JARABAWA TACE 76~80

JARABAWA TACE


yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                         (NWA)

                        7⃣6⃣➖8⃣0⃣


      Duk abinda yafaru gaban idon su Uncle akayi shi, falon suka k'araso dafashi Uncle yayi d'agowa yayi da idon shi da suka rine suka zama ja, murmushi Uncle ya mashi tashi yayi ya rik'e Uncle yace "Uncle wai bata sona mina mata haka mike gareni da zata k'ini" ba Uncle ba ko yaya ya bata tausai. Bubbuga kafad'arshi Uncle yayi yace "kayi hak'uri Sameer kabi komi a hankali ni nasan tana sanka kawai tana tunanin wani abu ne".
      Miyeshi? Wane abune da zai sa ta k'ini haka wlh ina santa sai kuma ya fashe da kuka kamar yaro, rarrashin shi Uncle yayi yace "kayi shiru zan maka bayanin komai.."
     Zama yayi ya dafe kanshi, suma zama sukayi nan Uncle ya mashi bayanin komai bai rage mashi ba, kallon Uncle yayi yace "dan Saleem ya yaudare ta shine zata k'ini?" Murmushi Yaya tayi tace "rad'ad'in da kakeji yanzu taji fiye da haka dan haka dole ka mata uzuri, ni nasan Lady na sanka dan banga k'iyayyarka a idon taba dan haka dole sai kayi hak'uri ka lallab'a komai.."

     Taya? Murmushi Yaya tayi tace "kad'auke k'afa gidannan ka daina kiranta a waya kaida kanka zaka gane ko tanasanka ko bata sanka"...
     Da wannan shawaran ya bar gidanmu...

    Ina shiga d'aki na fad'a kan gado kuka nake wanda bansan dalilin yinshi ba, waya na d'auka na kira Aflan bugu biyu ya d'auka jin ina kuka hankalinshi ya tashi yace "Lady miyafaru? Mi aka maki? Sameer ne babu lafiya?" Duk a tare yaman tambayoyin nan, kuka na cigaba dashi..
     Dan Allah kiyi shiru kiman bayani, kawai kizo ki tadaman hankali duk cikin fad'a Aflan keman magana..
      Cikin kuka na kwashe komai na gaya mashi, ban b'oye mashi komai ba. Ina gamawa yayi murmushi yace "to baki sanshi kenan?"
     Ni bansani ba abinda nace mashi kenan, murmushi yayi yace "yakamata kisani kefa keda kanki, yanzu Lady dan Saleem ya barki sai kice baki k'ara kula kowa? an gaya maki duka mazan suke hali guda, yanzu shi kinsan halin da zai shiga? Kamar yanda kikejin d'acin abinda Saleem yamaki a yanzu Sameer abinda yakeji yafi wanda kikeji.."
     Aflan bansan ya zanyi ba mazan duk halinsu guda karnaje na koma yar gidan jiya..

    Wayace maki duka aka taru aka zama d'aya? Ba kowa bane ba haka ki d'auka k'addararki ce haka, kuma wlh kinji na rantse kina san Sameer kina gudun karya maki yanda Saleem yamaki, amma ke kanki kin kamu da san Sameer wanda ke kin kasa yarda da sanshi kikeyi, Sameer yabi hanyar k'awance dake dan ya mallake zuciyarki kuma yayi sa'a ya mallaketa, hanyar da yabi itace daidai saidai ke kin kasa yarda kinasan sa amma ko kiyarda ko karki yarda kina san Sameer. Anty Nafeesa kefa yanzu ba yarinya bace ba ya kamata ki natsu kisan abinyi bawai ki dinga kuka ba, kije ki zauna kiyi tunani dakanki zaki gano kinasan Sameer, yana kaiwa nan ya kashe wayarshi..

     Kuka na cigaba dayi wanda saida kaina yafara sarawa, kuma duk abinnan babu wanda ya shigo bare yasan halin danake ciki..
     Ban iya fita falo ba kuma babu wanda ya shigo ba k'aramin mamaki nayi ba ganin babu wanda ya shigo wajena..

     Washe gari da safe tun 8 na shirya dan ina da lecture 9 haka na shirya na fito jiki ba kwari falo na tardasu suna break gaidasu nayi amsawa sukayi cikin sakin fuska, zan wuce makarana "abincin fa bazaki ci ba?" Uncle ne yace haka, na k'oshi abinda nace kenan, kud'i ya mik'oman yace "to saikin dawo", nayi mamakin yanda basu tambayeni miyasa banci ba..
     Haka naje na sami driver yakaini makaranta, duk naji ba dad'i saboda Sameer yasaba kaini..

     A haka muka kwashe sati d'aya babu Sameer ba k'aramin tashin hankali na shigaba na rashin ganinshi da banyi ba, gashi sai ramewa nake amma babu wanda ya damu, haka dai har mukayi sati biyu ba Sameer ba alamun zuwanshi..
      Nanfa hankalina ya tashi su Uncle nasamu falo ina isa nafara kuka d'agoni Yaya tayi tace "minene?" Sameer ne! miya sameshi? Yadaina, zuwa wajena..

      Uncle yace "aikam Sameer baya k'asar bai maki bankwana ba?" Da sauri na d'ago nace "nashiga uku shikenan yanzu yatafi yana fushi dani wace irin rayuwa ce wannan?" sai kuma na sake fashewa da kuka...

     Gyara zama Uncle yayi yace "miyafaru ne tsakanin ki dashi?" Wai dan yace........nan na kwashe komai na gaya masu ban rage masu komai ba, cikin zubda hawaye nace "Yaya inasan Sameer" ba k'aramin mamaki tayi ba cewar inasan Sameer ko dayake dama tasan ina sanshi amma batayi tsammanin zan iya fad'a ba...
      Shafa kaina tayi tace "shikenan kidaina kuka" taya zan daina kuka bayan yabar k'asar, yanzu ya zanyi Yaya? Babu yanda zakiyi abinda sukaji an fad'a kenan gaba d'aya suka kalli wajen da akayi maganan..

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245