JARABAWA TACE 6~10

JARABAWA TACE

yar_ficika

Assalamu Alaikum
Ina mai sanar da masoya na cewa na canja sunan littafina daga KADDARA TACE zuwa JARABAWA TACE sakamakon wata yar uwata tayi book din dashi....

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

        
               6⃣➖🔟


      Tana tashi da safe tayi aikace aikacenta, kafin  Zainab tazo K'arfe tara (9:00am) Zainab ta k'araso gidan, da murna suka tari juna d'aki suka nufa ruwa ta kawo ma Zainab da lemu da dambun nama, Kallonta Zainab tayi tace "kekam baki gajiya da hidima" dariya tayi tace "taya zan gaji?" Dariya sukayi gaba d'aya Zainab tace  "nikam nayi maki sammako" bugun kafad'anta tayi tace "wane sammako kikayi su Yaya tun bakwai sukabar gida" zaro ido tayi dagaske? eh mana wai gara su isa da wuri toh ina gamawa dasu na fara gyaran gida kinga yanzu nayi komai sai mufara. Kafin nan jiya Uncle yaban waya mik'a mata tayi, ido ta zaro Iphone7 nake gani? Murmushi tayi tace "wlh jiya yaman surprise" lallai yar gatan Yaya da Uncle, wlhi suna ji dake amma ke kin kasa kwantar da hankalinki, damuwar da kika shiga duk ya d'aga masu hankali, murmushi tayi ta share kwallan dasuka gangaro mata tace "idan kin shirya zanfara" zama ta gyara tace "na shirya mana..."

      Kamar yanda kika sani sunana Nafisa Ahmad mu biyu ne wajen iyayenmu Yaya Aisha ce babba saini tunda Mahaifiyarmu ta haifi ya Aisha bata k'ara haihuwa ba harma an cire ran zata k'ara haihuwa, Mahaifinmu bawani attajiri bane ba amma yana da rufin asiri daidai gwargwado, dan duk wani hak'in iyalanshi yana d'aukewa bai ragi iyalanshi da komi ba, Ya Aisha nada  shekara goma sha takwas Allah yaba Mahaifiyarmu  wani cikin, zokiga murna wajen Abbanmu cikina na da wata Bakwai Allah yama Mahaifinmu rasuwa sakamakon had'arin mota da yayi, kafin Mahaifinmu ya rasu yama d'an abokinshi alk'awarin zai bashi auren Ya Aisha da tagama secondary haka kuwa akayi Yaya nagama secondary aka saka bikinsu da Uncle Sadeeq lokacin cikina na wata takwas, an saka bikin da Mahaifiyarmu ta haihu ta gama wanka za'ayi bikin...
        Randa cikina ya shiga wata tara da kwana goma ranan Mahaifiyata ta tashi da wani irin ciwon ciki mai tsanani haka aka d'auketa akayi asibiti da ita, ko kafin a isa asibiti tasha wuya harta fita hayyacinta, ana isa Asibiti likitoci sukayi kanta dan ceton ranta da abinda zata haifa, anceto ran abinda zata haifa saboda CS aka mata, amma ita bata k'ara minti biyar ba bayan anmata aikin tace ga garinku, nan fa hankalin dangi yatashi idan ka kalli Yaya saita baka tausai saboda halin da tashiga...

      Haka tana gani aka shirya mahaifiyarmu aka tafi da ita gidanta na gaskia, tunda aka Haifeni nake hannunta tak'i yarda taba kowa ni duk wanda yace zai karb'eni saita fara kuka dan dole aka kyale mata ni ta dinga ban madara..
        Sati na zagayowa naci suna Nafisa saboda sunan Mahaifiyata kenan aranan kuma aka d'aurama Yaya aure ita da Uncle Sadeek danginshi ne suka nemi hakan saboda sunga halin da muke ciki...

      Basu buk'aci komai ba dan ko kayan d'aki babansu Uncle ne yama Yaya saboda Aminin Mahaifinmu ne, randa aka d'aura aure rannan aka kai Yaya gidanta tare dani tasha kuka kamar ranta zai fita daga baya ta hak'ura..
       Uncle ne ya sakaman Lady saboda sunan Mahaifiyarmu ne tun daga sannan kowa yake kirana da Lady..

      Tunda Uncle ya auri Yaya yake hidima damu baitab'a nuna gazawarshi akanmu ba, munshak'u dashi sosai saboda duk idan yana gida yana tare dani, duk abinda yagani na wasa saiya sayoman....

      Inada shekara d'aya a duniya Yaya ta Haifi d'anta namiji, zokiga murna wajen Uncle ranan su na aka sakama yaro sunan Mahaifinmu Ahmad amma ana kiranshi da Aflan..
      Haka muka taso nida Aflan kai d'aya ga san junanmu da mukeyi, idan kikaga Aflan zaki rantse ya girmeni saboda yafini girma, kullum Burin Uncle yaga ya kyautata muna nida Aflan, ina da shekara hud'u Aflan nada uku aka sakamu play group anan Hazel international school, kullum Uncle ke kaimu ya d'auko mu...
      Yaya bata sake haihuwa ba saida Aflan nada shekara biyar nikuma ina da shida ta haifi tagwayenta duk maza, tun daga Hasan da Husaini Yaya bata sake Haihuwa ba..
         
          Dangin Uncle suke cema Ya Aysha yaya saboda sunan Kakar Uncle ce to nima da haka nake  kiranta saboda dashi naji ana kiranta, shi kuma Uncle haka yan gidansu suke ce mashi Uncle, su Aflan kad'ai ke kiranshi da Daddy, ita kuma Yaya suna kiranta Mammy..
     
       Tunda natashi bansan wasu iyayen ba sai su saida nakai jss3 Yaya take gayaman, nayi kuka kamar zan fitar da raina amma daga baya na dangana, koda uncle yazo yaga halin da nake ciki yayi fad'an miyasa tagaya mani saboda bai san ganina cikin damuwa, Yaya tace "abinda yasa na gaya mata saboda ta dinga ma iyayenta adu'a" da haka Uncle ya gamsu har ya daina fad'an.
     Tunda nataso banda k'awa Aflan ne Abokina shi nake shawara dashi duk inda zamu tare, kullum muna tare ko fad'a mukeyi idan d'aya zai fita dole sai d'aya ya rakashi, kullum twince d'in Yaya cikin yi muna dariya suke..

      Haka rayuwarmu ta cigaba cikin so da k'aunar junanmu har mamakin irin k'aunar da Uncle keman, saboda yanda yakeman baima yaranshi haka. Bazan manta ba akwai randa muna zaune falo Uncle Sadeek ya shigo da ice cream dasu chocolate gaba d'aya ledan ya mik'aman Aflan yace "Uncle mufa?" Dariya yayi yace "na Lady ne idan zata iya baku ta baku" nikuma nace bazan bada ba, nan fa muka fara rigima, Yaya tace "wai miyasa kake nuna banbanci?" Murmushi yayi yace "saboda Amanata ce ita zan iya komai dan naga na kyautata mata banci amanar da akaban ba."
      Tashi nayi na rungumeshi nace "Uncle na gode ina rok'on Allah ya kawo randa nima zan saka maka" murmushi yayi yace "Amin my Lady"...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245