JARABAWA TACE 11~15

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION



              1⃣1⃣➖1⃣5⃣

      Haka rayuwa ta cigaba tsakaninmu cikin so da k'aunar juna, muna ss3 nida Aflan komai na d'iya mace ya fito man kyawuna yak'ara fitowa kamar yanda kika sani doguwace ni banda jiki sosai amma ina da hipz coca cola shape kenan, kuma ni ba fara bace ba chocolate colour ce, kyau na bawani shahara yayi ba amma duk wanda ya ganni saina burgeshi saboda Allah yaban kwarjini, inada gashi daidai gwargwado komai dai nawa zan iya ce maki daidai nine....
      Tunda muka shiga ss3 samari suka fara man magana amma bana kulasu saboda ni a lokacin bansan miye so ba, watarana muna zaune falo mu duka saiga yaro ya shigo wai ana sallama da Nafisa, kuka nafara nace "Uncle bansan da zuwanshi ba ba ninace yazo ba wlhi ban tsayawa da kowa ka tambayi Aflan" kowa saida yayi dariya saboda ganin yanda na tsorata, hawayena Uncle ya shareman yace "nasani Lady nasan bazaki ce wani yazo ba saboda karatu kikeyi" yana kaiwa nan ya tashi ya fita, bai jima ba ya dawo koda ya shigo ina hawaye duk'awa yayi kusa dani ya shareman hawaye yace "daina kuka my Lady bazai sake dawowa ba kinji" d'aga kai nayi alamar "to"..

     Da Aflan yaso tsokana na saiya fara cewa wlhi Uncle bansan da zuwanshi ba, bani nace yazo ba ban tsayawa da kowa ka tambayi Aflan, to ranan fa yini zamuyi fad'a kum gashi yafi k'arfina haka zanci wahala nayi kuka har nayi bacci, ita dai Yaya bata ce muna komai....

      tun daga lokacin babu wanda ya k'ara aikowa kirana, haka muka cigaba da rayuwarmu cikin so da k'aunar juna...
     tunda muka shiga ss3 kullum sai Uncle ya muna extra lesson har muka zana WAEC da NECO, mungama lafiya saboda result d'inmu ko da ya fito yayi kyau kuma munyi sauka a Islamiyya Uncle yaji dad'in ganin result d'inmu da saukar da mukai, ranan fita yayi damu ya muna siyayya mai yawa aranar yabamu waya Iphone6 zokiga murna wajena da Aflan....

       Watarana muna zaune falo muna fira Uncle ya shigo, gaba d'aya muka mashi sannu da zuwa amsawa yayi ya zauna cikinmu anata fira. Takarda ya mik'oman karb'a nayi hannu biyu ina bud'ewa naga admission ne na Ummaru Musa Yar adua University tsalle nayi ina murna, Aflan na mik'amawa nace "bro kaga admission dina kodai bak'in ciki kakeyi?" Tab'e baki yayi yace "mizanma bak'in ciki"..
      Dariya Uncle yayi yace "toh in bashi kake ba ka karb'a mana" tashi yayi yace "haba Daddy itafa kad'ai ka samomawa" saikuma ya fashe da kuka..

      Jikina yayi sanyi nace "Uncle nikam idan babu na Aflan na fasa zuwa"..

     Duk abin nan da ake Yaya batace komai ba hakama twinse d'inta..
      Murmushi Uncle yayi yace "toh ku zauna" zama mukayi ba musu...

      Zama ya gyara yace "yanzu ke Lady bazakije makarantar ba inba Aflan?" D'aga mashi kai nayi nace "Eh" dariya yayi sosai yace "toh idan shi ba k'asar zaiyi karatu bafa?" Nace "toh zanje tunda nasan shima yatafi makaranta" toh karku damu shima ya samu Admission amma a Cairo toh kinga ba tare zakuyi school ba shi nextweek zai tafi in shaa Allah, tun kafin Uncle ya ida magananshi muka fara ihu muna murna, Yaya ce ta daka muna tsawa da sauri muka natsu, d'aure fuska Uncle yayi yace "akanmi zaki hanasu murna?" Murmushi tayi tace "ayi hak'uri" sufa sojojinah ina zasuyi nasu karatun? Kusa dake mana, dariya tayi tace "ai yanda ka fitar da wancan waje haka suka zaka fiddasu ko ya kukace?" Gaba d'aya sukace "Eh Ammi" nan dai mukacigiba da fira duk rabin firan nasiha ne yanda zamu kula da kanmu idan muntafi jami'a...
      Haka muka cigaba da shirin tafiyan Aflan, randa zai tafi har kano muka kaishi saboda tacan zai tashi, koda mukaje airpot naga da gaske tafiya zaiyi ya barni kuka nafarayi shima kuka ya dingayi rungume juna mukayi muna kuka, da kyar aka rabamu saboda anfara masu screening haka ya juya yatafi yana d'agoman hannu yana share hawayenshi nima hannu nake d'aga mashi ina hawaye, inaji ina gani Aflan yatafi batare dani ba, tunda muka taso yau ce rana ta farko da d'ayanmu yayi tafiya ba tare da d'an uwanshi ba...

      Koda muka dawo gida ban walwala damuwar dana shiga yasa kowa na gidan damuwa, dan dole na saki raina na cigaba da harkoki na amma kullum muna mak'ale da waya..
      Nima na fara zuwa makaranta kuma cikin ikon Allah bansha wata wahala ba, saboda Uncle ya saka anman komai dan haka lectures kawai nafara...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245