JARABAWA TACE 86~90

JARABAWA TACE

Yar _ficika

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATIONS
                    (NWA)   

THIS PAGE IS FOR YOU MY MENTOR HAUWA JABO THANX FOR D LOVE, KIA, COURAGE AND SUPPORT. YOU MEAN A LOT TO ME❤ #1love💕💕


                 8⃣6⃣➖9⃣0⃣

Ina shiga d'aki na turo kofar d'akin, ji kake "Bammmf."
Na fad'a kan gado na fara rera Nannauyan kuka, kuka ne mai hade da tsananin bakin ciki, haka har wahallen bacci yayi awon gaba dani.
Na share awanni Ina bacci, mai cike da mafarkai kala-kala, Ina farkawa naga d'akin ya k'ara min duhu, tsaki naja, na wuce don sauke farali, na kare sallah Ina zaune ina karanta wasikar Jaki, kallon wayar nake yi sabida kusan kullum dai-dai wannan lokacin Sameer yana min SMS, a hankali na janyo wayar ina duba message d'inda yake min ada.
Hankali ya kai gun wani SMS da ya min yake cewa.....
"You're like a target that I always try to aim at. How I wish I could aim you at the heart. But every time I fail, I feel so sad. You know why? It's because I always end up missing you.
Bansan lokacin da hawaye suka fara sintiri saman kumatuna ba,
A fili na furta
"Ashe dama duk wayannan kala man naka zaka iya juya musu baya? Ashe cewar da kake u can't live without me, k'aryane?
Ina kake Yau? Ina gwala gwalan kala manka?
Kana can kana rayuwa da wata ba niba,
Oh ALLAH!!!, kana ganin baiwar ka, kana ganin halin da nake ciki!
Allah kamin mafita."
Na shafa na mike na koma saman gado, dan sam bana jin wata abu wai ita Yunwa.

                 ******

Haka rayuwar Lady taci gaba da kasancewa, ta ijiye soyayyah gaba daya a rayuwar ta, bata komai sai karatunta.
   "To Hajiyar Sokoto ba damuwa, Allah ya kawo shi lafiya"
Abinda kunnena ya jiyo min Kenan,
  Ban tambayeta ba, har zan wuce tace "yaron Hajiyar Sokoto ne zaizo wai Job ne zasuyi zai kai kamar 6 months anan, shine tace wai baya chin abincin waje sai na gida, shine tace zai rika zuwa yana chin abinci yana komawa, sai nace da hakan ai gara ya dawo nan da zama gaba d'aya tunda ma nan zai fi masa kusa da wurin da zasuyi aikin, ko ya kikace"
  Murmushi nayi,
  "Gaskiya kam nan zai fi masa kusa, shima dai akwai feleqe wani cewa bazai ci abincin waje ba Sai Na gida"
Ina kaiwa nan na wuce dakina,
   Mustafha yazo gidan mu,
Yaya Musty mutum ne mai sakin fuska, Amma Kuma baya daukar raini ko kadan, ya iya zazzaga masifa, idan yanayi kamar bai t'aba iya Dariya ba, nan da nan sai ya hau mutum da fad'a, hakan yasa na dan fara jin haushin sa.
   Mustafha d'an yayar mahaifiyarmune, shine babba gidansu sokoto suke zama..
  "Lady ni zan fita Kuma kinga kamin Mustafa ya dawo abinci yayi sanyi, so ki d'an girka masa please,"
  "Aah zan dai d'imama masa sauran na rana"
  "To girka masa nace kiyi bana son shashanci, kinbi kin raina shi sai kace bai girmeki ba"
Na zunburo baki na wuce Ina gunguni, araina nace
"Ke Kuma kina min fada Sai kace kin haifeni"
  Araina nake sakawa " mutum yazo yabi ya dami mutane da iya yin banza, Sai kace ba daga sokoto yake ba, sokoto kuwa ai kauye ce"

  (Nidai yar ficika shiru nayi, dan nasan idan  Jabo taji Lady tana fadan sokoto kauye ce zasu hau sama su fado.)

Ni sam na manta da ance na masa girki.
  Shi kuwa direct gurin ajiye abinci ya nufa, amma wayam ba wani bayani,
  "Lady! Lady!!"
  Haka ya rika kwala mani kira amma bani ba labarin na, kitchen ya nufa nan ma ba alama ta kuma ba abinci, dama Musty baya jure Yunwa ko kadan, fridge ya bud'a ko zai sami abin tab'awa, nan ma wayam, wani k'ololon bak'in ciki ya tsaya mishi a wuya, yana fitowa, ya nufi hanyar da yake ganin ina fitowa kullum, yana kaiwa yaga k'ofa biyu, a hankali ya tura kansa a dayar kofar da ya gani a bud'e,nice a tsaye d'aure da towel ina goge jikina da d'ayan towel d'in, a hankali towel d'in yayi k'asa zai zame da sauri na rik'oshi, mutuwar tsaye yayi da ganina, da yake fuskata tana kallon gafen window ne, shi yasa ban ganshi ba, a hankali yayi sauri ya fito daga d'akin, jikin sa duk a mace, shi kam duk na burgeshi, Sai yaji yana son ya tab'a jikin nan nawa, yayi ta tunani sam ya manta da wata yunwa, a haka har na shirya ta fito ina zuwa na ganshi zaune, gabana ne ya fad'i, dan nasan sai ya balbaleni da masifa, Amma akasin haka da ya bini da Murmushi,
Nima na mishi Murmushi, a raina nace ko ya k'oshine,
Hak'uri na fara bashi.
  Tun daga lokacin muka fara shiri da Yaya Musty, har takai mun shak'u da juna,
Tabbas bazan kira shak'uwar mu a soyayyah ba, sai dai na kirata a matsayin shak'uwa na yan uwan juna,
Har takai abin ya riked'e ya koma soyayyar gaske, wasa- wasa mukayi sabo da juna. Abinka da Wanda kake gani kullum, ko ba so, sabo wani abune da zan iya cewa yafi soyayyah tasiri a zuciya.
  Mun zama d'aya dashi, bana iya chin abinci idan baya nan, shima haka, duk inda zani tare muke zuwa, har idan munje gida ana tsokanarmu.
   YAya Musty ya iya soyayyah, ya iya lallab'a mace da duk wasu kalamai na faranta rai, haka ya samu zuciya ta ba tare da wahala ba.
Ban San na kamu har haka ba Sai lokacin da ya k'are abinda yazo yi, naji gaba d'aya kamar zai barni a makabarta ne ya tafi abinsa, lokacin da zamuyi ban kwana haka nayi ta kuka, yana bani hak'uri. Komawar Yaya Mustafha gida ba k'aramin Haifar min kadaici yayi ba, Amma Kuma Yaya Musty yana iya bakin k'ok'arin sa na kula dani yanda ya kamata, duk wani abu da ya dace ama budurwa yana min.
Har iyaye zasu shiga cikin zancen murna a guna ba'a magana.
  Wata rana na dawo daga kasuwa Sai naji ana kus kus a gidan mu, na kashe kunne naji, Ashe Mustafa koda yazo yanada wacce sukayi dating da ita, Amma da yake Munafukin namiji ne bai gaya man ba, Sai da yaga iyaye zasu shiga cikin lamarin.
Nayi kukan rasa Yaya Musty, Sabida ban tab'a kawowa a raina zai iya yaudarata ba, dan uwanane Kuma shak'uwar mu bata da misali, cikin k'ank'anin lokaci muka saba da juna, na sakankace akan nayi miji, sai gashi yayi abu mafi muni gareni wato zanba cikin Aminci, na kwallafa raina ga auren Yaya Musty sai dai shi kam ba haka a zuciyar sa.

     Dasauri na fad'a falon suna ganina sukayi shiru kallon su nayi cikin takaici nace "Uncle miye nayin shiru? Na riga danaji komai shikenan nikuma haka rayuwata zata k'are shima na rasashi kamar yanda na rasa sauran? nikuma kalar tawa jarabawan kenan" Ina kaiwa nan na yanke na fad'i da sauri sukayi kaina...
     Ruwa suka dinga watsaman amma ba alaman rai a tare dani, kallon Uncle yaya tayi tana kuka tace "mukaita asibiti bansan na rasata pls" d'aukata sukayi suka nufi asibiti dani, muna isa nurses suka karb'eni aka shiga dani ciki..

   Likitoci uku ke kaina, saida muka kwasha awa hud'u kafin suka ceto rayuwata, b'angaren su Yaya kuwa tun da aka shiga dani take kuka, kallon ta Uncle yayi yace "ba kuka zaki ba adua zaki mata" daidai likitoci na fitowa..
   Dasauri suka mik'e suka nufesu a tare sukace Doctor ta tashi? Wani saurayi kyakyawa ya d'ago ya kallesu yana murmushi yace kutardani office yana kaiwa nan ya wuce...

  Da sallama suka isa office d'in izinin shiga ya masu, shiga sukayi suka samu wuri suka zauna, saida ya gama yan rubuce rubuce ya d'ago ya kalli Uncle mik'ama Uncle hannu yayi suka gaisa, gyara zama yayi ya kalli su Uncle yace "ya kuke da ita?" K'anwata ce Uncle ya bashi amsa..
  To gaskia k'anwarka takamu da ciwon zuciya wanda zata iya rasa ranta idan ta cigaba da saka damuwa, dan na dad'e ban had'u da mai ciwon zuciya haka ba, "nashiga uku itama zan rasata kamar yanda na rasa iyayena" Yaya ke wannan maganan jawota Uncle yayi ya rungumeta yace "bazaki rasata ba in shaa Allah.."

   Kallon su Doc yayi cikin tausayawa yace "kiyi hak'uri duk wanda kikaga ya mutu kwananshi ne ya k'are, abinda zan baku shawara shine a guji b'ata mata rai duk abinda bataso a nisance shi abinda takeso a kawo matashi kusa, shi zaisa ta rage damuwa amma muddin tana damuwa to zaku iya rasata".. nan dai doctor ya basu shawara daga k'arshe sukayi sallama suka dawo d'akin danake...

  Satina biyu asibiti aka sallameni, duk wanda yaganni saiya tausayaman saboda irin halin dana shiga na rame sai fari da nayi..

Tun daga lokacin na rufe babin soyayyah, bana kula kowa. Sabida kusan duk Wanda naso Sai haka ta faru dani, har nazo Ina zargin kaina..
Nasan cewa JARABAWA TACE wannan, Kuma ina fatar na contenta.

Rayuwa juyi juyi...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245