JARABAWA TACE 71~75

JARABAWA TACE

yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                         (NWA)


                       7⃣1⃣➖7⃣5⃣

      Tun daga sannan shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanina da Sameer, shike kaini makaranta ya d'au koni kullum yana gidanmu, kowa yasan k'awance na da Sameer.
     Aflan har gori yakeman tunda na samu Sameer na daina kulashi saidai kawai nayi dariya, dan gaskia Sameer namiji ne mai saurin shiga rai duk abinda nakeso shi zaiyi idan banaso to ko yanaso ya barshi..
     A haka kullum shak'uwa na k'ara shiga tsakaninmu, ranan wata litinin ya d'auko ni daga school muna tafe muna fira. Har muka iso gida, bud'e k'ofa nayi zan fita hannu na yakamo juyowa nayi na kalleshi nace "yadai?" Murmushi yayi yace "babu" to muje mana, ah ah zan wuce gida ne amma ki saurareni aftr isha akwai maganan da zamuyi dake, gyada kai nayi nace "shikenan Allah ya kaimu" ina kaiwa nan na fita ina d'aga mashi hannu har yabar haraban gidanmu..
       Tafe nake ina tunanin wace magana ce zamuyi da Sameer haka, banda wannan amsar haka na hak'ura na shiga cikin gida..

    Tun da aka kira isha gabana ke fad'uwa a daddafe nayi sallah ina kan sallaya ina adua naji wayana na ringing ban tashi ba sai da na gama adua ina tashi wayan na tsinkewa, ina cikin ninke kayan sallah kira ya sake shigowa..
      Ina d'aukar wayan naga sunan Sameer kan screen d'in wayan gabana ne ya fad'i a sanyaye na d'auki wayan "Lady ina falo" abinda yace kenan to na amsa dashi na kashe wayan..

     Gyalena na d'auka nayi hanyar falo babu kowa falon saishi kad'ai da sallama na isa fallon. Amsawa yayi tare da d'ago ido ya kalleni, murmushi na sakar mashi wanda bansan nayi ba..
      K'arasawa nayi cikin falon na samu kujeran kusa dashi na zauna gaidashi nayi ya amsa cikin dariya, kallo na yayi yace "Lady yana ganki haka?" Dariya nayi nace ya zaka ganni?"

    D'aure fuska yayi yace "haka ake tarban bak'o ba kwalliya ba ko ruwa?" Dariya nayi nace "yau kuma da wannan rigiman kazo?" Bari na kira Deeyerh ta kawo maka, bansan Deeyerh ke nakeso ki kawoman ke. Girgiza kai nayi na tashi na kawo mashi lemu, ina dawowa na bud'e na zuba mashi a cup na mik'a mashi...
    Kurb'an lemu yayi kafin ya aje cup din, kallo na yayi yace "sauranki ki koma kiman kwalliya" ido na zaro nace "dan Allah kayi hak'uri wace kwalliya kuma yanzu, kai kullum da sabuwar rigimarka" dariya yayi yace "in saurayinki ne haka zaki fito mashi?" B'ata fuska nayi, yana ganin haka yace "yi hak'uri kafin ki fara fushi dani in rasa inda zan saka kaina" bansan sanda nayi dariya ba..

     Murya ya gyara yace "NAFEESA" da sauri na juyo na kalleshi yauce rana ta farko daya kirani da sunana sai kuma na sadda kaina k'asa, Nafeesa ya k'ara kira a sanyaye na amsa mashi, kiban hankalinki magana nakeso nayi dake. "Ina jinka" abinda nace kenan..

     Duk abinda zakiji daga bakina kiyi hak'uri ba laifina bane ba wlhi zuciya tane nayi nayi na hak'ura amma na kasa shiyasa na yanke hukuncin na sanar dake ko Allah zaisa naji sauk'i. Nidai tunda yafara maganan na tsura mashi ido..
     Lady tun randa na d'ora ido na akanki naji wani abu da ban tab'aji ba, haka nayini ranan kuma na kasa yarda da sanki nakeyi, a haka na yini ranan har na kwanta bacci tunaninki kawai nakeyi wanda narasa dalilin yinshi, tun daga ranan da tunaninki nake yini narasa yanda zanyi, abokina na samu namashi magana. Murmushi yayi yace man tabbas sanki nakeyi, nikaina nayarda da sanki nakeyi amma kuma nasan ba abu bane mai yuwa saboda baki kulani iyakarki dani gaisuwa, narasa yanda zanyi da zuciyata nayi nayi na yakice sanki a zuciyata amma na kasa, abokina na sama yabani shawaran dana k'ulla abota dake nakuma amince da wannan shawaran dan idan ina ganinki kullum zai rage mani rad'ad'in danakeji akanki...

     Randa nazo na gaya maki inasan abota dake ki kak'i amincewa ba k'aramin tashin hankali na shigaba, tun daga ranan na d'auke k'afana daga gidanku amma abinda baki sani ba tunda ki kak'i amincewa dani ban k'ara lafiya ba, sati na guda asibiti, sai bayan naji sauk'i na dawo na kuma sake tambayarki nayi sa'a kika amince dani tun da kika amince man na d'auki alk'awarin faranta maki koda hakan yana nufin na dawwama cikin bak'in ciki..
      Tasowa yayi yazo kujeran danake zaune ya d'ora hannunshi bisa hannuna yace "Lady wlh ina sanki san da bazan iya musulta makishi ba dan Allah ki amince dani wlhi l'll  secrifise anything to make you happy. Shiru yayi ya d'ago ya kalleni, da tunda yafara magananshi nake hawaye..
     Dasauri ya kalleni "yace Lady miye?" Tashi nayi ina kuka nace "Sameer kayi hak'uri pls wlhi I can't ba zan iya sanka ba pls ka kyaleni na tsani kalman so bazan so kaba dan Allah ka kyaleni" ina kaiwa nan na bar falon da gudu ina kuka...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245