nake, kallo na Uncle yayi cikin kulawa yace "Lady yadai? Naga bakicin abincin ko wani abu ke damunki?" Kafin na bashi amsa Yaya tace "tambayarta dai k'ila kai ta gayama maka saboda kwanakinnan na rasa gane kanta" kallona yayi yace "haka ne?" Murmushi nayi na sadda kaina k'asa...
        Aje spoon d'in hannunshi yayi yace "Lady miye damuwarki? Gayaman abinda kikeso ni kuma zan maki shi idan baifi k'arfi na ba" kai na sadda nace "dama dama" saikuma na fara kyarma, murmushi yayi yace "dama mi? Gayaman mana kina da wanda zaki gayama damuwarki bayan ni?" girgiza kai nayi nace "dama wani ne muka had'u dashi shine yace yanasan yazo yaganni, nikuma nace  saina gayama maka" dariya yayi yace "shine kika kasa fad'i?" Miye sunanshi? Saleem, toh ki gaya mashi na amince yazo "nagode" abinda nace kenan, twinse d'in Yaya suka fara dariya suna Anty Lady ashe ya Aflan yayi suruki bari mukira mugaya mashi, dariya Yaya tayi tace "ai yama rigaku sani" Uncle yace "kardai ku matsa mata" abinda nakeso dake shine ki shirya mashi abinci mai dadi kinji ko Lady" d'aga kai nayi alamar "to"...

     Yau bazan je ko inaba sai naga surukina cewar Uncle kenan, tashi nayi na nufi d'akina da gudu ina dariya...

      Koda na shiga d'aki miskal d'in Saleem biyar na tarda saida abun yaban mamaki, kafin na kira kal ya k'ara shigowa d'auka nayi ina sallama, yayi ajiyan zuciya yace "hankalina harya kwanta" dariya nayi na gaidashi, amsawa yayi yace "Lady kin tambayi yan Uncle din?" Ah ah ban tambayeshiba, miyasa? Hakanan! marairaicewa yayi yace "please Lady Allah ban iya komai idan ban ganki ba yau dan Allah ki taimaka na ganki" dariya nayi nace "shikenan saikazo ina nan ina jiranka" ihu yayi wanda saida na tsorata yace "ina nan zuwa wajen (8:00pm) ki turaman address" yana kaiwa nan ya kashe wayanshi, girgiza kai nayi na tura mashi adress...
        Ina tura mashi SMS naja bargo na koma bacci, ban tashi ba sai la'asar...

      Ina tashi kitchen na nufa tuwon shinkafa na d'aura sai miyan agushi da busasshen kifi, ferfesun kayan ciki nayi, coconut drink ina gama had'a drink d'in na saka a fridge dan yayi sanyi kafin kice mi gida ya d'auki k'amshi, nikaina ina mamakin yanda na dage nayi aikin ni kad'ain, Twinse d'in Yaya suka shigo suna shigowa suka fara tsokana na nidai bance masu komai ba sukayi suka fita suna dariya.
       Cikin mintuna k'alilan nagama aikina ina gamawa na aje na gida a dainning na  Saleem kuma na barsu a kitchen, ina fitowa na ci karo da Yaya tana kallo na ta fara dariya b'ata fuska nayi, jawoni tayi jikinta tace "sannu da aiki Lady lallai wannan surukin Uncle d'in anaji dashi" fizge jikina nayi na nufi d'aki ina dariya..
       Ina shiga d'aki na fad'a toilet, ina fitowa na tsinci kaina dayin kwalliya, kwalliya nafarayi wanda ta kusan d'aukan 30mnts inayinta, ina gamawa na jawo abaya black na saka, feshe jikina nayi da turaren rasasi, ina gamawa nayi rolling da black scarves, kallon kaina nayi a mirror nikaina ko ba'a fad'a ba nasan nayi kyau..

       Takwas daidai wayana tayi ringing ina d'auka yace man gani gaban gidanku, saida gabana ya fad'i saboda yau ce rana ta farko da namiji yazo gidanmu wajena da sunan zance, jiki sanyaye nace mashi toh bari na saka a shigo dakai, kashe wayan nayi na kira Hasan yana d'auka na ce mashi kaje waje Saleem na nan ka shigo dashi ka kaishi guess room, kasa deeyerh mai aiki ta kai mashi abinci, amsawa yayi da to amaryan Uncle Saleem, yana fad'a yana dariya...

      Ina kashe wayan nakira Aflan, yana d'auka yace "Lady ya ake ciki ne?" Dariya nayi nace "normal" guess wat? Saleem yazo gida ko? Dariya nayi nace "waye ya gaya maka?" Sai an gayamani wannan zakwad'i naki, dariya nayi nace "sharri ko?" Shima dariya yayi yace "to kidai bari yafara fad'in yana sanki pls karki rawar kai har ya gano kin mutu kanshi" tsoki nayi nace "kaidai kasani ni kaga tafiyana" kashe wayan nayi na tashi na nufi hanyar fita....

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245