JARABAWA TACE 36~40

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                     (NWA)

  
THIS PAGE IS FOR YOU MIEMIE BEE
                    BIEHEART❤




On your birthday, I may not be there. But that doe'snt mean that I don't care. I regret that I won't be by your side to celebrate, but I wish nothing but happiness in your fate. HAPPY BIRTHDAY IN ADVANCE MIEMIE BEE🎁🎊🎉




                 3⃣6⃣➖4⃣0⃣

        Ina shiga d'aki nafad'a kan gado ina dariya, waya na jawo na kira Aflan bugu biyu ya d'auka yace "Lady ban labari". Dariya nayi nace "wane labari zan baka?" Tsoki yayi yace "bansani ba Malama idan zaki gayaman ki gayaman yanda kukayi dashi" tab'e baki nayi kamar yana ganina nace "labari fa babu dad'in ji" da sauri yace "WHY?" Ceman yayi yana san k'awata Zainab kuma yaga nikad'aice Frnd d'inta shiyasa ya biyo ta hanya ta yasan zata amince dashi. Dariya Aflan ya bushe da ita yace "u mean bake yakeso ba? Lallai amma guy d'innan yasha dake duk rawan kan da kikayi kanshi ya maki haka, gaskiya bai kyauta muna ba duk delicious d'in da aka had'a mashi haka zai mana?  to ke ya kika ce mashi?" Saika gama yiman dariyan na gaya maka yanda nace mashi, marairaicewa yayi yace "kiyi hak'uri Allah bazan k'ara maki dariya ba."
      Toh yanzu inda hakane abinda na gaya maka dariya kenan zakaman? Toh kina nufin ba gaskiya kika fad'aman ba, dama bari nayi naga irin hankalinka ashe har yanzu yaro ne kai. Lallai ma yarinya kinfa rainani nifa namiji ne kinsan na girmeki, yanzu ba haka ba gayaman ya kukayi dashi...
      Numfashi naja na kwashe duk yanda mukayi da Saleem na gayama Aminina, murmushi yayi yace "dama ai nagaya maki dole ya soki dole ya kawo kanshi" bafa dole Malam, nidai shaawarata gareki shine ki natsu kisan waye shi kinga shine first love naki kuma zan iya cewa baki tab'a sanin so ba sai yanzu, toh yanzu zakisan d'acin so da dad'in sa kuma saikin yi hak'uri dan shi so da kika gani yagaji abubuwa da yawa, saikin yi hak'uri, dole watarana ku samu matsala kiji kin tsaneshi amma kuma zaku shirya wannan is normal thing akan love, so you have to take care. Jikina duk yayi sanyi dan nasan maganganun Aflan gaskiya ne, numfasawa nayi nace "in shaa Allah zan kula kaidai ka tayani da adua" karki damu adu'a kullum cikin yimaki ita nake Ladyn Uncle. Bankwana mukayi kowa ya aje waya...

      Ina aje wayan Aflan, wayan Saleem ya shigo d'agawa nayi tare da yin sallama, amsawa yayi yace "nayi fushi dake" da sauri nace "miyasa?" Saboda kin tafi kin barni, Allah kunya nakeji, haba Lady wane irin kunya yanzu fa yakamata mufahimci juna mu nunama juna irin san da mukema juna, idan kinajin kunyata taya zanji dad'in nuna maki soyayya, dariya nayi nace" natuba next time ba zan gudu ba, Allah yasa nace "AMIN"
       Nan muka dinga fira yana fad'aman irin san da yake man wata kalmar ma ranan nafara jinta, bamu ankara ba mukaga biyu na dare (2:00am) bankwana mukayi ba dan ranmu yaso ba
      Tun daga ranan Saleem ya koya man sanshi, soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanina da Saleem babu abinda muke b'oyema juna duk wanda yake tare dani yasanni dashi, idan ina makaranta muna tare gida kullum sai yazo haka waya kullum waya na kunnena kowa yana mamakin irin san da Saleem yakeman, nikaina wani lokacin ina mamakin irin sanda yakeman..

       Kallon Zainab tayi tace "yanmata yakamata kiyi sallah kici abinci kafin na cigaba, nidai fashin sallah nakeyi" dariya tayi tace "nima ina fashin sallah" abinci fa? Allah banjin yunwa kawai ki cigaba labarin nan duk yasa na koshi, murmushi Lady tayi tace "gara dai kici saboda k'ila gaba labarin bazai maki dad'i ba" tana kaiwa nan ta mik'e ta nufi kitchen dan kawo mata abinci....

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245