JARABAWA TACE 31~35

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                      (NWA)

This page is for you Meerah Saad❤

               3⃣1⃣➖3⃣5⃣

       Ina fita muka had'u dasu Uncle, Yaya na ganina tafara dariya baya nayi da gudu zan koma d'aki cafko ni tayi tana dariya, sunne kai na nayi k'asa ina murmushi. D'agoni tayi tace "lallai wannan saurayin anaji dashi har gayu aka d'auka haka?" Kumbure fuska nayi na kalli Uncle dake ta faman dariya nace "Uncle kanajin Yaya ko?" Dariya yayi yace "Yaya adaina" nidaina,  "amma surukin nawa mai hankali dashi" cewar Uncle kenan dariya nayi na fizge jikina na ruga...
     D'akin Deeyerh mai aiki na wuce nace mata! ta kwashi kayan abinci ta kaiman guess room ina da bak'o, ba musu ta tashi ta nufi hanyar fita....

      Saida Deeyerh ta dawo kana na tafi, ina isa bakin k'ofan gabana ya dinga fad'uwa haka na daure na shiga da sallama, zaune yake yana latsa waya d'agowa yayi ya amsa man sallama cikin muryanshi dake firgitani, tsaye nayi kamar an daskarani tasowa yayi yana murmushi yace "Lady yadai?" Murmushi nayi na sadda kai k'asa nace "bakomai.."
      Rab'ashi nayi na shige ciki, shima shigowa yayi ya samu wuri ya zauna kaina na k'asa na gaidashi amsawa yayi. Munkai minti biyar babu wanda ya sake magana, kallo na yayi yace "Lady" amsawa nayi da "naam" amma nakasa d'agowa d'ago mana murmushi nayi na k'ara k'asa da kaina..
      Dariya yayi harsaida fararen hak'oranshi suka fito yace "yau bazaki man magana ba ko?" nidai bance k'ala ba, Uncle sun  shigo gaskia Lady yan gidanku na da kirki naji dad'in yanda Uncle da Matarshi suka karb'eni na gode sosai saura ke naga irin taki tarban, kallon shi nayi dan bansan inda magananshi ta dosa ba, murmushi yayi ya d'agaman gira wanda yasa nayi k'asa da ido na da sauri. Tashi nayi na d'auki plate na zuba mashi abinci na tsiyaya mashi lemu na aje gabanshi...

     Saukowa yayi k'asa ya fara cin abinci yana ci yana santi nidai binshi nayi da kallo ina murmushi komi yayi burgeni yakeyi, yana gamawa yasha lemu aje cup d'in yayi ya lumshe ido yace "gaskia wannan girkin na Lady nane" dariya nayi nace "ya akayi kasani?" ya bazan sani ba?
      Tashi yayi ya shiga toilet ya wanke hannunshi dawowa yayi kusa dani ya zauna, kallo na yayi ya kira sunana NAFEESA saida tsikar jikina ta tashi, amsawa nayi da "NAAM."
        Tashi yayi yazo gabana ya duk'a, tunda ya duk'a gabana ke dakan uku uku a hankali ya furta NAFEESA d'agowa nayi na kalleshi shima k'uri yaman da ido munkai minti goma a haka kana can ya nisa. Yace "kinsan duk idan namiji yazo wajen mace akwai abinda ya kawoshi ko?" Nidai shiru nayi bance mashi komai ba..

      Murmushi yayi ya mik'e tsaye, gaskia tun sanda na ganki naji kin kwantaman kece kalar macen da nake fatan na samu a rayuwa, amma lokacin dana fara ganinki banyi gigin binki ba ko nuna maki wani abu har saida na binciki halinki, kuma Alhamdulillah kinsamu kyakyawar shaida wajen yan uwanki student..
      Takowa yayi yazo gabana yace "dan haka gani gabanki nazo da k'ok'on barata agareki." Kallonshi nayi nace "nifa bangane abinda kake nufi ba yakamata kaman yanda zangane"
     Murmushi yayi yace "NAFESAH ina sanki ina k'aunarki ina san ki zama mother to my unborn child wlhi tun randa na fara ganinki nakamu da sanki" tunda ya fara magana ido na ke kulle na rasa wane irin nishad'i nake ciki, lallai Aflan yayi gaskia da yace zai soni...
      Huraman iska yayi a ido, firgigit nadawo daga duniyar tunani. Kallo na yayi yace "yadai" murmushi nayi na sunne kaina k'asa, bakice komai ba kabani lokaci zanyi tunani gaskia ban yarda ba ni dana kamu da sanki ai ban tsaya tunani ba, dariya nayi na mik'e tsaye kallon shi nayi "nace Lady ta mallaka maka zuciyarta ta baka amana kasani babu wanda ya tab'a shiga zuciyan Lady sai kai kai zaka koya mata yanda zata soka please karda kayi yunk'urin tarwatsa mata zuciya"

      Takowa yayi yace "in shaa Allah bazan tarwatsa zuciyanki ba, zaki Alfahari dani.

       Murmushi nayi na sadda kaina k'asa d'ago fuska na yayi yace "Lady ki kalli cikin idona kice kina sona" dariya nayi wanda saida kumatuna suka lotsa nace "aikam bazan iya ba, zaki iya...

      Juyawa nayi na fara tafiya saida nakai bakin k'ofa na juyo nace "Saleem I love you from d buttle of my heart, ina kaiwa nan na ruga da gudu, inajinshi yace "WOW" I love u to d moon n bac my Lady....

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245