JARABAWA TACE 56~60

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                      (NWA)


THIS PAGE IS FOR YOU MY FOUR STARS⭐

ZARAH BUKAR~Besty
AUTAR HAJIA~Kawa
NAFEE ANKA~Sweetest
STYLISH BICH~Hajia nah



                    5⃣6⃣➖6⃣0⃣

      Zanci abinda nace kenan, zama Aflan yayi ya dinga bani abinci a baki har sai da nace mashi na k'oshi kuma ya tabbatar da naci da yawa kana ya kyaleni. Babu wanda baiyi murna ba ganin naci abinci ranan, kallo na Aflan yayi yace "kinsan wani abu?" Girgiza kai nayi, yace " tashi kije ki wanka ki shirya fita zamuyi yanzu" nikaina inasan fitan dan nagaji da gidan. Ba musu na tashi nayi hanyar d'akina, ina shiga na fad'a toilet danyin wanka....
      Ban d'auki wani lokaci ba na fito daga toilet, tsintar kaina nayi da sha'awar yin kwalliya gabam mirror naje mai na murza, simple makeup nayi nabi jikina da turaren rasasi, ina gamawa na kalli kaina ga mirror nikaina nasan nayi kyau murmushi nayi na nufa gaban wardrobe abaya na d'auko black nd red na saka  rolling nayi da black veil kallon kaina nayi na k'ara kallo, bansan sanda hawaye suka gangaro man ba...
       Daidai Aflan ya bud'e d'akin, ganin ina hawaye yasa ya k'araso da sauri, d'aure fuska yayi yace "kinyi kyau amma zaki b'ata kwalliyanki, please kidaina indai kinasan mushirya" murmushi na k'ak'alo nace "nadaina" gud gal kokefa yar k'anwata, duka na d'aka mashi nace "waye k'anwarka?" Dariya yayi yace "natuba Unty Lady." Dukanmu muka sa dariya...

      Hannuna ya kama muka nufi hanyar falo, muna isa Uncle da Yaya har had'a baki suke "MASHA ALLAH,  duka muka saka dariya harda yan biyun Yaya..
      Kallona Uncle yayi yace "wannan kwalliya haka kokefa? Lallai wani aiki sai Aflan" dariya Aflan yayi yace "Daddy aini nasan halin kayana nasan yanda zan bida ita" dariya Uncle yayi yace na yarda kam..
      Yaya tace "Allah yasa asamoma Uncle saurayi," b'ata fuska nayi nace "kana jinta Uncle Allah zan fasa fita" murmushi yayi yace "kyaleta kinji, ga wannan kunyi amfani dasu" dubu hamsin ce yabamu karb'a nayi na mashi godia muka fita...

      Muna fita bamu tsaya ko ina ba sai Jifatu nan nafara sayayya ba abinda na saya sai chocolate shidai Aflan ido ya sakaman saida na gama na juyo na kalleshi nace "yarona nagama" dariya yayi yace "suka dai zaki siya?" D'aga kaina nayi alamar "Eh"..
      Kud'i ya biya muka fita, kallo na yayi yace "saikuma mi kike buk'ata?" Babu abinda nace kenan. Kin tabbata? Na tabbata mana dariya yayi yace "shikenan..."

      Haka muka dinga yawo cikin gari, muna tafiya muna fira kamar ba abunda ke damuna. Bamu dawo gida ba saida ana kiran sallar magrib, Aflan bai shigo gida ba masallaci ya wuce ni kuma na shigo gida, ina shigowa ban iske kowa falo ba nayi d'aki, ina zuwa na baje kayan da nasawo kan gado na fad'a toilet danyi alwalla....
        Ina fitowa na tada sallah ina idar da sallah nafara adua akan Allah yasaman dangana, ban tashi daga inda nake ba saida nayi sallar isha....

      Ina cikin tashi daga inda nayi sallah, Aflan ya shigo da sallama guri yasamu ya zauna yana murmushi yace "kingama sallah?" Eh nagama, to muje falo ba musu na bishi...
        Muna isa kowa na kan dainning, wuri na samu na zauna kusa dani Aflan ya zauna, gaidasu Uncle nayi amsawa sukayi, Aflan ne yatashi ya zubaman abinci da kanshi yana zubaman ya mik'oman ba musu na k'arba nafaraci, k'uri yaman da ido yana kallo na. Ina d'agowa na had'e rai nace "kallon na lafiya ne?" Dariya akayi gaba d'aya yace "naga yanda kikayi k'ibane yau kad'ai ashe dai ina da rana gaskia Daddy albashi zaka yankaman tunda naga Ladyn ka tafara murmurewa" dariya akayi gaba d'aya...
      Tashi nayi ina hawaye, da sauri ya kamo hannuna yace "wlhi wasa nake maki pls kiyi hak'uri".
      Bance komai ba, "please kiyi hak'uri wlhi da wasa nake i don't mean to hurt you please forgive me", hawaye na share na zauna, yace "smile mana" fuska na k'ara b'atawa marairaicewa yayi yace "please" bansan sanda na saki dariya ba. Shima dariya yayi haryana dungurina...
      Ahaka muka cigaba da cin abinci munaci muna wasa. kowa kaganshi cikin farin ciki yake..
      Tabbas Aflan wani b'angare ne na jikina, saboda zan iya ce maki shine wanda yasan halina, shi zaice nayi abu nayishi ba musu....

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245